Uncategorized

HALIN GIRMA 15

     Dariya Mman halima tai tana tare masa. Ana cikin haka Maman Sakina ta shigo da yaranta wai zatai musu gaisuwa. duk da bataje can gidanba sai mmn sadiq bata nuna mata komaiba ta amsheta hannu bibbiyu suka gaisa tai musu godiya. 

   ______________,★

      Har washe gari babu wanda ya sake tada maganar komawar Zinneerah gidan hajiya Iya. Dan shi Abba ma ya fice kasuwa abinsa tun safe. 

       Sai bayan sallar la’asar ne Mmn Sadiq da abin keta cin ranta dai ta tunkari ƴar uwarta da maganar. “Maryama nifa inaga kodan matsalar gidan nan zanbar yarinyarnan ta koma wajen Gwaggo, sai dai kuma idan na tuna kar ace dansu masu arziƙi ne mukai haka abin na damuna. Sannan shi kansa Yaya na fahimci baison maganarnan”.

     Murmushi Gwaggo Maryama tayi tana gyara zamanta sosai. “Yaya Hauwa nifa kin ganninan babu abinda ya dameni da cewa ta mutane. Abinda duk ra’ayina ya bani na kuma ji raina ya aminta da shi kuma bai saɓama addinina ko al’adata ba to tabbas yinsa nake dan bama kaina farin ciki. Shi ɗan adam babu wani abu da zakayi a rayuwa ƙyaƙyƙyawa ko mummuna da zai iya gani bakinsa bai tankaba koda kuwa shi a tare dashi akwai abinda yafi naka muni ɗin da ƙyau. Dan haka ajiye batun cewa na mutane muyi abinda ya cancanta. Tun jiya nima cikin nazarin maganar nakeyi da shi Yaya kansa. Shi kawai abinda na fahimta da shi gani yake kamar za’a nuna gazawarsa akan riƙon Zinneerah tunda ba shine ya haifetaba. To amma abinda bai tunaba kuma shine sufa mutanen nan bawai sunsan bama shine ya haifitaba. Sai dai ni har cikin raina na yarda da komawar Zinneerah can gidan kodan wannan fitinanniyar matar tasa dake ganin Yayan ne kawai keda arziƙin da ake zuwa a ci”.

        “Maganganunki duk suna a kan hanya Maryama. Harga ALLAH inason basu ita domin ALLAH da suka roƙa da kuma darajar zumincin da suma sukayi dan shi. sai dai inason tai nesa da su Saude kodan ɓata mata suna da suke a anguwatnan miji zaima Zinneerah wahalar samu. Dan damafa ni ko wannan bata tasoba nayi niyyar ta biki can ku zauna har muga abinda ALLAH zaiyi”.

      “A to tunda hakane a bani abata mu tafi”. Gwaggo Maryama tai saurin faɗa tana dariya. Itama Mmn sadiq dariyar tayi. Haka suka cigaba da tattaunawa har tsawon wani lokaci kafin subar maganar da nufin jiran dawowar Abba yau su tunkaresa da batun.

       Zinneerah da batasan mike faruwaba tana can ɗaki da Little wanda a yanzu yake maƙale mata baya yarda da kowa a gidan sai ita da Gwaggo Halima. Sai su Sadiq idan yaso. Makarantama yau da zata tafi kuka yayta zabgawa sai daga baya ya haƙura bayan yayi barci ya tashi. Wauta da ƙuruciyar dake tattare da ita kuma yasa bata ɗauki hakan komaiba saima tausayin yaron da ƙaunarsa dake ƙara ratsata. Maganar komawa gidan Hajiya Iya kuwa bata damuba ba kuma ta mantaba. Sai dai bata wani ɗaukesa da muhimmanci ba balle taji wani abu a ranta game da hakan.

_________________★

        Koda Abba ya dawo gidan sai da Mmn Sadiq ta bari yaci ya ƙoshi ya nutsu sosai sannan ta tunkaresa da zancen kasancewar yau itace dashi dama. Shiru yay mata tamkar baijitaba. Ita kuma tunanin baiji ɗin bane ya sata sake maimaitawa kai tsaye. Sai dai yanda ya sake tsuke fuska ya saka tasha jinin jikinta kuma.

        Bai kulataba sai da ya mula dan kansa sannan ya fara magana a ƙufule. “Hauwa’u kun shirya hakanne dama saboda abinda ya faru a gidan nan kwanaki shida da suka wuce komi? Shin halin Saude ne baki saniba a gidan nan ne? Da har zaki yanke hukuncin rabani da Zinneerah bayan ni har cikin raina ɗaya na ɗauketa da duk wani yaro dake a gidan nan”.

      “Yaya kayi haƙuri dan ALLAH, sam ba yanda kake tunani baneba. Ni abinda yasama kaji namaka magana saboda mu toshe ɓarakar da dangin mahaifiyarmu ke ganin mahaifinmu ne ya assasata. Su daina ganin tamkar muna gudunsune. Sannan baiwar ALLAHn nan ka duba yanda suka ɗauka Inno, wandama bai saniba zai ɗauka itace ta haifi Hajiya Iyan ai. Wlhy na tabbata da ace banan ta kawo Inno har ALLAH ya ƙaddara rasuwarta ananba da sai munyi kuka bana wasaba akan wannan rasuwar. Yanda zuminci ya taɓarɓare kowa zagayewa zaiyi yabar Buba da gawar Inno, da kuma sun bizneta su kama gabansu su barmu. Amma yanzu kaga yanda suke tururuwar zuwa nan hardama waɗanda bakai zaton ganiban. Amma kayi haƙuri nayi kuskure, dan babu yanda za’ai Zinneerah ta koma can bada yardarkaba”.

      Numfashi Abba ya sauke yana ɗan jinjina kansa. “Maganarki akan hanya take Hauwa’u, ni kaina naji daɗin wannan karamci da suka nuna akan marigayiyar, dan sun nunama sauran dagi su basu manta alkairin Inno ɗinba garesu har yanzun. Badanma ALLAH bai ƙaddaraba kinjifa maganar kaita india da suka fara. Da ace masu kuɗi haka suke daraja zuminci fiye da dukiyarsu dake tsone idonsu lallai da bamu lalace hakaba. Ace dan ALLAH ya baka wani abin jin daɗin duniya kakoma ƙyamar ɗan uwanka baka ƙaunar ya raɓeka. shiko yana gudun raɓar takane saboda karka wulakantashi. Kaiconmu da fifita abinda zai halakamu sama da abinda zai kaimu aljanna”.

       “Amin ya rabbi Yaya. Al’amuran kam sai dai addu’a. Ni kaina halayyar mutanen nan ta zaburar dani wani muhimmin abu insha ALLAH”.

      “Ai haka akeso dama. idan kaga wani ya aikata alkairi kayi ƙoƙarin koyi da shi, ka kuma nisanta kanka ga mai aikata mummuna. Dan masu iya magana kance zama da maɗaukin kanwa shike kawo farin kai”.

         “Sosai kuwa Yaya, ALLAH kai riƙo da hannayenmu”.

    “Amin. To amma nima kuma sai a duba ni dan har cikin raina inason zaman Zinneerah tare damu kodan kansu ya haɗu da sauran ƴan uwanta. Gashi kuma inajin matuƙar kunyar mutanen nan wlhy, yanzu hakamafa ɗazun sai da Alhaji Kabir ɗin ya kirani da kansa akan suna nan dai suna jira”.

       Cike da mamaki Mama tace, “Wai kirafa Yaya?”.

       “Wlhy kuwa, mutanen nanfa mutanen kirkine masu ban mamaki. Toni banda dalilinki ta inama zan ishesu kallo koda a haɗuwar hanyane. Amma ki duba yanda suke da sauƙin kai. Yanzu da wani zaiji nace Alhaji Kabir Shira na kirana a waya ai cazai na zuga ƙarya ko”.. 

     Dariya ta kufcewa Mmn Sadiq, shima Abban ya shiga tayata. “ALLAH kuwa Hauwa’u koni kallon abun nake tamkar mafarki. Ku riƙe bayin ALLAHn da ƙyau bawai dan arziƙin da ALLAH yay musuba, sai don sanin darajar ɗan adam da zuminci da ALLAH ya azurta zukatansu da shi”.

     “Insha ALLAHU Yaya. ALLAH ya bamu ikon gina zuri’armu bisa ƙyaƙyƙyawar tarbiyya muma. Koda sun zama wanu abu a rayuwa sukasance masu sanin mutunci da darajar ɗan adam”.

      “Amin ya rabbi Hauwa’u. To ammafa zan basu Zinneerah ne kawai banda Abdul-Mutallab. Tunda ba wani shayar dashi takeba tabar mana abummu anan. Itama dai su tausaya mana ta dinga ziyararmu akai-akai. dan ɗazun namasa maganar karatunta dan shine babban burina a gareta. Inason rayuwarta ta inganta sosai kodan kaddarar data ziyarci rayuwarta tun tana ƙanƙanuwarta. To shine yake cewa indai karatune sai Zinneerah tace ya isheta da kanta insha ALLAH”.

       “Yaya ALLAH ya saka da alkairi. Dama nima damuwata akan Abdul ɗinne. To amma kana ganin mu sanar dasu gaskiyar al’amari game da haihuwar tata kenan?”.

      “Eh to, bazance miki a’a ba, bakuma zance e ba. amma inaga muɗan bada lokaci taje gidan muga yanayin zaman nata tukunna, duk da har cikin raina bana tunanin wani abu saɓanin ƙyaƙyƙyawa”.

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button