Uncategorized

HALIN GIRMA 29

  Cikin dare sosai taji ishirwa, irin wadda bata taba jin irin ta ba, tashi tayi ta lallaba ta fito bayan ta duba fridge din dakin ta tuna babu ruwa a ciki, ta manta kuma bata kawo ba dan bata bar kowa cikin masu aikin sun taba shigar mata dakin ba, iyakar su falo shima dan babu yadda zatayi ne amma ko yaushe suna BQ sai wani abu me muhimmanci sannan take kiran su.

   A kitchen ta samu ruwan, tasha sannan ta dauko karamin katan na ruwan ta taho dashi. Falon yayi dim amma kuma akwai dan haske kadan da ya hasko ta corridor din kitchen da yake a kunne, kafarta take sawa a hankali tana tafiyar har ta kai tsakiyar falon, da yake falo ne katon gaske da sai kayi tafiya tsakanin kitchen da corridor din bedrooms din, motsi taji kad’an kad’an, tana matsowa yana karuwa har ta kusa kai wa corridor din abinda ta gani a wajen ya sakata daskarewa a wajen. Chak ta tsaya ta kwalla wata irin kara da ta tashi Moh daga bacci, ya mike a firgice yana kiran sunan ta, sai kuma yayi hanyar fita daga dakin da sassarfa kirjin sa na bugawa da karfi! 

BIYAN BASHI ⛹️⛹️⛹️⛹️⛹️⛹️⛹️⛹️

[ad_2]

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button