Halimatus sadeeya

Alhaji shazali yaturo manyan mutane adanginsa sunkawo kudin auren asiya dubu hamsim malam yabasu ankuma tsaida mgnr biki kwana goma
Su lami se shirye shirye akeyi kullin se anyada habaici har takai su habi sun kullaceta sunce da su take amarya Kuma Bata fasa fita tallaba Kuma ahaka Dan jahilci ita da alhaji shazali basu fasa aikata mashaar da sukeba
Tin saura kwana hudu biki lami tasa yan,uwanta na kauye sukazo saboda alhaji shazali yamusu alkawari ze turo da buhunhunan shinkafa na biki ranar da hauwa tazo tagaya Mata ansha habaici
itadai umma dariyane nata
Yan uwan lami du sunzo suncika gida wasuma Yan San azo aga birnine saura kwana biyu biki lami se baza Ido take taga alhaji shazali yaturo da buhunhunan shinkafa Amma shuru babu labari gata jinjiga se kashe kudi take wajan dafawa Yan uwanta na kauye abincin da zasuci kunsan dai Yan kauye da ci tinda su komai awadace yake annoma anajje kawai dauka zaayi adafa Dan haka su BasuSan lami tadafa abinci kadan tabasuba
musummanma suna ganin sunzo birni Kuma ance yanbirni kudi garesu gashi sunzo da Yara idan lami yafara Raina fata tasamu hauwa ya mgnr shinkafa da alhaji shazali yace zeturo
hauwa tace yace yau azakawo
Dayamma alhaji shazali yaturo da buhun masara biyu yace ayi hakuri Wanda yaaika yasiyo shinkafa bashi da lfy yayiwa hauwa dadin Baki tayarda yabata da dubu goma yace tabawa babarta lami tayi cefane
Tindaga Nan jikin lami yafara sanyi mekuwa su tala zasuyi inba dariyaba lami se borin kunya takeyi
itadai umma nata dariyane Kuma da ita ake aiki baruwsnta takuma Kira sadiya awaya tagaya Mata mgnar auran hauwa sadiya ta gayawa aliyu yace se ranar daurin aure zasuje tare
Yau ranar daurin aure gida yacika har da Yan unguwa da dangin malam umma takira su Yaya da kannanta su nafisa du sunzo
Lami itama har da masu kidan kwaryama ta gaiyato se doka kwarya ake lami se gayawa yanbiki take ai daurin auran hauwa augo yace har da kujerun makka zebayar da miliyoyi se murna ake tayata
Daga kofar gida Yan daurin aure antaru andaura auran hauwa malam Musa da alhaji shazali akan sadaki nera dubu ashirin
Acikin gida kuwa lamice tace abata fili zatayi rawa ita Daya akabata tace masu doka kwarya su doka Mata kidan hauwa amaryar nera auran da Babu irinsa me sadaki nera miliyan goma da gidaje da motoci da kujerun makka
Aikuwa Yan kidan kwarya naji tafadi haka suka hau kida suna Waka suna murna zasu samu kudin da Basu taba samuba lami rawa take tana juyi Yan uwanta namata liki umma tashigo tahau Mata liki
Babu zato Daga soro sukaji maroki nacewa Allah yayarda aure yadauru andaura auran hauwa malam Musa da alhaji shazali Akan sadaki nera dubu ashirin masu kidan kwarya sunaji maroki yafadi haka suka tsaida hannunsu suka Dena kida Dan suji me ake fada daga waje maroki yakara cewa kowa yasheda sadaki nera dubu ashirin amarya tayi goshi masu kidan kwaryama cilli sukayi da abin da suke kada kwarya
lami natsaye segani akayi tafadi akasa yifff ko motsi batayi dagudu akayo kanta ana Kiran sunanta ruwa aKa zuba Mata Taki ta motsa kirjinta akahau dannawa ana yaiyafa Mata ruwan sanyi sannan ta farfado tana bude Ido tace Ina miliyan goma da gidaje kumanisu narike ahannuna
Umma tace dubu ashirin daiko lanlai lami ki godewa Allah yarki tayi goshi sadaki har nera dubu ashirin miliyan goma tahaifi ashirin Ina tayaki murna Allah yabada zaman lfy augo yace baze shigo gaisuwar sirikaiba sauri yake yakumace agaya Miki zeturo motar daukan amarya da karfe biyar na yamma ko nace motoci tuba nake Bari naje tinda kin farfado nabar tatsotse awuta Kar ta Kone inanan
Sadiyace da aliyu suka shigo atare abin shashaawa yaransa natake musu baya malam nabiye da su
maroka se kirari suke musu sun tsaya daga soro suna cewa hajiya sadiya Mata awajan alhaji aliyu me azurfa godiya muke kaga matar manya masu ruwan kudi ana ganinsu kudine yake mgn ajikinsu
Haba masu kidan kwaryama ai se suma suka Kama doka kwarya suna musu Waka
aliyu har zeshiga dakin umma yadawo yakama hannun sadiya sukaje wajan masu kidan kwarya yafara musu liki yanawa sadiya rada akunne se gani akayi tasa hannunta acikin aljihun aliyu taciro kudi masu yawa tafara likawa aliyu shima ita yakoma likawa guri yakaure da Buda yaransa se kakkaresu sukeyi sunnan suka fito suka shige dakin umma
Lami tagumi tayi tana kallo Dan takoma abar tausayi kowa yawatse daga wajanta tinda ta farfado kuka takeso tayi ko zataji tadi azuciyarta takasa se Jan zuciya da take tayi jitake tana neman tafara hauka da rarrafe tajah kafafunta tashige daki
Du abinda lami takeyi su tala na ganinta me su tala zasuyi inba dariyaba suna ihu du da ransu abace yake da ganin sadiya da aliyu da sukayi musamman likin da sukayiwa junansu gakuma sunga sadiya ta canza tayi fari tayi kiba fatarta tamurje kana ganinta kasan tana cikin kwanciyar hankali
Ashe aliyu yadade da zuwa lokacin da suka iso mutane sun tare hanya Babu ta inda Sadiya zata ratsa tashige amota yabarta yafito shi yaje wajan daurin auran Dan haka sadiya Bata shigo cikin gidaba se da aka daura sure
Alhaji shazali naganin aliyu yarude yaje wajansa da rawar jiki yahau gaisheshi yace yallabai Ashe zakazo kaimafa Yar uwar amarya kake aure ko nace yayarta ai yallabai kayi Saar Mata Dan nasan labarin Yan gidan malam gaba Daya Dan Allah yallabai arufamun asiri Kar agayawa malam koni wanene atemaka yallabai ai natuba nadena komai
Aliyu yace hm alhaji shazali kenan Ni yazaaiyi nayi haka tinda Ina maka fatan shiriya nidai abinda zance maka Akaji tsoran Allah kamar yanda nasaba Gaya maka kakuma rike Masa yarinyarsa da mutunci karka cutar da bawan Allah itama yarinyar karka cutar da ita
Yace yallabai angama zanyi du abinda ka fadamin godiya nake
Acikin gida aliyu gaisawa sukayi da umma da Yan uwanta har su lami du sun gaisa yaciro kudi masu yawa yabawa lami agaban su tala Ido suka,hau zarewa har yafice daga gidan sadiya ta gaisa da Yan uwa sosai
farida se shinshigewa sadiya take umma tajawa sadiya kunne Kar tabar farida tashiga jikinta sosai ita bata yarda da faridaba da abinda take nufi Kan sadiya tace Mata ko Dan iyayansu Kar tasaki jiki da ita har
Da yamma karfe biyar motar daukan amarya tazo ai da gudu habi da tala suka yi hanyar waje Dan suga irin motocin da akazo daukan amarya da su ai suna lekawa suka hau dariya har da Buda akori kurace guda biyu da bus guda biyu ai dagudu suka koma ciki suna sanarwa mutane har daki suka samu lami suna Gaya Mata suna dariya mgnma takasa du akunyace take
Umma shigowa dakin lami tayi tace to Ina amarya tafito murakata gidanta Dan nayi alkawari nice agaba wajan Kai amarya
Haka akafito da amarya tana kuka Dan wulakancin da alhaji shazali yaimata yabata Mata Rai Dan bahaka sukayi da Shiba abinda yadada Bata Mata Rai tayi ki,ranshi awaya akashe haka akasata abus guda Daya tare da kawayanta sauran akori kurar da bus din da tarage yankai amarya suka shiga zuwa gidan alhaji shazali awani katan gida motocin suka tsaya gidan Babu lefin kana gani kasan gidan me kudine se dai abin mamaki yankai amarya nashiga sukaga ai katan gidane daga gani gidan yawane da mutane da yawa aciki wata dantijuwar matace Tai musu jagora zuwa dakin da zaa sauke hauwa dakine ciki da falo me Dan girma daga ciki gado me runfane aciki irin nada dinnan da aka Gama yayinsa se wasu kujeru da aka jera alalo Suma Basu masu tsada bane