HALIN GIRMA COMPLETE HAUSA NOVEL

HALIN GIRMA 36-40

“Tunda har ban isa na saka ko na hana Zeenatu abu a gidan
nan ba, kin nuna min ban isa ba tun fil’azal, na bar miki ita, idan har tana so
mu shirya da ita lallai ta koma dakin ta, ke kuma, hakuri na ya gaza, kije gida
kya dawo duk sanda kika shirya gyara auren yarki, idan har Zeenatu bata koma
dakin mijinta ba, toh zaman mu ba zai cigaba ba. “

 

Daga haka ya saka kai ya fice, ba don darajar yaran dake
tsakanin su ba, ba kuma don darajar zaman da tayi dashi na dadi a baya ba, da
zai sauwake mata ne kawai, amma hakan ba zai yiwu ba, har yanzu yana sonta yana
kuma son ta gyara halayenta.

   Tashin hankali ba’a saka maka rana, da girman ta
da komai gotai gotai zai ce taje gida, zagaye ta dinga yi a falon kaamar tayi
hauka, duk tsawon shekarun da sukayi da Ibrahim be taba nuna mata ko yatsa ba,
sai gashi a yanzu da girma ya soma hawa kansu, tayi abinda gaba daya mutuncin
ta ya zube a idon sa, har yana cewa zaman su ba zai yiwu ba.

 

” Mama dan Allah kiyi hakuri, zan koma wallahi ba zanzo ku
samu matsala da Abba akai na ba, zan jure koma menene dama ni na jawo ma kaina.

 

” Ba laifin ki bane, babu abinda zai faru , sake gwada
kiran Bashir din idan be daga ba sai kawai na saka Habib ya kaiki chan gidan
su, daga nan sa neme shi ai dole yazo ya dauke ki.”

 

Da sauri ta dauko wayar, ta kira amma sai taji alamar anyi
blocking number, ajiyewa tayi jiki a sanyaye tana fadawa Maman, kira mata Habib
tayi, tace yazo maza gida yanzu duk abinda yake yi, be dau wani lokaci ba sai
gashi, ta fad’a masa abinda take so yayi,yace mata babu mota Abba ya fita,
sakashi tayi yaje ya kira musu napep yazo suka tafi, suka fita ta ja ajiyar
zuciya, ba zata iya jure tafiyar ko ina ba, ta riga tayi girman da zaman gidan
su zai mata wahala sosai, idan kuma ta tafi bata san ta yadda zata dinga ji
daga wajen Zeenat din ba.

 

***Yana zaune bayan sun gama wani taro da sukayi, ba zaka iya
tantance yanayin da yake ciki na bakin ciki bane ko na farin ciki, kiran layin
Musaddik yake amma still amsar daya ce, switch off, sunyi dashi kafin su taso
zai kirashi, gashi babu wani isashen lokaci da zasu sake batawa, su biyu ne
suka shigo, suka sara masa sannan suka koma gefe suka tsaya

 

“It’s time sir.”

 

Mikewa yayi be ce komai ba, ya shige cikin dakin, ya dauki
jacket dinsa da dayar wayarshi, sauran kayan nasa sun riga sun fitar dasu tun
dazu,gaba yayi suka bishi a baya, yana cigaba da kiran Musaddik din, ganin da
gaske ba zai same shi ba, shiyasa ya sauya akalar kiran zuwa kiran ta. Jiya
basuyi magana ba gaba daya, yasan tana kaiwa yamma a school haka kuma yasan ta
dawo a gajiya, ko da ya kirata no answer sai kawai ya kyale ta, a zuwan suyi
magana a yau kafin ya taho. Ringing wayar tayi tayi ba’a daga ba, bayan ta
katse ya sake kira amma still no answer, sai ya kashe wayar tasa baki daya ya
tura ta cikin aljihun wandon sa, sanda suka karaso wajen motocin da zasu dauke
su, tuni duk sun shiga shi kadai ake jira, dama kuma shine Captain din tafiyar.
Yana shigowa duk suka mike tsaya, irin doguwar babbar motar nan ce, sai da ya
zauna sannan duk suka zauna, driver ya jasu suka bar harabar wajen.

   Tun daren jiya labari ya kai fadar Maimartaba na
rashin dawowar Iman din daga makaranta wanda ma’aikatan gidan ne suka kai
labarin, kamar wasa da kowa ya dauka, a tunanin su ko wani wajen ta biya, amma
ganin har dare ya soma yi ya saka hankali ya fara tashi, zama ma neman gagarar
Fulani tayi bayan an tabbatar da bata je gidan su ba, ba kuma wani da zata je
wajen sa, number driver da tata duk suna shiga amma kuma babu answer. Waya
Maimartaba yayi a dare ya sanar da yan sanda abinda yake faruwa, a take ya
tashi jami’an tsaron ko ta kwana, suka bazama neman, in da aka samu wayar Iman
din da ta driver a cikin makarantar in da aka ajiye a waje daya cikin wata
farar leda.

   Tsawon daren babu wanda ya runtsa a tsakanin su,
in da suka gama tabbatar da sace su akayi, kuka sosai Fulani take tana hango
kalar tashin hankalin da muhammad zai shiga idan ya dawo. Zuwa safiya labari ya
fara fita, bayan Maimartaba sunyi waya da gwamna, da wasu manyan jami’an tsaro,
cikin kankanin lokaci labari ya baza lungu da sako na k’asar har ma da kasashen
dake da makfwataka da k’asar.

  Ana zargin an sace matar dan sarkin Adamawa, jikan
sarkin Kano babban jami’in sojoji Captain Muhammad Ahmad Santuraki haka gidajen
jaridu suka dinga wallafawa a shafukansu, nan da nan mutane suka dauka kowa na
kokarin tofa albarkacin bakin sa.

 

_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

 

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO) s_*

_SO DA ZUCIYA_

 

*_SAFIYYA HUGUMA_*

_DABI’AR ZUCIYA_

 

*_MAMUH GEE_*

_DEEN MARSHALL_

 

*_HAFSAT RANO_*

_HALIN GIRMA_

 

*_BILLYN ABDULL_*

_TAKUN SAKA_

 

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇

D’aya 300

Biyu 400

Uku 500

Hudu 700

Biyar 1k

 

*_Zaku tura kudin a_*

 

6019473875

*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*

*keystone bank*

 

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

 

08184017082

 

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

 

09134848107

2/17/22, 09:45 – Buhainat: Halin Girma

37

 

*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾_*

https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

 

*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

 

*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇🏾_*

https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS

 

*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇🏾_*

https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw

 

*******�

Cikin matukar tashin hankali Abba ya shigo gidan, bayan abinda
ya gani a shafin BBC HAUSA, ya saka shi matukat kaduwa, idan har suna nufin
surukin sa kenan, toh kenan Iman aka sace? Innalillah wa inna ilaihi
rajiun,tashin hankalin da ba’a saka maka rana. Sauri sauri yake yana kokarin
isa bangaren Abba babba, kiran Mummy ya shigo wayar sa,

 

“Shikenan.” Ya furta

 

“Sun samu labari kenan, ta tabbata da gaske ne.”

 

Ya sake fad’a sai kuma ya daga wayar yana kokarin daidaita
tashin hankalin da yake ciki.

 

“Hello Abban Iman, abinda nake gani a news gaskiya
ne?”

 

“Labarin da nake samu yanzu kenan, yanzu muke shirin tafiya
dan samun sahihancin labarin, ki kwantar da hankalin ki, in sha Allah babu wani
abu da zai faru.”

 

“Innalillah wa inna ilaihi rajiun.” Ta furta tana
sakin kuka

 

“Zan tawo yanxu..”

 

“Sai kin zo.” Ya katse kiran da sauri yana shiga ciki,
a tsaye ya tarar da Abban yana kaiwa da komowa, yana shiga Abba Musa da Abba
Kabiru suka shigo, babu wata magana da suka tsaya yi suka fice da sauri, suka
dauki hanyar gidan sarki, dan anan ne kawai zasu samu gaskiyar abinda suke so
suji, da Abba Musa yace su kira Muhammad din amma kuma sai suka fasa suka ga
gwara su je din kawai ba lallai shima ya iya daukar waya ba.

  Haka sukayi, cikin tsananin tashin hankali suka isa gidan,
bayan sun gabatar da kansu aka shigar dasu har in da maimartaba yake, babu wasu
mutane sai makusantan sa, suna jimamin abinda ya same su haka bakatatan, sannan
lokaci zuwa lokaci suna communicating da chan police station din, duk da babu
wani labari akai, dan duk wanda yayi aikin yayi masifar kwarewa wajen gudanar
da plan din nasa dan be bar duk wata hanya da za’a neme shi ba, amma duk da
haka ba zasu karaya ba, zasu yi iyakar kokarin su dan ganin an samu so cikin
kankanin lokaci.

   Labarin da su Abba suka samu yayi masifar sake
daga musu hankali dan har kwalla sai da Abba yayi ba tare da kowa ya lura,
yadda ake bada labarin rashin imanin masu kidnapping din nan kawai yake tunawa,
ga iman sam bata da hayaniya, zata cutu ainun a wajen su sai dai fatan Allah ya
bayyana ta cikin aminci da koshin lafiya.

  Suna zaune jugum kowa yana tunanin yadda Moh zai idan ya
dawo, ya ci karo da wannan mugun labarin duk uban tsaron da yake ganin ya zuba
a gidan sa, lallai addu’a ce kawai mafita a wannan zamanin, dan a duk in da
mutum yake ba wai ya tsira daga sharrin su bane.

   Haka kawai yaji kamar bashi da lafiya, duk daukin
da yake na zuwa gida ya ganta bayan tsawon lokacin sai yaji kamar duk guzarin
sa na barin sa. Tun a airport din yaga kamar ma’aikatan na kallon sa, kallon da
ya kasa gane na menene, sai kawai ya kyale hakan a wani dalili nasu da suka
sani. Daga nesa ya hango motocin sa, suna jiran isowar sa, dora jacket dinsa
yayi a saman kafadar sa ya shiga takawa zuwa wajen su dan basu ganshi ba. Sai da
ya kusa daf dasu sannan suka ankara, duk suka taho da sauri kowa na kokarin
riga dan uwansa isa, kayan hannun sa suka karba, aka bud’e masa motar ya shiga
ya zauna.

 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button