Halimatus sadeeya

Kai yagirgiza azuciyashi yace Allah sarki yaro inda ake sanshi Nan yakeso Dan Allah yanzu Ina Dadi Yara basa mgnar uwarsu sedai wasu Dan abin haushima na kirata nagaya Mata abinda yake faruwa tataho gidan taki daga wayata karshema kashe wayar Tai Allah kashiryi wannan baiwa taka Allah kakawomin sauki akanta Allah kaga irin hakurin da nake da ita Malika akwai Ranar da zakiyi kuka da idanki Akan yarannan lokacin kina binsu su kuma suna gudunki numfashi yajah mekarfi yafesar da iskar bakinsa
yakalli yaran suna bakin kofa shi suke jira hannunsu yakama suka fice zuwa inda motocinsa suke yaransa na ganinshi sunsan fita zasuyi aka bude Masa mota yashiga da su Amira direba yaja motar megadi yabude suka fice yaransa na binshi abaya har suka isa inda zasu wato gidan mahaifansa inda aka haifeshi mahaifiyarsa da ummi suke kiranta tin suna Yara har suka girma
ana bude musu kofa kafinma yafito su Walid sun rigashi fitowa da gudu suna murna suka shige cikin gidan suna kwallawa ummi Kira da sauri ummi tafito daga daki kana ganinta kasan tazuba kyau lokacin da tana da kuruciya kana ganinta kaga aliyu ita yayo kamarsu Daya sedai ita ta manyanta dagudu su Amira suka rinriketa har suna niyar kadata
Tace wlh Ni kun bani tsoro irin wannan Kira haka Ashe kune yau inah da manya Baki megidan da amarya ne sukazo gaisheni ku dawa kukazo
Sukace mu da daddy mukazo mu Nan zamu zauna bazamu komaba
Ana haka aliyu yashigo yace ai Daman nasani yau damun uwata zakuyi wlh in bazaku zauna kawaiba Mai da ku zanyi
Tace kajimin yaro Ina ruwanka Babu inda zaamai da su yaran da nake ta jaje nakeso na gansu Allah yasa ka kawosu zaka daga musu hankali Hala Yar mulki batasan Nan zaku,zoba nasan da Bazata bariba kamar yanda tasaba cewa zaa lalata Mata Yara in ankawosu Nan ko a Ina babansu yagirma har ta ganshi ta aureshi be lalaceba se yaranta maza kuje kuce tabawa tabaku abinci injini in bakwacin Wanda yake kasa kusa tadafa muku wanda kukeso kunji yan Albarka
Sukace to ummi
Da gudu suka tafi
Aliyu yace ummi nifa nimafa Zanci Naga yanzu kinfi San yarannan akaina ko fa gaisawa bamuyiba se kulasu kike Ni kinki kula
durkuwasa yayi ya gaisheta ta amsa
Salati tahauyi tace Amma girma yafadi da yaranka kake kishi Ni bazan baka abincinaba ai kana da Mata kaje ta baka ko dayake wannan sarkin yawan yaushe ma ta zauna agidan bare har takula da mijinta da yaranta
Fuskar,shice ta canja takoma ta damuwa yajah numfashi yasunkuyar da kansa kasa
Tace ikwan Allah yanaga daga fadar gaskiya ka koma haka ai bakarya nai mataba gaskiya nafada
Yace ko Daya ummi nima nagaji da halin Malika inaga hawan jini ko ciwan zuciya ya kamani
Nan yakwashe du abinda yafaru dawowarsa yau yafada Mata yace ummi daga yau na kwace yarannan daga hannunta sun dawo wajeki da Zama Zan Nemo Miki me tayaki kula da su Dan hidimar zatai Miki yawa ko nace na daukesu daga gidan dan dama bakula da su takeba batasan komai nasuba du Yan aikine suke musu tin suna jirajirai ko nono Bata Basu in suna jirajirai sedai Madara in nai mata mgn tace bazata basuba Kar nonanta yazube ta tsufa da wuri acuceta sefa na bude Mata Ido nanuna Mata bacin raina take daukan fida ta matsa musu ruwan nonan aciki Dan kazanta tabawa Yan aiki subasu susha watarama bazasu shaba sedai azubar Kuma in sunsha na fidar da ta matsa musu gudawa sukeyi cikinsu baci yake tinda ba kullin ake basuba Shima afidar da take matsawa abasu befi a irgaba har su girma Kuma Yan aikin wuya take Basu har dukansu take Dan haka basa dadewa suke tafiya tawajena kawai suke Jin Dadi wasuma Danni Suke zaune agidan Dan haka Yan aikin suke ganawa yaranta azaba in tamusu surama akansu suke Kuma iskancinsu yanda sukeso saboda ansakar musu kome Babu me kula da su
Ummi tausayin Dan natane yakamata tace aliyu kayi hakuri komai lokacine insha Allah Allah zekawo maka canji arayuwarka aure yadace kakara Zan Nemo maka Mata tagari Yar mutunci ka aura batun Yara Kuma zan nemo maka dattijuwace Wanda zatana kularma da yaranka tana Basu tarbiya kanma tafara aikin senayi bibcike akanta tukunna zatazo tafara Amma batun Wai yaranta sundawo hannuna da Zama be tasoba baruwana mutane zagina zasuyi ace da ranta da lfyarta bakuma rabuwa kukaiba na kwace Mata yaranta ko ita Malika bazata yardaba kasan in akwai abinda ta tsana ace yarannan sunzo wajena bataso yarinyar da ko taro muke adanginka bazuwa takeba seka matsa Mata take zuwa Shima in tazodin bawani dadewa takeba tana wani yiwa mutane kallan daidai tana toshe hanci take tashi tatafi in tagama wulakancin ta
Yace ummi batun aurefa narufeshi har abada bazan Kara aureba Daman can Mata dayace tsarina bani da raayin Mata biyu dayarma yanzu yanakare da ita bare nakaro wata natsani Mata yanzu in Banda ke da nakeso azamanki na mahaifiyata ko Yan uwana Mata kanlan irin halin Malika nake musu bani da lokacin dada kallan du wata mace bare har na aureta mgnar Yan aiki Kuma ummi Suma narufe dauka agidana in Malika bazatai du wani aikin gidaba amatsayinta na matar aure shikenan abar gidan ya lalace du Wanda yai sallama agidan yaga kazantar da ke gidan bani ze zagaba ita zezaga Dan Allah ummi kihakuri kibar yaran awajanki kome mutane zasuce sufada Malika ma kome zatayi sedai tayi na kwace yarana ai Ni nake da iko dasu itama akarkashina take
To naji mgnar aure bazanma doleba in Allah yanufa zaka Kara Dole kakara Amma mgnar Yara bazan rikeba Dole Kuma ko bazaka Kara daukan Yan aikiba Dole ka dauko me kula da su Walid zanbaka shawarrarin da zakasawa me aikin Ido sauran aikin gida Kuma Malika tayi tsakanin kune in Kuma Wanda zaa kawo takula da yaran tayarda zatana gyara gidan duka ana biyanta shikenan mgn yakare daga yau zuwa ko yaushe zaa iya samun Yar aikin ka kwantar da hankalika in Allah yayarda wanna Karan Babu abinda ze faru sema kayi alfari da Wanda zaa samu insha allahu Zan gayawa adamu yaran alhaji Naga Yana da rikwan Amana Kuma kaga yadade da alhaji kaima kasan halinsa ko adanginsa yasamo Mana inma Abu yafaru ta gidace Yar aikin zaa dau mataki Bari Zan fada,Masa irin kalar Yar aikin da mukeso Kuma Zan gayamasa gidan zata dawo da Zama gaba daya ba zuwa kullin tatafiba
Yace shikenan tinda kince haka du abinda kikace shi zaayi Allah yasa haka shiyafi alheri
Tace ameeeen
Yace yanzu dai bazan koma da yaranba se ansamu me aiki se nazo na daukesu Bari naci abinci natafi da in da zani
Tace to ga abincin can angama shiryama Bari naje Naga su Amira ko sun Gama cin nasu
Ko da aliyu yagama da gidan iyayansa be koma gidaba wajan Kayansa da yakaraso yaje dubawa be samu damar komawa gidaba se Tara da rabi na dare ko da yadawo Malika Bata dawoba abin yabata Masa Rai sosai har yaje yai wanka yai Shirin kwanciya bacci Bata da woba falo yadawo yazauna yana jiran dawowarta se kanlan agogo yake Bata shigoba se goma da rabi na dare tana taunar cingwam tashigo Babu sallama ko kallan arziki batai maiba bare yasamu darajar sannu da zuwa bare ta tambayeshi yaushe yadawo tana wata irin tafiya zata shige ta gabansa saboda bacin Rai besan lokacin da ya fincikota tadawo baya saura kadan tafadi
Tsawa tadaka Masa malam baka ganine ko nashiga harkarka banasan damuwafa matsa nashige