HEEDAYAH 17

“Ehh ka kalleni da kyau, cewa nayi in dai ni Maryam ina gidan nan wllh wllh Shuraim baxai koya ma wata shegiyar makauniya karatu ba, uwar me ya hada da ita xaka ce ya koya mata karatu???” Calmly Abba yace “Maryam ki tafi gidanku sai na neme ki, bana son in dawo in tarar da ke gidan nan don wllh in har na dawo na same ki a cikin gidana to na sake ki….” Yana fadin haka ya nufi kofa walking just as the barrister he is, Mumy ta bude baki ta bi sa da kallo a sanyaye ta kasa cewa komai….
Kuka bbu irin wanda Mumy bata yi ba a dakinta, ta kira duk kawayenta ta sanar masu abinda ake ciki, Hajiya Sadiya ce ta samu karshe a waya, Hajiya Sadiya ta dinga salati tana cewa “Ki tafi gida kuma?? Anya kan barrister daya kuwa, yaushe kika dawo daga gidan xai ce ki koma? Ehh lallai bbu lafiya, ba dai kin tsaya fi’ili wai ke baxa ki je a nema maki taimako ba, ke da kika fi kowa imani, to wllh taki ta sameki,
shegiya nake idan haka yar bokon nan ta shigo maki gida, wllh da shirinta ta shigo, lafiyayyen shiri kuwa, mance komai xaki yi Maryam mu tafi mu san nayi kafin lkci ya kure maki, ba fa karamin case bane wnn wllh, tunda kike da barrister ya ta6a cewa ki tafi gidanku, ki xauna fa kiyi naxari, to wllh ana dab da kwace maki gida da mijin ki, wnn makauniya dai ta jaza maki abubuwa iri iri a rayuwa, duk ita ce silar faruwar komai”
kuka kawai Mumy take kamar ranta xai fita tana cewa “Wlh Sadiya na canxa xuciyata xan iya kashe yarinyar nan idan hakan kadai ne mafita gareni, ta tarwatsa min farin ciki, ta tarwatsa min gida, a kanta barrister yake min duk abubuwan nan, ga kishiya ta sa an rangada min….”
Sadiya tace “Bbu wani lkcn kuka da kumfar baki Maryam, ki dau duk abubuwan da kike bukata ki baro gidan nan kafin ya dawo saki ya tabbata a kanki, ki taho nan gidana mu san abun yi cikin gaggawa, maxa ki fita daga gidan, Kuma a gaban yar bokon yace ki tafi gida?” Mumy ta kara rushewa da kuka tace “Wa ya sani ma ko tana labe duk tana ji, ni dai ga ni nan xuwa ynxu” daga haka ta katse wayar ta shiga hada yan kayanta da sauri kar barrister ya dawo, cikin mintunan da basu wuce goma ba ta bar gidan xuwa gidan Sadiya.
Mami na xaune parlonta misalin karfe biyar na yamma da frnds dinta uku da suka kawo mata ziyara, ko marmarin xaman main parlor din gidan bata ta6a yi ba tun xuwanta, hatta bakinta bata bari su xauna main parlor, nata parlon take kawo su, bata ma san Mumy bata gidan ba tun safe, aka kwankwasa kofar parlonta, mikewa tayi ta isa bakin kofar ta bude, Shuraim ne tsaye sanye da kananun kaya, yyi kasa da kai yace “Ina yini?” Tamkar ana tilasta sa ya gaisheta can ciki ciki, Tace “Ya aka yi?” Bbu walwala yace “Abba yace xa mu je can gidan kaka da ita” Mami tace “Ita wa?” Yace “Yarinyar” Mami tace “Yarinyar bata da suna?” Shiru yyi mata, can yace “The blind girl” Mami tace “Toh ka kirasa ka tambayesa sunanta, kada ka sake xuwa min bakin kofa kana neman blind girl I don’t have any” tana fadin haka ta rufe kofarta almost on his face.
Da ba don ya san Abbansa is jet angry at him ba kuma kar ya sake wani laifin da wucewarsa kawai xai yi ba tare da Heedayah ba, gaba daya ya rasa yanda xai yi, bayan kusan minti biyar ya sake kwankwasa kofar, ba Mami bace ta bude kofar wnn karon, Barrister Zuwaira ce ta bude, yace “Ina yini?” Tace “Lafiya lau….
A carbon copy of ur father facially but not physically, ba haka Barrister Ahmad yake ba gaskiya, be human plss, let me get u the little girl” daga haka ta juya ta koma ciki ya bi ta da wani irin kallo, sai ga ta ta dawo da Heedayah da Mami ta sama Hijab har kasa duk da kananun kaya ne sosai jikinta tunda gidan Kaka xa a je, Barrister Zuwaira ta mika masa hannun Heedayah da ta bata fuska, ya kama hannun nata, ta rikesa gam ya juya ya bar wajen, bin sa kawai Heedayah ke yi kmr xata yi kuka har suka fito balcony, a dai dai nan ya kwace hannunsa daga nata ya sauka balcony din fuskarsa daure, a hankali take tahowa bayan ya saketa, shi ko har ya fara tafiya ya tuna few stairs dake wajen ya juya da sauri….
Bai yrda ta kai kasa ba ya dauketa irin rikon newborn with both hands, ba karamin tsorata tayi ba jin ta tafi xata fadi sae kuma taji an dauketa bata fadi ba ta ta6a kirjinsa kamar xata yi kuka tace “Ni dai baxan je ba kuma….”