Halimatus sadeeya

Ummace Kawai Bata dorawa yaranta tallah agida take saida Yan kulle kullan Kayan Miya irin su kuka magi dadai sauransu se sadiya da take yin awara kullin tafita kofar gida tana soyawa tana siyarwa yaran umma du suna zuwa makarantar boko da ta isilamiya da wani babban yayan umma yadau nauyin biyawa su sadiya kudin makaranta Yana kokari wajan temakawa umma Kuma shi yahana yaran umma suyi talla har Kayan abinci wani lokacin Yana turo Mata meyawa se ankwana biyu in yakare yadada turo Mata basosai take samun matsalaba se Dan abinda baa rasaba Dan haka du su lami suka dada tsanarta yanzu haka sadiya tagama secondary batasamu damar ciga da karatuba se isilamiya da take zuwa safe da yamma tana tafiya isilamiyar yamma karfe biyu na Rana ta dawo karfe biyar tana dawowa take sanaar awararta Allah yabata kasuwa sosai tanayi da yawa kuma kafin karfe Tara da Yan mintina tagama saidawa ta koma gida gakuma yanzu manyan yaranta maza guda uku da suke temakawa umma da yaranta har gobe su lami suna bakinciki da umma dandai ba yanda zasuyi da itane sun buga sun barta sunga Babu riba sedai neman fadanta da suke kullin Kuma Bata kulasu
Cigaban labarin
Aliyu ne yadawo daga tafiya wajan karfe Daya na Rana yadawo zuwan bazata yai Babu Wanda yasan zedawo yau se yaransa amintantunsa ne kawai yakira yagaya musu suzo su daukoshi in jirginsu ya sauka abinda yazo yagani agida yayi mugun daga Masa hankali yanda yaga Yan aikinshi masu kular Masa da Yara sunsa Masa Yara agaba suna ta duka kamar ba mutane suka samuba Kuma Yara kanana ranshi yayi mugun baci hankalinshi yatashi yanda yaga irin dukan da akaiwa kananan yaransa guda biyu hannu yasa a aljihu yakira jamian tsaro yasa masu gadi surufe Masa kofofin gidan gaba daya yanda Babu Wanda ze iya fita yakaraso yadauki yaransa yasasu ajiki se Mai da numfashi suke abin tausayi lamo sukayi jikin mahaifinsu ko mgn sun kasa Masa se ajiyar zuciya suke Ido yaruntse yanajin tausayin yaransa azuciyarsa da Allah wadaran halin uwarsu budu Ido yayi yasaukeshi Kan Yan aikin nashi da suka zube akasa jikinsu na Bari budar Baki yayi dakyar
Yace Kun bani mamaki su asiya me na rageku da shi arayuwarku wace irin kyautatawace bana muku saboda Kuna kula da yarana ai kobana Baku komai ai da na kowane Kuma iyaye matane dukanku babu Yara ke asiya ai kina da Yara kekuma Indo ai bazawarace ke Duda Baki taba haihuwaba wataran kema uwace kome yarannan sukai muku bedace kusa yarannan agababa kuhau dukansu kamar Kun samu wasu masu hankali ko Dan kunga yanda uwarsu take banzatar da su shine Kuma kuke wulakantamin yarana
Shigewayai yatafi ciki da yaransa Dan su asiya sunkasa cewa komai ga kunya tarufesu ga tsoro yarufesu sunsan ba zebarsu hakaba be dau matakiba Kuma sunsan karshan zamansu yazo agidan
Hannu aliyu yasa yabude kofar babban falan gidan tinkan yakarasa budewa yakejin wani irin Nishi natashi acikin falan dasauri yakarasa shiga falan dauke da addua bakinshi abinda yagani acikin falan yayi mugun daga Masa hankali Yar aikinsu me dafa Masu abinci me suna folina yagani da wani Kato atsakiyar falo azage haihuwar uwarsu suna tamka mashaa da sauri yajuya da yaransa waje yai maza yaja kofar falan ahankali yarufe du wannan abin da ake sunyi nisa basusan yashiga falanba har yaga mesuke aikatawa yafita jiyayi juwa na ibansa kamar ze Fadi dakyar Yana hada hanya yatafi Daya bangaran inda dakinsa yake da falansa yabude dakinsa yashiga yaajje yaran Shima yakwanta saboda sarawar da kansa yake ga juwa na ibansa rintse Ido yayi Yana Mai da numfashi can wayarshi Tai Kara yadaga daga Daya bangaran akece Masa jamian tsaran da yakira sun karaso yace abude musu su shigo surufe kardai subar kowa yafita seyace tashi yayi ze fita da sauri Amira tarikeshi jikinta narawa tasa kuka
Tace Dan Allah daddy karka tafi su Indo zasu zo su daukemu suyi ta dukanmu Kuma basa bamu abinci yunwa mukeji sune suke cinye Mana abinci
Walid yai saurin cewa yanzuma Dan munce musu yunwa mukeji cikinmu naciwo subamu abinci Amira na ta kuka shine suka rufemu da duka Wai mun damesu mun cika musu kunne uwarmuma basanmu takeba bare su Yan aiki asiya Kiran yaranta take tajuye musu abincinmu sutafi da shi gida mukuma muyi tajin yunwa ko ita da Indo su cinye Mana Kuma sunce in munje makaranta du ranar da muka cinye Kayan break dinmu bamu rago musuba se sun yankamu Kuma Kar mu ringa ci da yawa
Aliyu jiyai hawaye na zuba daga idansa sauri yayi yagoge Dan Kar yaransa su gani yace Babu inda zani kunji kuyi hakuri zuwa zanyi nasa adauke muku su asiya bazaku Kara ganinsuba Zan kaiku gurin ammi kuyi zamanku bame takura muku ku jirani yanzu Zan dawo
Ficewa yayi yabarsu suna ta murna
Karasawa yayi wajan yan,sandan bayan sun gaisa yaimu bayanin abinda yasa yakirasu
yace gasunan kutafi da su karku sakesu har se na nemesu Suma abasu wuya kamar yanda suka azambar da yarana da yunwa da duka bayan Babu abinda na ragesu da shi inkun Kama wayannan kuje can bangaran zakuga meyake faruwa Suma kutafi da su Sena nemesu Kan kufito da su ku canja musu kamanni Ina tuhumar namijin Akan shigomin gida da sunan aikata Zina Ina tuhumar macan da kawomin gardi gida cikin iyalina afalona suna aikata Zina kuma nasan bayaune farkoba Daman ansha kawomin karar su banaso nahukunta mutun Akan lefin da bangani da idonaba yau Kuma Allah yanunamin du abinda yake faruwa da idona Dan haka Ashe cc TV din gidannan daga nayi tafiya ake lanlatata Dan Kar nadawo Naga me yake faruwa Inna dawo zansa agyara Amma Ina barin kasar zaace talalace gashi yau da Allah yayi zamgani da idona nagani
Lokacin da Yan,sanda suka je inda su folina suke sun samesu kamar yanda aliyu yagansu Babu zato Babu tsammani sukaji saukar duka Tako inah dukansu ake ba sausautawa Dan azaba namijin yasauka daga Kan folina saboda zafin dukan da ake musu sun rasa inda kayansu yake bare su dauka surufe jikinsu seda akai musu lulus aka kunbura musu jiki kafin aka barsu sukasa Kaya aka fito dasu akasasu amota su asiyama se da akai musu shegen duka kafin suma akasasu amota Daya da su folina akatafi da su
Yawan comments dinku shine kwarin gwiwata masoyana godiya nake ????
New writer’s
Hakan Take
*Husba’ahfama* ????????????
*’Yar kwalliya* ????????????
????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????????
????????????
????????????????????????
????????????????????
????????????????
????????????
????????????????
????????????
????????????
???????? *HALEEMATUS SADEEYA*????????
Written by *HUSBA’AHFAMA*
IG *officiall_husba’ahfama*
Facebook *Real Husba’ahfama*
Follow me on Wattpad *@ Real Husba’ahfama*
*Bismillahir Rahamanir Rahim*
5-6
Aliyu wajan yaransa yakoma ransa abace haka yadaure yai musu wanka yashiryasu se mita suke mai yunwa sukeji Yana rarrashinsu har yasamu yagama shiryasu yace kunsan yanzu Ina zamu gidan ummi zamu acan zakuci abinci acanma Zan baroku
Murna sukahau yi amirace tace daddy in ka kaimu bazamu dawo nanba ko wajan ummi zamu zauna se dai kana zuwa kana ganinmu ummi na sanmu Bata Mana komai ita da abbah kome mukeso zasu bamu zamu tafi da kayanmu duka can ko Walid
Yace eh bazamu dawoba can yafi Dadi zamuna wasa da su Anisa in sunzo