Halimatus sadeeyaHAUSA NOVEL

Halimatus sadeeya

Makika najin abinda baraka tace gabanta yayanke yafadi jikinta yahau rawa wani kukan bakinciki da nadamar auran alhaji bushashane yazo Mata lokaci Daya tana jawa nusaiba allah ya,Isa tindazu take Kiran nusaiba Taki dauka Kuma wayarta akunne har sako tarubuta tatura Mata Amma Bata Bata amsaba tashiga tashin hankali sosai Baki narawa malika tahau yiwa baraka godiya da temaka Mata da tayi baraka nafita malika takira mahaifiyarta mommy tawaya tana dauka tafashewa mommy da wani mahaukacin kuka

Tace nashiga uku mommy nusaiba tacuceni tabani shawara naauri alhaji bushasha nakai kaina inda zaa kasheni mommy wlh alhaji bushasha mugune bashi da imani besan darajar Dan adamba bashi da mutunci

Nan tagayawa mommy abinda alhaji bushasha yai Mata daran jiya

Mommy tace nashiga uku Ni rukaiya Amma nusaiba miguwace Kuma Nima tinjiya da dandare nake kiranta awaya Taki dauka Ni hajiya zaliha tace taga nusaiba akofar kaffanin aliyu tana mgn da masu gadi nifa nafara zargin nusaiba Amma zanyi biccike akanta in Nagano abinda nake zargi akanta wlh se na wulakantata yanzu shi alhaji bushasha Daman bashi da mutunci haka afuska kamar na Allah Ina murna kinrabu da aliyu Ashe har gara aliyu tawani wajan Akan alhaji bushasha barni dashi Zan kirashi yazo har wajena wlh Sena zageshi zanrama Miki Ni da shine

 

Hm mommy wannan ba aliyu bane ????

 

Nan mommy Tai ta rarrashin malika tana Bata shawarar yanda zata rabu da bushasha lfy sannan sukayi sallama takashe wayar ta ajje

Alhaji bushasha natashi daga bacci yasa baraka tahada Masa shayi me kauri da biredi da wainar kwai yaci yakoshi agaban malika ko tayi bemataba se lasar Baki take yaki Bata har yagama cinye kayanshi duka yamayar da Kayan shayinsa dakinsa yakulle

itakuwa malika wannan tuwo da aka kawo Mata tana ganinshi zataji wani amai yataso mata kasa ci tayi haka taleko tabawa wani yaro tace yakaiwa baraka tagumi tayi tana tunani ga yunwa na damunta tarasa abin karyawa ga tanemi jakarta da kudi yake ciki tarasa bare tasayi wani Abu taci nankuwa Bata saniba nusaibace tadauke tafice da ita Dan mugunta irin na nusaiba

Tana wannan tinanin taji alhaji bushasha ya kamota yaturata Kan gado yahaye kanta tanaji tana gani yaci gaba da shaaninsa ga yunwa na damunta ga jarabar bushasha yasata agaba

 

 

Amarya sadiya da ango aliyu amarcinsu sukeci wata shakuwace me karfi tashiga tsakanin sadiya da aliyu har basaso daya yai nesa da Dan uwansa in aliyu yafita wajan kasuwancinsa kafin yadawo kewa ta ishi sadiya shima Kuma yanacan Yana tunaninta Kira kuwa awaya tsakanin shi da ita Babu adadi Abu kadan aliyu ze kirata yaji lfyarta itama haka take kiranshi taji lfyarshi

yau tinda yafita tin safe besamu yadawoba se dare aiki yamasa yawa akwai Kayan da yasiya yaturasu gida yau ko waya besamu yayi da sadiya ba tinda yafita wayarma acikin mota yabarta saboda aiki yamasa yawa du hankalin sadiya yatashi Babu irin Kiran da batamasaba be daukaba kuka tayini tanayi ko abinci takici tana tunani ko wani Abu yasamu aliyu ko Kuma lefi Tai Masa Bata saniba yaki daga wayarta gashi ita batasan ko inaba akasar mutane bare tafita nemoshi ko ta tambayi wani ko yaga mijinta lokacin da aliyu yashigo yasamu tana zsune Kan kujera tana ta gyangyadi ga hawaye yabushe afuskarta ga idanta har ya kunbura saboda kuka da Tasha tausayi tabawa aliyu

Ahankali yasunkuya agabanta yasa hannu yahau shafa fuskarta Yana mgn ahankali yace haskena yau na Miki lefi aiki yamin yawa bansamu naji lfyarkiba bare nadawo gida na ganki

wuyanta yataba yaji zafi rau Ido tabude da taji muryarshi kamar amafarki ga tabata da taji yanayi tana ganin da gaske shine tawani fashe da kuka tafada jikinshi atare suka sauke numfashi rungumeta yayi Yana rarrashinta Yana hura Mata iska akunne

Mgn tafara tana kuka tace abban Walid Ina kashiga haka tin safe hankalina yatashi se kiranka nake awaya kaki dauka Dan Allah meyasameka ko lefi nai maka ban saniba wlh ko girki na kasayi bare nici abinci shawarar fita nemanka nakeyi kadawo yanzu

Tausayi tabashi sosai yaji kaunarta nadada shiga ransa wani Dadi yaji sadiya tadamu dashi haka ko Bata sanshi yasan tadamu da shi

Yace wlh Babu lefin da kikayi min tauraruwata aikine yasha kaina bansamu na dau kirankiba wayarma Bata hannuna amota nabarta ko su zaiyanu ban barwa wayoyinaba yau lfyta kalau Babu abinda yasameni se aiki da yaimin yawa kidena kuka haka ya Isa Kuma in Kinga nafita nadade irin haka karkice zakifita nemana bakisan ko inaba Bata zakiyi Ni Kuma ba bako bane akasarnan na Dade Ina zuwanta kidena daga hankalinki haka kinji aiki namin sauki ko Ina nake Zan kiraki naji lfyarki

Dagota yayi daga jikinshi yasa hannu biyu yatallafo fuskarta yakura Mata Ido itama shi take kallo Ido suka hada kasa jure hada Ido dashi tayi tarufe idanta murmushi yayi yasa harshansa Yana lashe hawayen da ke zuba a idanta tanajin hucin numfashinsa afuskarta

Cikin sanyin murya yace tashi muje nahada Miki shayi Kisha kafin kici abinci gashinan na shigo Mana da shi haka kawai zuciyata tagayamin bakici abinciba yau Dan haka nashigo dashi yini zuciyata tayi tana begenki haskena du inda nake zuciyata na tunaninki kin Gama siye zuciyar aliyu Babu kowa acikinta se ke Daya da narufe soyaiya natsani Mata ko kallansu banasan yi yau se gashi kin wanke lefin da nake ganin kusan ko wace mace dashi da nadauka ko wace mace halinsu Daya Basu da kirki da tarbiya Ashe bahaka bane akwai irinki masu hankali da nutsuwa da sanin yakamata da tarbiya HALIMATUS SADEEYA kin Zama Barin jikina kin Zama zuciyata kinzama jini da hanta ajikina gashi kin kaunaci yarana da zuciya Daya

 

Wani farincikine yarufe sadiya tahau murmushi kamar ba itace take kuka yanzuba tace Nima kazama haskena mijina uban ya’yana Nima zuciyata yini tayi da begenka Ni nasan irin tashin hankalin da nashiga da ban ji lfyarkaba alhamdulillah tinda kadawo gida lfy kaunarka tagama mamaye zuciyata aliyuna hannu biyu tasa tarufe fuskarta

Farincikine yamamaye zuciyarshi ji yayi tafi kowa iya Kiran sunanshi yace nifa banasan gulma meye Kuma najin kunya nifa kunyarnance banaso wlh cutata takeyi yau Ina cikin farinciki matata tauraruwata haskena tabudi Baki tace tana Sona tana kaunata kamar yanda Nima nake Santa nake kaunarta Allah yaiwa iyayanmu Albarka da suka hadamu Ni tashi muje kin gaba birkita bawan Allah aliyu da kaunarki

Daukanta yayi yai kicin da ita suna ta dariya da farinciki kana ganinsu kasan suna kaunar juna Kuma suna cikin kwanciyar hankali

 

 

 

[ad_2]

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button