UBAYD MALEEK 1-END

UBAYD MALEEK Page 51 to 60

Tana aje wayar ta waiwaya ta kalli NURU har lokacin baccinta takeyi hankalinta kwance Kamar wata ‘yar baby.Kyakkyawar fuskarta ta kalla zuwa jikinta ta sauke ajiyar zuciya me qarfi sbd tausayin NURUn da Kamar rayuwarta ta raunane auren sa’ar mahaifinta bayan tanada Wanda takeso daidai ita sabon jini Amma yanzu gashi auren dattijo yahau kanta duk da MALEEK yawuce duk wani tsarin Imran nesa ba kusaba Dan kuwa Kota Ina Babu inda Imran yakamo maleek bayan qananun shekaru dazai nuna Masa Wanda shikansa maleek din kyau da hutu tareda wani irin iko da sarauta dake yawo a jininsa suna boye manyancinsa matuqa sosai dan kuwa jikinsa kawai masu qananun shekarunma bazasu kaisa kyawun jikiba musamman dayake Yana geamin sosai haryanzu shiyasa jikinsa koyaushe Kamar na yara.

Ajiyar zuciya tasake saukewa tareda cire wannan tunanin aranta Dan kuwa ita yanzu tariga ta cire kanta acikin maganar komaima Dan kuwa ko lokacinda take muradin raba auren nasu bataga ta inda zata faraba dama fatanta idan mum tadawo dad zai sawwaqewa NURUn sbd wadda zuciyarsa keso tadawo to Amma ita ta ina take gano yiyuwar saki arayuwar dad dinsu Wanda ko rabuwarsa da mum haryanxu duniya Bata gama saniba bare yayi wani sakin.

Aje laptop dinta tayi gefe tareda Miqewa ta Sanya slippers ta fita zuwa kitchen Dan yin wani aikin duk da Bata iyaba Dan debewa Kai kewa batason tunanin komai yadawo Mata musamman na mum dinsu datake fatar shafewa ta manta gabaki daya.

Sai gab da magriba NURU ta farka daga baccin miqe tashiga toilet tayi fitsari da brush ta fito ganin bakowa a dakin tasan wani Abu sukeyi ta zame gajeran wandonta ta dauko wani dogo da zo har qasan gwiwanta ta fito riqeda wayarta tana duba wani email da aka turo Mata daga karatun court din dataje jiya tana dariyar mark din data samu ta nufo kicin dan tunda tafito yanayin qamshin datakeji tasan afiace a kitchen din.

Ganin uban aikin da afia din keyi tareda farhat da mum Sarah sai Fana dake tayawa yasata sakin dariya cikeda mamaki ta miqawa farhat wayarta tana cewa”

OMG meyake faruwa anan ne?

Cikin kanne dariya mum Sarah tace”

Princess na aikin abincin dinner ne.

Wani wargazajjen flat bread ta cire daga pan duk ya sauya kala sbd Kwan jikinsa duk ya kone afia tayi tana aje spoon din hannunta tace”

Alhmdlh na Gama waye zaiyi Mana testing?

Shiru kowa yayi NURU ta matsa tana sake kallon girke girken da mamaki da dariya akan fuskanta tace”

Nidai bana cikin ‘yar dandanawa.

Farhat kuwa da sauri tayi bayan NURU tana cewa”

Nima bana ciki.

Kallon mum Sarah afia tayi da alamar ke fa??

Wani yawu mum Sarah ta hadiye tareda kallon Fana tace”

Saidai Fana kinsan Ni inada suga ba komai nakeciba musamman yau ya haye da yawa sugan.

Tana gama fadar hakan ta sulale ta fice daga kicin din.

Fana Kam ba damar wani zance ta matso ta diba komai daya bayan daya tana dandanawa harta Gama ta dago idonta na kallon qasa tace”

Komai yayi daidai ranki ya dade.

Da mamaki NURU ta kalli Fana daketa faman danne yunqurun amai dake taso Mata na abincin Amma ahaka sbd gudun batawa afia tace komai yayi.

Afia da kanta tajera komai a dining ta wuce tabarsu NURU ta kamawa Fana suka gyare kitchen din tsaf komai yakoma kaman ba’ayi aiki dashiba Fana ta wuce sashensu na ma’aikata NURU ta rufe koina na cikin ta fito ta nufi dakinsu tayi alwala tayi sallar magriba lokacin afia hartayi wanka ta shirya ta fito taje Tasha black tea kawai Takoma daki sbd karatu takeson yi.

Har akai ishai suna Palo suna kallon wani adventure film a Netflix daganan ta hadowa farhat _Rice Krispies_ har suka Gama suka koma daki sukai sallah sukai Shirin kwanciya Bata Bari dakin farhat ba Saida taga tayi bacci tukuna tabaro tadawo dakinsu har lokacin afia n karatu tazo ta zauna kusada ita itama tana duba wasu hardcover books na lauyoyi na _Michael Connelly THE BRASS VERDICT_ 

Karkata tunaninta yayi akan abincin da afia din ta dafa dake kan dining Wanda maleek zai iyaci yasa ta aje littafin hannunta tareda kallon afia da bacci bacci yafara fizgarta ta miqe ta fita Dan dauke abincin daga kan dining duk da tasan kilama ya shige zuwa yanzu.

Direct dining ta nufa ta kwashe kayan ta maida kitchen tana qoqarin barin kitchen din taji motsin bude kofar kicin din ta baya tayi saurin waiwayowa cikin sauri da Yar fargaba tace’

Waye??

Muryan mum Sarah taji daga bayanta ta kofar nata dakin tana cewa’

Fana ce zata shigo ta hadawa MALEEK tea yakira Yana buqatarsa yanzune kafin ya sauko.

Jin haka tasake ajiyar zuciya ta matsa jikin kofar tace”

Fana ki koma kawai zanyi masa.

Juyawa Fana tayi ta wuce itakuma ta juyo ta kalli mum Sarah tana cewa”

Tea kawai Koda wani Abu?

Tea kawai yace amma bansaniba ko Zaki hada Masa da wani abun. 

Fara hada Masa tayi tareda dauko cake dinda tayi jiya ta jera masasu a plate ta dauko ganyen lemon daga fridge ta wanke tareda zuma ta hada tea din ta zube ta jero a tray ta fito mum Sarah na biyeda ita daukeda sauran kayan suna shiga dining room Yana shigowa itace agaba ta ‘dan dago kadan cikin taushin murya tace”

Barka da fitowa.

Akaro na farko ya amsa gaisuwarta da “yawwa” Yana zaunawa kan dining ta ajiye tray din hannunta ta matso kusadashi Dan zuba Masa qamshin turarenta na _Black Opium_ ya bugo Masa cikin hanci ya dago ahankali ya kalleta 

Jin idanuwansa akanta yasa ta dakatawa tana Dan juyowa suka hada ido ta sauke nata tana juyowa da sauri ta kalli mum Sarah dake gurin tun kan ta Gama juyowa mum Sarah tayi saurin aje tray din tabar gurin tana soke kai ganin abinda yake neman fun karfin mamakinta.

Mum Sarah na wucewa ta juyo tana qarasa zuba Masa tareda jawo Masa cake din ta koma kitchen ta dauko ruwa ko zaisha ta ajiye tareda budewa ta zuba a cup.

Kasa wucewa tayi saida taga yagama tana daga kicin tana hangensa ya miqe ya wuce ta fito ta kwashe kayan ta maida ta nufi daki tana miqa sbd bacci takeji yanzu Kam.

Saidata shige ya kashe wutar palon farko yashigo ciki ya wuce sama.

Washe gari suna Shirin zuwa makaranta afia ta dauko zancen padima tafadawa NURUn tana qara cewa”

Inaga zaifi idan tazo Nan taga likita gaskia sbd Sam yanda nayi Mata tambayoyi da amsoshinta akwai rikitarwa bangane komaiba gskia sosai so inaga tazo taga likita zaifi.

Kallon bansan ta yayaba NURU tayiwa afia jikinta a sake tace”

Bansan ta inda zanfara bane,

Bansan ta gurinwa zan fara ba.

Kiyiwa jekadi bayanin komai da abinda kikeso ita zata isar Miki da saqonki koina dakomai saidai kawai kiga padima ankawota.

Shiru tayi hakanan tanajin wani iri kamar zata wuce guri idan tayi hakan Amma Kuma ceton ‘yar uwartane zatayi tunda tanada damar yin hakan zatayi Inshallah.

Juyowa tayi ta kalli afia tace”

Thank you,zan yiwa jekadi magana idan na Isa makaranta inshallah.

Suna Isa makaranta takira jekadi saidata jira jekadi tagama gaisuwarta ta amsa cikin bawa jekadi nata girman itama kafin ta fadawa jekadi buqatarta tason akawo Mata ‘yar uwarta padima tazo Mata ganin gida.

Ba musu jekadi tace”

Angama Inshallah MUSHRA,zanje yanzu na sanarwa Anneti ta sanarwa da MALEEK sai a aika gida ataho da ita Nan daganan sai akawo Miki ita har inda kikeso.

Koda jekadi ta isarda saqon NURU ga Anneti Bata musaba tace jekadi ta isarwa da MALEEK sakon aikuwa Kai tsaye shima ta isarda sakon a waya ta hanyar Mr Omar Wanda yace anbasu dama take washe gari aka aika aka taho da padima wadda Ta taho badan iyayensu sunso ba sai Dan saqon ta hanyar kaleeb ya iso musu.

1 2 3 4 5 6 7 8 9Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button