Uncategorized

HALIN GIRMA 15

LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu????????????_**Page 15*

____________________

*_INA MATA ƳAN ƘWALISA BA’ABOTA SON GYARA JIKI DA FATA SUYI ƘWANAS TAMKAR WATA ƊAN DAREN SHABIYAR?!_* 

_Ku marmatso kusa maza na kaiku kantin sauƙi na UMMU DUFAIL gidan sauƙi da biyan buƙatar MATA SARAKAN ado harma da MAZA ƴan ƘWALISA._

*_MATA da yawa kanso su koma Taurari ababen kallo da burgewa ga ma’abota kallo sai dai basusan ina zasu sami sinadarin kankaro wannan ƙyawu da mutuncinba._*

_To maza kuzo kusa dan Bilyn Abdull ta lalubo muku kantin sauƙi na Umm Dufail dakeda kaya masu sauƙi da gamsar da maison afani dasu_.

*_UMMU DUFAIL nada kayan gyaran jiki masu rahusa da inganci da gamsar da mai saya cikin ƙanƙanin lokaci kamar haka????????????_*

*Customers price list By Ummu Dufail FACE AND BODY*

 SCRUB=2500(300ml)

Face and body mango butter=3k (250ml)

Face cream= 1800

Corretor oil/vitamin C oil=2k

Fairness skin lotion= 2500

Hot chocolate skin lotion 2500

Serum (for Nuckles )2k

Nuckles cream (stubborn)3500

Mix fruits Arabian black =soap 1800

Mix fruit glycerine soap =1900

Beetroot=1900

Coconut, milk,egg..face soap=1200

Lavender mix fruit soap =1800

Body wash =1500

cleanser=1600

Hair spray =700

Hair oil =1500

Hair relaxer =700

Hair butter 1700

Shampoo =1500

Breast=oil 2k powder 2k

Strech marks cream= 2k

Beetroot pink lips =700

Baby care soap glycerine=1k

Baby care butter =1500

Shea butter baby soap =700

Tsumin tula =2200

Tsumin zinariya =1200

Sliming tea =1500

Amarya set =25k

Liquid Arabian black soap =1900

Cleansing water =1500

*_Zaku iya bibiyarta domin gani da ido ta Handle ɗinta na istagram da facebook kamar haka_*

Ummu Dufail @ Facebook 

Ummu Dufail @ instagram

Phone no: 07067943479.

_Ƴammata harma da masu auren karku bari ayi babuku. Dan gyara shine mace a wannan ƙarnin????????????_.

______________________

*Page 16*

…………Kamar da wasa sai ga ƙaramar magana ta zama babba. Dan kuwa dai Hajiya Iya da gaske take akan amshe Zinneerah daga hannun su Mama. Dan take a wajen ta ɗaga waya tai kiran Alhaji Kabir da dukkan ahalin gidan ke kira da suna Baffah.

     A rayuwa Alhaji Kabir bai haɗa uzirin mahaifiyarsa dana kowaba. Kai bama shi kaɗaiba har sauran ƴan uwansa da jikokin familyn babu mai sakaci da buƙatar Hajiya Iya. Dan ita ko wasan jika da kaka sai taso takeyinsa. 

    A cikin ƙanƙanin lokaci sai gashi a sashen nata. Hannu ya bama Abba suka gaisa yana faɗin, “Ai bansan ka shigo gidanba Alhaji Isma’il, dana fito mun gaisa”.

       Abba yace, “Wlhy yanzuma na shigo Yayanmu, nazo wucewa da ƙannenka ne, sai kuma ƴayanka dana kawo suma suyi gaisuwa su kuma gaida Gwaggo”.

       “Kai kai masha ALLAHU, lallai yau ka farantamin sosai sosai. Kuzo-kuzo ƴaƴan albarka ga babanku da baku saniba ko”.

     A nutse su Sadiq duk suka nufesa harda Zinneerah. Sai dai ita ta durƙusane daga gefensa kaɗan. Saɓanin su Abdul daya jawo jikinsa ya rungime. Sai da su Sadiq suka gama haishesa ya amsa da kulawa da tambayarsu sunyaensu da ajinsu nawa a makaranta kafin ya maida dubansa ga Zinneerah itama.

     “Ikon ALLAH, Inna wannan ai saikace Inno ta haifeta dan kamanninsu. Ɗiyata yaya sunanki?”.

       Zinneerah da kanta ke duƙe tana wasa da yatsun hannuna tace, “Zinneerah”.

“Masha ALLAHU suna mai daɗi kamar yanda kike ƙyaƙyƙyawa ɗiyata. ALLAH yay muku albarka. Ke ajinki nawa a makarantan?”.

     A take murmushi ya subucema Zinneerah tace, “Abba ss1”.

      “Kai-kai, kice Maman nawa bata wasa bace ƴar boko ce”.

      Barkwancin nasa ya saka dariya suɓucema Zinneerah. Yayinda hakan kuma ya sake saka ƙaunarta a zuciyar Alhaji Kabir dan nutsuwar yaran da tarbiyyarsu ya matuƙar birgesa, musamman Zinneerah ɗin da take mace.

    Kallonsa ya maida gasu Mmn Sadiq yana fadin, “You see. Gashi kun fara tara zuri’a amma basusan kowaba suma. Sai dai ko a hanya naci karo da Zinneerah ai nasan jini nace. Idan akaimin gaddama kuma har kotu zan kai dole a bani abata”.

      Sosai maganar tasa ta saka kowa dariya. Hajiya Iya tace, “Aini kiranma danai maka kenan. Dan nikam dai babu mai rabani da mai kama da Inno tazo gida kenan”.

      “Ina bayanki Innata. Dan haka Alhaji Isma’il dan ALLAH a taimakemu badan halinmuba a bamu Zinneerah, bamason a kalli hakan kuma fin ƙarfi roƙo muke gwiwoyinmu a ƙasa. Ƙila hakan ya zama sanadin gyaruwar zumincin dake neman kufce mana. Amma kuje dai kuyi shawara. Idan kuma akwai matsala dan ALLAH karkuji kunya ku sanar mana kanku tsaye zamu fahimceku insha ALLAH. Kunga ko ba’a bamuba sai take zuwa mana hutu ita da sauran ƴan uwanta lokaci-lokaci”.

        Cike da jin kunyar wannan roƙo nasa Abba yace, “Ai kunfi ƙarfin hakan a garemu”. Yay maganar yana duban Mmn Sadiq data duƙar da kai.

       Daga Hajiya Iya har Alhaji Kabir suma idonsu na kanta. Dan haka Alhaji Kabir yay saurin fadin. “To Alhmdllh, yanzu dai kuje kuyi shawaran nan da kwana uku sai muji yaya ake ciki kamar zaifi”.

      Sam Hajiya Iya bataso jin hakan daga bakin ɗan nata ba, dan sotai take yanke su tafi su barta da Zinneerah, saboda wata irin ƙaunar yarinyarce ta musamman ta shigeta lokaci guda. Amma sai tai shiru dan itama taga cancantar barinsu suje su shawarta ɗin. Amma kuma komai zasuyi tasa a ranta sai Zinneerah ta dawo hannunta da zama dan yarinyar ba karamin shiga mata rai tayiba lokaci guda. shi kansa Alhaji Kabir wani irin kaunar yarinyar yaji a ransa batare da yasan dalilin hakanba.

      Alkairi mai tsoka Alhaji Kabir yayma su Aliyu. kamar yadda aka koyar dasu tarbiyyar godiya haka suka shiga masa godiya da addu’ar fatan alkairi a rayuwa. Sosai hakan yay masa daɗi har cikin rai. Ya kuma kara jin girma da darajar su mmn sadiq sosai. Dan a wannan zamanin bama yaro tarbiyya shine mai matuƙar wahala ga iyaye aynun.

★★★★

       Tunda suka baro gidan babu wanda ya iya yin magana, sai da suna gab da shiga anguwarsune ma Gwaggo Maryama tai ƙarfin halin tambayarsu ina suka baro little kuma?.

      “Gwaggo ai baida lafiya an kwantar dasu a asibiti shida Umma”. Abdull ya bata amsa da damuwa a fuskarsa.

      Saurin juyowa Mmn Sadiq tai ta kalli yaron, kamar zatai magana sai kuma tai shiru ta maida kanta. Fahimtar hakan da Abba yayi ya sakashi faɗin, “Ban faɗa muku bane dan banason raba muku hankali biyu, amma jikin nasama Alhmdllh dan yanzu haka sun koma gida ta kirani cewar an sallamesu ga Naziru yaje zai maidasu gida. Bakomai ke damunsaba kuma sai zazzaɓin haƙora”.

     Addu’ar samun ingattacciyar lafiya sukai masa ita da Gwaggo Maryama. Daga haka suka ƙarasa gidan.

        Sai da sukayi sallar magriba suka huta Maman Halima ta shigo gaishesu ɗauke da Little daya rame sosai saboda yasha jiki. danma ALLAH yayisa mai kwaramniya ga karfin hali da akasan duk yaro da shi.

    Ƙiri-ƙiri sai gashi yana musu ƙyuya. Yaƙi yarda da kowa sai Zinneerah da kunya ta rufe kamar ƙasa ta tsage ta shige. Badan tasoba dole ta amshesa. Aiko ya wani lafe a jikinta yana kallon su Gwaggo Maryama dake jan kafarsa cikin tsokana tana fadin, “Aiko yaro nama fasa auren. Na maka saki goma sha biyu ni da kai baram-baram”.

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button