Halimatus sadeeya

kuka wiwiii hauwa take ta rusawa yankai amarya du sunzata kukan rabuwa da iyaye da Yan uwa takeyi nankuwa bahaka bane kukan bakinciki takeyi Dan taci buri sosai akan auranta kamar yanda akayi na sadiya alhaji shazali yawulakantata
haka yankai amarya suka koma gida da magana abakinsu su habi ai sunsamu abinyi se habaici suke tasaki Babu Wanda yatanka musu Dan kowa yasan yanda lami Tai tasakin bakaken maganganu acikin mutane suna shiga gida lami suka samu suka Bata labarin komai na gidan hauwa suna ta gasa Mata bakar mgn takasa mayar musu
Umma ita tausayi lami takoma Bata har ita hauwan
Sadiya da laasar aliyu yaturo mota takoma gida ba da ita akaje Kai amaryaba
Yau alhaji bushasha yaje har gida yasamu nusaiba da mgnar yanasan yaauri malika ta,shige Masa gaba wajan neman auran malika lokaci guda wani bakinciki yakama nusaiba saboda gani take malika tafita masu kudine suke zuwa su aureta
Alhaji bushasha yagane me nusaiba take nufi bataso Tai Masa hanya yace nusaiba indai Kika yarda Kika shigar Dani wajan malika har na aureta kema akwai kyauta me tsoka da Zan miki Kuma ga albashir da Zan Miki akwai wani abokina me kudi da yake zaune adubai yace na samamai matar aure me hankali bazawara ta nunawa jamaa Kuma da ita zetafi Dubai su zauna acan tare
Shuru nusaiba tayi can Kuma tace Yana da sakin hannu sosai
Alhaji bushasha yace eh sosaima Zan kawoshi ki ganshi Kuma nasan tashin farko kyautar mota ze Miki
Nusaiba Shawara da zuciyarta tashiga Yi tahau zancan zuci tace ko bazan aureshiba zanci kudinsa nasamu nazuwa wajan bokayena nakai aliyu amallakemin shi
Shidai alhaji bushasha nazarin nusaiba yake Dan shi yasan irin muguntar da yashirya Mata ita da malika burinshi su yarda su shigo hannu
Nusaiba tace na yarda alhaji bushasha zanyi mgn da malika kadawo gobe zan rakaka har gidan da take zaune
Alhaji bushasha yace to ngd kudi yaciro dami guda yabata aikuwa tarude godiya tahau yimasa har wajan motarsa ta rakashi yatafi
Tana komawa gida malika takira awaya ta tsarata sosai tace inaso kiyarda da aurannan kawata malika ko Dan aliyu kinuna Masa cewa har yanzu da sauranki maza na Rubibinki Kuma Kinga alhaji bushasha yamafi aliyu kudi Kinga koshi aliyu inyaji Wanda kike aure se yaraina kansa yasan cewa kinfi karfinshi yanzu kiyarda musha biki kawata tinda kindade da Gama wankan jego kinyi kwari gobe har inda kike Zankawo Miki shi
Malika lokaci guda tayarda da mgnar nusaiba Dan haushin aliyu takeji Sosai Dan Daman neman abinda zatayi Dan aliyu yaji labari yaji haushin takeyi
Yau aliyu yaje gai da ummi bayan sun gaisa
Ummi tace aliyu dafatan,dai Kai da sadiya Babu wata matsala Kuma kanajin dadin Zama da ita Dan Allah rokona kullin agareka kaji tausayin sadiya kazame Mata madubu ka haskaka zuciyarta da farinciki yau zan baka labarin rayuwar da sadiya tayi agidansu da Kuma kishiyoyin mahaifiyarta
Labarin sadiya ta,bashi tin daga zamanta nagida da tayi da auran da batayi da wuriba da irin tsanar da Yan uwanta da suke uba Daya suka Mata da tanar da su habi suka Mata ita da mahaifiyarta har hawan jinin da takamu da shi
Lokaci guda aliyu yahau tinanin rashin lfyar da sadiya tayi har yakaita asibiti da yayi lokacin bema San zatazo gidansa aikiba Yakuma tuno irin wulakancin da su malika suka Mata da Kuma kula da su Amira da takeyi alkawari yadauka azuciyarshi ze gyara dangantakarshi da sadiya zejata sosai ajikinshi suzama abu Daya tafiya yakeso yayi Yana dawowa komai zeyi dedai shi da sadiya
Numfashi yajah yace ummi wlh labarinta yabani tausayi nakuma dadajin tausayinta azuciyata yanzu tafiya zanyi zuwa America da Kayan da Zan shigo da su Dan haka sadiya da su walid zasu dawo wajanki kafin nadawo Kar kadaici yadamesu
Ummi tace aliyu kenan Amira da Walid sune zasu dawo wajena Amma Babu sadiya da ita zaku tafi yadace kayi hankali daga Kan malika tinda Allah yamaka canjin alheri ko wace kasa zaka tafi kafarka kafar sadiya hakan shi zekara muku kusanci atsakaninku kaje kahadomun Kayan su Amira sudawo Nan su hadu da Yar uwarsu Amina Daman kullin in munyi waya da su se suce nakawo musu baby Amina Kuma banaso kamusa min kayi abanda nace
Dole aliyu yayarda da mgnar ummi Amma shi bahaka yasoba haka sukayi sallama da ummi yatafi gida da tinani azuciyarshi Yana shiga falan gidan yasamu sadiya da su walid suna wasan buya su Amira sun daure idan sadiya da dankwalin kanta se laluben inda su Amira suke take batama,san aliyu yashigoba walidne yaleko daga wajan boyansa yaga aliyu atsaya Yana kallan sadiya walid yataho ahankali wajan aliyu rada yai Masa
yace daddy Dan Allah karka nunawa mommy inda muke dasauri yakoma inda yaboye
sadiya se laluben inda su Amira suke har takai inda aliyu yake shidai kallanta kawai yakeyi Yana tsaye faga inda yake Bata zataba taji tayi karo da kamar mutun Kuma babba kirjinshi tashafo Dan ta dada tambatarwa da lalube tashafo furkarshi taji tatabo kasunba me laushi takuma tabo hanci da sauri tasa Daya hannunta ta kunce daurin Dan kwalin da yake daure a idanta aliyu tagani tsaye agabanta ga hannunta nakan furkarshi ihu tabude Baki zata kurma dasauri yasa hannunnshi yarufe bakinta
Yace ke lfy Zaki taramana mutane nine Baki saniba
Bakinta rawa yafara tace Dan Allah kayi hakuri su walid nake nema
Kafin yabata amsa su Amira suka fito suna ihu suna cewa mommy takama daddy shine dayi mu Bata kamamiba daddy Kai zskayi yanzu mommy rufemasa fuska
Aliyu yace Kai su Amira aini nagirma bazan iya wannan wasanba na barwa mommy nawa Tai muku Amma se anjima yanzu zataje ta sharemin dakina kuje kuyi karatu kafin tagama
Dagudu suka tafi inda suke karatu itakuma yakama hannunta zuwa dakinsa gabanta se faduwa yake suna shiga daki
yace matsoraciya Ni gyaran daki zakiyi min Amma Kan kifara da mgnar da zamu da ke
Zaunar da ita yayi abakin gado shima yazauna kusa da ita sosai tanaji jikinsa na gogar nata Kai tasunkuyar tana wasa da hannayenta Ido yakura Mata Yana ta kallanta
Yace Daman mgnar da zanyi dake tafiya zanyi zuwa America Kuma dake Zan tafi dasauri tadago Kai tana kallanshi mamaki mgnrshi tabata su Amira gidan ummi zasu koma kafin mudawo yanzu kihada kayanki da du wani Abu da zakiyi anfani da shi acan Dan zamu dade sosai acan zamuyi kamar wata uku ko biyu yanzu ki,sharemin daki ki gyaramin Kinga dakin yahargitse Kuma banaso Yan aiki suna gyaramin daki Allah yasa ummu Walid baraguwa bace kamar yarta amira
Murmushi tayi tace Daman se Tai shuru ta sunkuyar da Kai
Yace inajinki kifada Mana
tace nazata da su walid zamu tafi
Murmushi yayi yace ummi tace abarmata,su wani zuwan se mutafi da su
Kai tadaga Masa tatashi tahau gyaran dakin
Yana daga Kan gado azaune Yana kallanta takasan Ido Yana karewa jikinta kallo
Azuciya yafara mgn yace Babu karya Babu wata makusa ajikinta Allah yasa haka zata zarce da biyaiya Kar daga baya tafara abinda banaso narasa meyake damun zuciyarta Akan sadiya Ido yarufe yai kamar bacci yake
Har tagama gyara ko Ina kallan inda yake sadiya tayi taga kamar yafara bacci danhaka tayi hanyar fita daga dakin har tabude kofa zatafita taji
Yace Baki Gama aikinkiba saura gado
Tace nadauka bacci kakeyi
Sauka yayi tagyara ko inah tayi shinfidar gado Sannan tafita zuwa dakinta tahau hada kayanta tshada nasu Amira dadandare yakai su Amira gidan ummi har kuka sadiya tayi