Halimatus sadeeyaHAUSA NOVEL

Halimatus sadeeya

Nusaiba tasumu nasarar hada alhaji bushasha da malika soyaiya me karfi tashiga tsakaninsu ruwan kudi sosai alhaji bushasha yakewa Malika abin na batawa nusaiba Rai kullin tsanar malikane yake karuwa azuciyarta har alhaji bushasha yaturo magabatansa neman auran malika in da suka samu daddy bayanan ko da yaiyun malika suka kira daddy suka Gaya Masa mgnar auran cewa yayi aishi yanzu bayarsa bace baburuwansa Yar uwarsuce in sunga mijin da takawo yamusu sushige gaba ayi komai Dan haka sukabi mgnar daddy sukaba da malika ga alhaji bushasha bawa lokaci me tsawo akasaba malika da mommy se shirye shirye aketayi

Tala tinda taga lami ta aurar da hauwa hankalinta yatashi tamatsawa asiya Akan itama tafitar da nata mijin tayi aure tinda hauwa tayi sadiya tayi Kuma tajawa asiya kunne in tatashi kawo mijin aure Kar ta kawo talaka se dai mekudi

Asiya tace haka kikace me kudi kikeso babarmu

Tala tace eh

Asiya tace kinsamu mekudi babarmu kingama Zan Gaya Masa yafito muyi aure

Baki tala tawashe tace yauwa kokefa Yar Albarka

Asiya nafita tallah bayan tasiyar da abinci Kai tsaye gurin saurayinta rodi tatafi shugaban yandaba tasameshi Akan yafito tace rodi iyayena sunce nafito da mijin aure babana bashi da matsala kowa nakawo Masa ze auramin se dai matsalar daga wajan babata yake tace se dai nakawo me kudi nikuma Kai nafiso banasan alhaji da sauran da muke muamula da su

Rodi yasa wani ihu yace ai yarinya da tsautsayi yasa kinzabi wani wlh da har gidan Wanda Kika aura zanna binki kumafa kinsan asiri Zan rufa Miki saurace ke Dan nasan jarabarki asiya bani kadai kike biba yanzu kije kisamu dagus dinki kice Masa zanzo neman auranki yashirya ita kuma tsohuwar Taki zamu rufata ayi auran daga baya taji koni wanene

Asiya tace to

Yau dawuri takoma gida daga wajan tallah tana ajje Kayan tallanta tatafi wajan sanaar malam ta sameshi da mgnar rodi Bata boyewa malam komaiba Akan rodi takuma gayawa malam dokar tala Akan mijin da takeso ta aura

Malam yace hm asiya kenan nadade da sanin ko waye rodi da Kuma abinda yake aikatawa nasan iyayan rodi Dan babban malamine yakangare yakoma haka du wani shige da ficenku ke da shi nasani mutane nazuwa su fadamun nidai kullin addua nake binki da shi Allah yashiryeki shima rodi Allah yashiryeshi alhamdulillah tinda har zakuyi aure du da abinda kuke aikatawa ita Kuma tala nasan burinta akanki kirabu da ita zaayi auranki da rodi dagabaya tagane gaskiya shi Kuma rodi Allah yasa silar shiryuwarsa kenan kice Masa yaturo ayi komai kitare yafimiki wannan yawan tallar da kikeyi

Murna asiya tahauyi tanawa malam godiya Kiran rodi tayi awaya tagaya Masa malam yace yaturo ya,yarda tana komawa gida ta gayawa tala alhajin da zata aura ze turo

Murna tala tafara tasaki Buda tace Nima tawa Yar zata fito zata auri me arziki kamar yanda wasu suke takama

Babu wani Bata lokaci rodi yagayawa mahaifinsa yasamu matar aure ance yaturo mahaifinsa yayi murna yahada Yan uwansa sukaje suka nemawa rodi auran asiya sunkai kudin aure da du wani Abu da akeyi ansa ranar biki wata biyu

asiya da malam sun tsara tala Akan mijin da asiya zata aura me arzikine sosai itakuma tayarda

 

 

Jikin sadiya yayi sauki Babu lefi aliyu se tattalinta yake Yana riritata kamar kwai yau kwanansu hudu da angwancewa Babu lefi tana tafiya sosai ba tare da dingishiba Dan haka aliyu yashirya musu tafiyar da zasuyi zuwa rasha aliyu yakai sadiya gidan ummi tayini taga su Amira da Amina jinjirar da malika tafita tabari tayi wayo sosai washe gari yakaita gidan iyayanta tayini tayi sallama da su umma da malam

da su lami sukaji Ina sadiya zata abin yataba musu Rai karara suka nuna bakincikinsu afili se habaice habaice sukeyi umma da sadiya Basu kulasuba se dare aliyu yaje yadaukota washegari jirginsu yatashi zuwa kasar rasha

Sun Isa lfy suna sauka taga wasu hadandun motoci ajere securityn sa atsaye suna jiransu mamakine yakamata yaushe suka taho Dan ita tasan batare suka shiga jirgi da suba tasan dai tare sukazo airport bude musu mota sukayi suka shiga zuwa masaukinsu sadiya se kalle,kalle takeyi ganin tsaruwar da garin yayi aliyu nakula da ita murmushi yake ta Mata Yana yaba irin kyan da take da shi ga garin sanyi akeyi sosai tin amota take rawar sanyi Kai aliyu ya girgiza yacire rigar sanyin jikinshi yasa Mata yajanyota jikinshi yarungume wani sansanyan numfashi suka sauke atare yai Mata rada akunne Yar kauye Yar gidan ummi batasaba da sanyin kasarba dariya Zan tamiki ba ruwana

dariya tayi taboye fuskarta akirjinsa tace Sena gayawa ummina kana tsokanata ta karasa mgnar ashagwabe

Yace rufamin asiri Kar ummi Tai fishi da Ni kinsan yanzu tafiji da ke

Baki tatura cikin shagwabaTace Kai ba ka kwace ummaba

Kafin yabata amsa motarsu tatsaya bude motar akayi suka fito Yana rike da hannunta har cikin gidan da suka sauka gidansane da yasiya akasar gidane mekyau madedaici Babu abinda Babu acikin gidan

Yace ummu Walid ga gidanki nanan kasar Allah yasa yamiki ki duba du abinda kikaga be mikiba kifada acanja wani

Tace komai yayi Allah yakara Budi

rungumeta yayi tabaya yakwantar da kansa agefen wuyanta yace ummu Walid ke ta dabance awajena kome nai Miki bakya rainawa inajin dadin yanda kike karbar abin da nakawo Miki hannu binbiyu yanzu dai muje muyi wanka muci abinci mu huta kin sanfa Abu biyu nazoyi akasarnan cin angwanci da kasuwanci zamu Dan Dade akasarnan Ina adduar mukomawa ummi da umma da tsarabar baby acikinki

Hannu biyu sadiya tasa tarufe idanta tana murmushi

Yace ke nifa wannan kunyar Taki basanta nakeba gaskiya tana cutata tinda naware nake Miki mgn nacire kunya da shuru shuruna kema yadace ki ware kicire wata kunya musha soyaiyarmu kibude Baki kiyimin mgn banasan shurunnan da kike yimin ko se na dada yine yanzu nacire kunyar gaba Daya Dan Naga rannan ban cireta dukaba barima kigani yafara kokarin daukanta

Dasauri tajuyo ta rungumeshi tace Dan Allah kayi hakuri wlh zanna mgn in kamin mgn kaji cikin shagwaba takarasa mgnar

Dariya yasa yace matsoraciya muje muyi wanka to tinda kinji tsoro

 

 

.yau ake daurin auran Malika da alhaji bushasha awani karamin masallaci da ke unguwarsu aka daura auran malika da alhaji bushasha
taro sosai malika da nusaiba suka hada sun gaiyato kawayansu anci ansha anrakashe Wanda du alhaji bushasha ne yadau nauyi ba karamin kudi yakashe wajan auro malika nusaiba har bakinciki tafara Akan irin bushashar da taga alhaji bushasha yakewa malika

washegari akakai amarya gidanta inda alhaji bushasha yanunawa malika zata zauna in sunyi aure ba Nan yakaitaba har Kayanta ankai anjera agidan da yanuna Mata zasu zauna Yan jeran Kaya na tafiya yasa aka kwashe Kayan dakin malika aka mayar da su gidan da iyalinsa suke ciki yasa Yan rakiyar amarya suka kai malika gidan babbane

alhaji bushasha karya yaiwa malika yace Mata matarsa Daya Ashe ba haka bane matansa ukku itace ta hudu Kuma auri sakine da shi du matar da yaaura Bata dadewa yake sakinta azabar gidansama ta Isa tasa matar da yaaura tagudu Yana da ya’ya dayawa zasukai Susu talatin da wani abu yaran gidan Kuma du kananane manyan cikinsu Basu da yawa saboda auri sakin da yakeyine yasa yake da tarin Yara Kuma kanana du wacca yaaura se ta haihu yake sakinta du matar da yasaki se yakwace dansa sannan ze barta tatafi gidansu wato alhaji bushasha awaje yake alhaji bushasha Amma agida sarkin manmakoma yafishi sakin hannu awajan iyalinsa baya kyautata musu ta ko Ina dedai da abinci bawani me Dadi yake siyowa yabawa iyalinsaba kusan kullin tuwone safe da rana da dare ranar da akasamu canji da Rana to garin kwakine zaakwadanta aci ko adafa shinkafa Yar hausa Kuma ahannu ahannu abincin gidansa yake bawani koshi akeba daga tuwan har kwadan garin da shikafa da yajin da ake dafawa agidan alhaji bushasha bawasu masu Dadi bane Dan bawani kudin cefanen kirki yake bayarwaba Kuma abincin gidansa shi yake aunawa da kansa du ranar da mace take da girki agidan shi zebata da kansa amatansa uwargidan,sace tafarko suke atare har yanzu ko yaji batataba yiba tin lanlen fari itama hakurintane yasa take har wannan lokacin Bata fitaba suturar kirki Babu agidan alhaji bushasha daga matan har yaran bayi musu sutura yakeba daga sallah se sallah shima in yagadama Suma Kayan bawasu masu tsadabane matansa saboda yunwa ko wacce in kaganta kamar ka bushe haka suke rigama Bata Zama ajikinsu zamewa take saboda Rama kana ganin matansa kasan suna cikin matsala dedai da yaransa ba makaranta me tsada yasasuba Wanda yaran talakawa suke zuwa ita yaransa suke zuwa du ranar da yaro yazo yace Masa ance yakai dari biyar amakaranta tofa ranar Babu kwanciyar hankali agidan bushasha kafin yabayar se ankai ruwa Rana dashi gashi mutunne me mugunta bayaso yaga matansa sunci gaba ko Sanaa bayabarinsu suyi bare su rufawa kansu asiri yaauri Mata da yawa da suke aiki suna shiga gidansa ze hanasu zuwa se dai su zauna agida alhaji bushasha bayacin abincin da akadafa agidansa sedai yaci medadi awaje ko yashigo da shi gida ammafa Babu meci Allah yabawa alhaji bushasha kudi me yawa Amma kudin badai iyalinsa suciba sedai nawaje suci musamman Mata Kuma manemin Matane duda matan da yake da su agida Basu isheshiba

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button