Uncategorized

HALIN GIRMA 29

 Halin Girma      29

*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK????????_*

https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK????????_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK????????_*

https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS

*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK????????_*

https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw

******* ★

Tana daf da shigowa ta kira Samha tace ta wuce part dinta dan ba zata iya zuwa wajen Ammi ba, tashi tayi ta fita bayan ta saka wayarta a cikin purse dinta, taja kofar ta nufi wajen Laila din da ya kasance nata ita kadai kusa da na Kilishi. A waje suka hadu ita tana fitowa daga mota ita kuma tazo daidai bangaren, sallamar driver tayi yaran suka dauko mata kaya suka biyo ta, suka hadu suka rankaya ciki tare da Samha. Bayan sun zaune ne Lailan ta tuge mayafin kanta da yake dan yalolo da ta yane kan, ji taka kamar iska bata ratsa kan nata sosai shiyasa duk take jin ranta a jagule babu dadi, ga haushin abinda ya faru ga na karatun ta da take jin kamar ta rasa komai a yanxu.

“Kin ganki kuwa Queen, ya akayi haka?”

“Menene ma ba zaki gani ba, hmm wallahi bansan waye yayi min zagon k’asa ba, amma ko waye toh tabbas baya kaunata ko kad’an!”

” Kin binciki Hadimar nan? Ba kince ita kadai tasan da plan din ba.”

Girgiza kai tayi

” Ba ita bace ba, someone very close to me ne, dan yadda ba kowa ke shiga part din nan ba, toh lallai wanda yake da direct access da part din ne.”

” Lallai, gaskiya ko waye be kyauta mana ba, yanzu ya ake ciki?”

” Wai hakuri? Wallahi ban ba,kinsan yadda nake son Capt tun muna school haka shima kinsan kaunar da yake min ba kad’an bace, ba zan iya rayuwa da kowa ba sai shi, bayan haka kinsan matsala ta da Dr. Bryan Ford.”

” Haka ne, toh shikenan yanzu menene next move dinki?”

” Har yanxu ban dawo daidai ba, I need time to recover nasan me zanyi.”

” Shikenan, duk abinda zakiyi dai kiyi informing dina, zan baki shawara yadda ya kamata.”

” I know I can count on you, Nagode Bestie!”

“DM!”

 Tayi murmushi yana relaxing sosai akan kujerar, tana tunanin yadda zatayi amfani da Laila ta samu cikar burin ta! 

   Sai wajen tara sannan suka tafi, bayan Maman sun gama zantawa da Ammi, babbar aminiyar ta ce sama da kowa a kaf adamawa dan da ita ta fara sabawa lokacin da aure ya kawota, sannan yaransu ma tare suka taso ita tana da yara biyar compared to Ammi da take da guda daya tal…

   Zuciyar ta fari kal sanda suka isa gida, ta san ko babu komai zata dinga samun duk information din da take so ta bakin Laila, tunda tayi masifar yarda da ita fiye da yadda ma ta yarda da uwarta mahaifiya. Bata da kirki ko kad’an idan har ka shiga gonar ta, amma kuma tana masifar ganin mutuncin Samha din, dan itace tafi mata kowa a yanzu, gani take ma babu me kaunar ta sai Samha din kawai. Ko Kilishi ta san ta Kamal kawai take yi ba tata ba, shiyasa itama bata wani sanar da ita idan zatayi abu sai dai daga baya, daga Samha sai amintacciyar hadimar ta guda daya wadda zata iya bada ranta fansa ga Laila din saboda tsabar biyayyar da take mata.

  Wurgi tayi da tarkacen da ta debo daga mota tayi a saman gadon ta, ta kwanta tana kallon sama ba tare da ta cire dogon takalmin kafarta ba, murmushi take ita kadai duk kuwa da abinda Muhammad din yayi ya bakanta mata rai, amma kuma ta raina yarinyar da ya kira ta da matarsa, a shekaru ba wata babba bace haka ma wayewar rayuwar duniya sam bata cikin sahun amma kuma tana da nutsuwa a yanayin ta, da kuma iya handling abu dan yadda tayi da taji da wanda take waya ya matukar bata mamaki, kamar bata fahimci komai ba bayan sarai ta gane, kuma bata ko bi takanta ba ,ko ta tuhume shi ko ta chanja masa fuska sanda ya shigo, sai ma ta tarbi mijinta da fara’ar da ta mantar dashi komai da kowa.

  Tashi tayi tsaye ta soma zagaye a tsakanin dakin tana jin kamar taje ta jawo ta da karfin gaske ta fidda ta daga gidan, duk yadda suka kai da wayewa amma ya tsallake su ya dauko wadda bata kai ko rabin ajin sa ba, adah Laila kawai take jin haushi amma yanzu na Laila ya daina damunta, dan tasan babu wani abu da zatayi sai da sanin ta, yarinya karama ce yanzu take neman zame mata ciwon ido.

   

***Suna shiga part dinsu tun daga kofa ya daga ta sama, ta saki siririn ihu tana kankame shi, da gaske taji tsoro dan bata yi tunani ba, sai ji tayi anyi sama da ita, kin ajiyeta yayi sai da ya kai karshen falon sannan ya zaunar da ita ya bita ya zauna a gefenta yana dariya

“Kin fiyaa tsoro Allah!”

“Ai it was unexpected shiyasa.”

“Ba wani, tsoro dai kawai, ki yarda, you have to be strong, kinsan dai ance a wife of a soldier is a soldier!”

” Wasa suke suma wallahi.” Ta saka dariya

” Haka dai aka ce.” Yayi dariyar shima

“Yawwa… Dazu na gani a WhatsApp wai anyi calling off strike?”

” I can’t say, bari na kira naji, amma zaki koma ne? Ko a samu wata school din daban?”

” Duk yadda akayi yayi.”

” Owk toh bari naji.” Yace yana ciro wayar sa daga aljihu, yayi dialing number wani lecturer abokin sa, suka gaisa sannan ya tambaye shi, baa gama daidaitawa ba amma dai akwai yiwuwar komawar nan kusa. Ajiye wayar yayi ya fad’a mata yadda sukayi 

“Matsalar k’asar nan kenan, yanzu fisabilillahi fiye da 9month ana strike amma gwamnati tayi shiru? Shikenan karatun yara ya lalace akan wani dalili mara tushe, it’s so unfortunate gaskiya.”

“Wallahi har sai mutum ma ya gaji da zaman, babu dadi sam.”

“Dole ai, Allah ya kyauta.”

“Amin.” Tace sai sukaayi shiru, chan kuma yace

“Bari muga idan basu daidaita ba, kawai sai mu chanja ko Base ne, ko kuma wata private uni din na Kano.”

“Owk Allah ya zaba mana mafi alkhairi.”

” Amin Matata!”

*** Tare suka shiga ciki bayan sun kammala duk abinda ya kamata su kammala a falon, zama yayi ya kunna system ya shiga aiki ita kuma ta wuce toilet dan ta watsa ruwa tazo ta kwanta. Sharp sharp tayi wankan ta fito sanye da rigar da ta cire , be kalle ta ba, har ta isa gaban wardrobe ta dauki wata mara nauyi iyakar ta kasan guiwa, dan duk sauran kayan da take dasu anan ba zata iya kwanciya dasu ba, idan ma ta saka tasan shi, zai iya yin karfa karfa ya hanata yayi amfani da damar yayi mata wayo. A gajiye take jin ta yau din ba wai don tayi wani aiki ba, bata san dalili ba gaba daya jikin ta ciwo yake mata, wankan da tayi take saka ran zai dan saka taji dama-dama. 

  Kallon ta yayi bayan ta sako rigar, yayi mata alamar tazo, ta taho ta zauna agefen sa, ya cigaba da aikin da yake na hada kan wasu takardu masu muhimmanci sosai, yana lura da ita yadda jikinta yayi sanyi sosai, jawo ta yayi bayan ya dan matsar da system din, ya kwantar da kanta a jikin shi

“Goodnight sweet dreams.” Ya rankwafo yayi mata peck a kunci, lumshe idon ta tayi bacci na cin karfin ta sosai. Be san iya adadin awoyin da ya dauka a wajen ba, ya dade sosai har sai da ya fara jin bishi-bishi, sannan ya rufe system din, ya gyarata a hankali sannan ya tashi yana mika, alwala yayi yazo yayi sallah raka’ah biyu, ya lura da ko shafa’i da wutri da ta saba yau bata yi ba, be san wanne irin bacci take ji haka ba, dan har ya gama aikin sa ya tashi ko motsawa batayi ba. Taimaka mata yayi zuwa gadon ya kwantar da ita ya lullube mata iya kafarta, sannan ya kwanta bayan ya rage kayan jikin sa ya rage daga shi sai boxer kawai.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button