HALIN GIRMA COMPLETE HAUSA NOVEL

HALIN GIRMA 36-40

“Nooo Dr… No be mutu ba, Dan Allah karka ce min ya mutu
dagaske, ban kyauta masa ba, be kamata ya mutu ba, he’s innocent be kamata yayi
facing irin wannan mutuwar ba, me yayi? Menene nasa a ciki?”

 

“Get hold of yourself Capt, kullu nafsin za’ikatul ma’ut,
hakikaa kowacce rai sai ta dandani zafin mutuwa, shi da ya tafi be yi sauri ba,
mu kuma bamuyi jinkiri ba, addu’a kawai yake bukata.”

 

Dr yace ya juya ya barsu a wajen, babu wanda ya iya motsi a
wajen saboda tsabar kaduwa, yaro me zumunci me shiga rai, me son yan uwan sa,
ya Yaya zataji? Labarin mutuwa irin wannan mara dadi, kullum korafin ta akan
Nigeria shine rashin tsaro, ko waya sukayi ta kan ce musu Nigeria ta zama
abinda ta zama, rai ba abakin komai yake ba. Kullum maganar ta kenan, tsoron ta
kenan, ashe bata tsira ba, Ashe zaman ta a chan bashi ne zai sauya kaddara ba?
Innalillah wa inna ilaihi rajiun kowa yake maimaitawa babu hargitsi ko hargowa,
saboda dauriya irin ta maza, sai dai kana kallon su zaka san mutuwar ta dake
su, musamman Habib da Moh, kafin kace kwabo labarin ya zagaye ko ina, kowa sai
da ya tausaya wa Mahfuz irin kaddarar da ta fad’a masa.

   Zuwan Aji da Bubu ne ya dawo da Moh cikin
hayyacin sa, babu hawaye ko digo a fuskar sa amma ya daku, ya kadu da zaka iya
rantsewa ya dade a kwance yana jinya me tsanani.

   Baya magana bayan amsa gaisuwa sai dai kawai ya
amsa maka da ka, har zuwa lokaci itama bata farka ba, yaje yaga Musaddik wanda
yake da sauki sai ciwuka a jikin sa yawanci na duka ne. Sai kuma yunwa da ta
ramar dashi sosai, driver da Ummimi babu abinda ya same su dama su ba sune
targets din ba.

   Wajen azahar ya dawo dakin da take, har lokacin
bata tashi ba, mummy ce kawai a dakin tana zaune gaban gadon da Iman din take,
idon ta yayi ja sosai, addu’a take tofa mata ya shigo ta tashi a kunyace tana
kokarin barin dakin

 

“Dan Allah mummy ki yi zaman ki, dama nazo na duba ko ta
farka ne, zanje station din na dawo.”

 

Komawa tayi ta zauna shi kuma ya fita, ya shiga mota ya nufi
station din. Direct office din CP ya wuce ya samu DSP yana press conference
akan case din, kokarin fita yayi amma babu dama sun riga sun ganshi, sukayi
masa cha kuwa kowa na son masa tambayoyi, be basu dama ba dan yanzu ba wannan
ne a gaban sa ba, da kansa zai shirya ya basu lokaci amma ba yanxu da be ma san
me yake masa dadi ba sam. Hakuri aka basu, aka kuma sallame su sannan ya samu
ganin CP din sukayi magana, ya kuma shiga wajen da aka ajiye Jabir din. Yayi
matukar laushi sosai saboda ba karamin duka sojajin nan sukayi masa ba, dama
yasan ba zasu kyale shi ba, hakan ba dan dai basaso a samu matsala ne amma tsaf
zasu iya kashe shi a wajen.

    Baya jin a yanzu akwai wata halitta da ya tsana
sama da Jabir din, shiyasa ya tsaya daga kofar be shiga ba, dan idan ya shiga
zai iya shake shi har sai ya daina numfashi. Wani dan sanda ne a gaban sa rik’e
da wani katon katako, yana masa tambayoyi, sai kuma wasu yan sandan suma daban
daga gefe cikin fushi suke interrogating dinsa yana rokon suyi hakuri. Juyawa
yayi ya bar wajen ya koma suka karasa magana da CP sannan ya bar station din ya
dawo asinine, in da ya wuce kai tsaye wajen Musaddik, ya samu dakin da yan
sanda suna daukar bayanai daga wajen sa, wucewa yayi ya koma bangaren Mahfuz da
har yanzu ba’a saki gawar sa ba, sai an gama bincike tsaf sannan za’a basu suyi
masa sutura. A chan ya zauna tare da su Habib dasu Abba har bayan Magriba
sannan aka basu gawar tasa, suka dauke ta suka nufi gida da ita don yi masa
sutura a mika shi gidan sa na gaskiya.

   Zuwan su ya saka gidan rikicewa, dama kowa ya iso
ana zaman jira cike da alhini, ba karamin taba kowa mutuwar tayi ba, nauyi da
kunya ya Moh shiga ciki, sai yake ganin kamar shi ya jawo, da be saka shi a
cikin maganar ba, da duk hakan bata faru ba, a daren aka hada shi, aka kuma
rakashi gidan sa na gaskiya. Allah sarki.

 

Mutuwa darasi ce babba, Rayuwa bata da tabbas, Allah ya bamu
ikon amfani da lokacin mu kafin ya kure mana,Allah kasa mu cika da imani. Amin
😭

  

 

 

***Wani irin juyawa cikin Samha yayi lokacin ta samu labarin an
kama Jabir, tsoron ta daya kar sunan ta ya shigo ciki, itace ta bawa Jay din
shawarar kidnapping Iman din, kuma ita kadai ce tasan plan dinsa duk da itama
bata san amfani yayi da ita ba. Wayar ta ce tayi kara da take gefen ta,dan
tsorata tayi, sai kuma ta kai hannu ta dauka tana kallon number, Kamal ne yake
kiranta, dagawa tayi ta saka wayar a handsfree

 

“Ashe dama abinda zaku aikata kenan ke da dan iskan chan
shine kuka shigo dani ciki kuka samu duk wani bayani akan shi, daga karshe kuka
watsar dani.”

 

“Ai kai ba karamin kidahumi bane, idan banda gara irin ka,
waye yake da amana a wannan zamanin, kowa kansa ya sani bari kaji, dan haka
karka dameni ka kyale ni naji da abinda yake damuna.”

 

“Ai wallahi kadan kika gani, asirin ki ya gama tonuwa dan
na gama zayyane komai a gaban yan sanda, abubuwan da kuka sakani nayi duk na
fad’a sai ki jira hukunci, wallahi ko shi MOH ya kyale ki wallahi ni ba zan
kyaleli ba kinji na rantse!”

 

Kit ta kashe wayar ta jefar da ita,

 

“Wannan wacce irin masifa ce?”

 

Da sauri ta ja jakarta ta fito, bata tarar da maman ta a falo ba
dan haka tayi saurin ficewa ta dauki mota ta bar gidan, tana tafe tana gwada
kiran Laila amma bata dagawa, ta rasa abinda yake mata dadi, sai kawai ta wuce
gidan ta sameta suyi magana ko zata taimaka mata, amma tana zuwa gate sai aka
hanata shiga, tayi mamaki sosai hadda fitowa tayi musu bayanin kanta, amma
kemaimai suka hanata bayan sun tabbatar mata da sun gane ta, umarni ne aka basu
kar su sake barin ta, ta shiga masarautar.

[ad_2]

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button