Uncategorized

HALIN GIRMA 15

       Cike da gamsuwa Mmn Sadiq ta gyaɗa masa kai.

___________________★

        Washe gari Gwaggo Maryama ta shirya taje yoma Hajiya Iya sallama dan zata wuce itama. Shatara ta arziƙi aka haɗota dashi, tare da driver na ɗaukar Zinneerah, dan Hajiya Iya tace ta gaji da gafarasa bataga ƙaho ba. Da tarema zasu zo da kanta ta ɗauka Zinneerah ɗin sai akai rashin sa’a tai baƙi. Hakan yasa ta haɗo Gwaggo Maryama da driver tace kafin itama tazo, dan tayi alƙawarin dukkan zuri’arta sai sun tako har gidajensu suma insha ALLAH.

       Wannan al’amari ya bama su Mmn Sadiq Mamaki da dariya. Babu shiri tai kiran Abba ta sanar masa. Dole ya baro kasuwa yazo sukai magana. Gashi su kofa Zinneerah basu zaunar akan batunba dan sun yanke da saita samu hutun makarantane.

       Ganin kar Hajiya Iya taga kamar suna mata yawo da hankali suka yanke shawarar barin Zinneerah taje kamar da nufin yin kwana biyu haka. Dan karsu mata gatsau takuma shiga wani hali musamman akan Little.

      Ilai kuwa da suka kirata aka sanar mata zataje wajen Hajiya Iya ta zauna da ita na kwana biyu saboda batajin daɗi sai bata wani damuba. Hasalima taɗanji daɗin tafiyar kodan taje ta huta daga izgili da ƴaƴan mmn sakina da ita kanta maman sakinar kemata a kwanakin nan musamman a makaranta. Shiru kawai takeyi dan karta tada hankalin mahaifiyarta. Amma abin na damunta, dan takai yau har ihu Sakina ta saka akai mata a aji ana kiranta agola ƴar cin arziƙi. Damuwarta ɗaya karatunta da kuma Little dake nane da ita a kwanakin nan duk da ya ƙara samun sauƙi bakamar daba.

     Bayan Mama da Abba sun mata nasiha akan ta kula da kanta da kuma girmama kowa yanda zasuyi alfahari da ita ta ɗauka kaya kala uku kawai abinta tai musu salama cikin dabara ta fito saboda little. Su Sadiq kuwa suna makaranta sai dai su dawo suga wayam bata nan.

      Motane lafiyayya kuma ƙosashshiya. Dan ƙamshin dake a cikintama kansa na musamman ne. (Abinda bata saniba wannan mota ta mai gayyace mai aiki ce. dan Alhaji Kabir motarsa ya bada musamman domin ɗakkota. Haka kawai yarinyar ta shiga ransa yakejinta tamkar ƴaƴansa daya haifa. Ga kuma son daya fahimci mahaifiyarsa na mata itama). Tana a baya driver na gaba yana tuƙinsa a nutse, tai tagumi kawai tana kallon waje da zurfafa a tunanin yanda rayuwarta keta walagigi. Anya kuwa ita tanada farin jini ga mutane? Duk inda zata rayu bata taɓa samun salama hundred percent sai da matsaloli. A Danya matsalarta Inna, Yaya Karima, Tinene. Bayan ƙaddara ta haɗata da mahaifiyarta gakuma su Maman Sakina da ƴaƴanta yanzu suna neman hanata shan ruwa a gidan data samu gata da kulawa. Anya kuwa idan ta dawo daga inda zata yanzu bazata shawarci mamansu akan a maidata boarding school ba ko zata samu nutsuwar yin karatunta cikin salama?.

      Wannan tunanin yasata jin nutsuwa a ranta taketa sakin murmushi batare data saniba har suka iso gaban katafaren milk color ɗin gate ɗin gidan. Sai da driver yay horn maigadi ya wangale gate ɗin ta dawo hayyacinta. Nannauyan numfashi ta sauke zuciyarta na wani irin tsargawa tamkar waccan ranar da Abba ya kawosu. Addu’a ta shiga karantowa a ranta har driver ya buɗe mata ta fito. Godiya tai masa cikin risinawa. Hakan ya sakashi jin daɗi har cikin ransa. Ya miƙa hannu zai amshi jakkar hannunta amma sai ta hanashi. “Haba Yayana, jakkarma kai zan ba ka ɗauka min, ai babu dacewa a cikin hakan, kaine zan ganka da kaya na amsa bakai zaka ganni dasu ka amsa ba”.

     Murmushi ya mata cike da jin ta kuma birgeshi. Shine da kansa yay mata rakkiya har sashen Hajiya Iya. Inda a tafiyar tasu take samun damar yima gidan mai sassa da yawa kallon tsaf. A ranta kuwa raya irin jin daɗi ta masu hannu da manda takeyi. Shiyyasa akace wasu tun a duniya suke cinye rabonsu na lahira. Wasu kuma sai kaga ALLAH ya haɗa musu duniyar da lahirar duka. Ya ALLAH kasa muna cikin masu samun dukan gaba ɗaya………….✍  

         

        

     

    *_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_*

Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki????????????????.

*_★ AL-ƘIBLA_*????

_Na Safiyya Huguma_

*_★ MABUƊIN ZUCIYA_*????

_Hafsat Rano_

*_★ DALAAL_*????

_Na Miss xoxo_

*_★ UBAYD MALEEK_*????

_Na Mamu gee_

*_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*????

_Na Bilyn Abdull_

Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za’a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi????????????????????????????????.

Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka????????????????

Ɗaya___300

Biyu____400

Uku_____450

Huɗu____500

Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????????

0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????????

*_08085405215_*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????????

  0903 234 5899

????????????????????????????????????????

TEAM—-ZAFAFA BIYAR????????????????

   

      

[ad_2]

Previous page 1 2 3

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button