INTEESAR 4

Inteesar tayi shiru a dan tsorace bayan ta
hadiye maganin tana jiran jin me xata fara ji
a jikinta, har na kusan minti goma bata ji
komai ba hkn yasa ta mayar da hankalinta
ga TV dake ta aiki shi kadae tana kallo, taji
ta fara jin bacci amma har lkcn bata ji ko da
ciwon kai a jikinta ba, hkn yyi mugun daga
mata hankali, tace na shiga uku kar dae
cikin baxae xube ba, ta dauko magungunan
ta shiga balla su kuma xata sha yanda ta sha
daxu hankalinta a tashe, ta ciro su knn ta
jawo kofin ruwanta xata sake korawa taji
wani matsanancin ciwo a mararta da bata
taba ji ba, tayo waje da ido a tsorace
gabanta na faduwa, a hankali cikinta ma ya
fara ciwo ya hade da na maran, tunda take
bata taba jin irin wnn ciwon a jikinta ba,
kankame cikinta tayi ta shiga mutsu mutsu
daga xaunen da take tana buga tiles da
hannunta, taga xama ya gagareta ta kwanta
kasa tana rike da cikin tana juye juye, ita nn
tana ga xata iya jure ciwon har ya gama
cikin ya fita, da marar ta yyi wani irin murda
mata ta daura hannu a ka taji kmr
mutuwarta ce ta xo, bata san lkcn da ta fasa
wani axababben ihu ba tana rike da cikin,
lkci daya ta hada xufa, ta shiga kwala ihun
axaban da take ji a gigice, a tare Aliyu suka
fito da Safeena ya karasa kusa da kofar a
rude ya murda yaji a rufe, bubbuga kofar ya
shiga yi yana kiranta, ta fashe da wani
matsanancin kuka da kyar tace “wayyo
mutuwa xanyi ya Aliyu,” ya koma daki a
rikice ya shiga neman spare key, safeena
kam da gudu ta koma dakinta ta dinga
tsallen murna shknn ta sha ruwan, ya
karaso jikin kofar jikinsa na rawa ya bude
kofar ya afko cikin dakin yana kalle kallen
inda xae ganta, can kusa da gado ya ganta
kwance tana juye juye ya karasa gabanta da
sauri ya durkushe ya dago ta a rude yana
tambayarta me ya faru, kasa cewa komae
tayi sae juye juyen da kawae take a
hannunsa, a rikice ya shiga cewa “don Allah
kiyi min magana fateema me ya same ki,”
duk da mugun axaban da take ji hannunta
na rawa ta shiga tura kwalin magungunan
karkashin gado tana mayar da numfashi da
kyar wae kar ya gani, ya lura da abinda take,
ya rike hannunta da sauri yana kallon
kwalin yace “meye wnn,” girgixa masa kai ta
shiga yi tana neman xamewa daga jikinsa
ya daga kwalin tabs din yana kallo baki
bude, a rude ya jefar ya shiga cewa
“innalillahi wa inna ilaihi raji’un meye wnn,”
wani ihun ta kuma fasawa ta kankamesa
tace “wayyoo ya Aliyu, cikina, mutuwa xanyi
wllh,” yana jijjigata cikin tashin hankali ya
shiga cewa “ki gaya min shi kika sha
fateema?” kasa cewa komai tayi sae jujjuya
kanta da take cikin axaba, ya ga farar
takardar scan din dake gabanta ya dauka da
sauri hannunsa na rawa ya bude, jefar da
takardar yyi ya fixgota cikin mugun tashin
hankali yace “wayyo fateema ki gaya min
magungunann nn kika sha? Plss kiyi min
mgna,” a rude yake maganar, ita ko da kyar
ta shiga gyada masa kai tana jawo
numfashi kmr me shirin suma, ya dafe
kansa yana kallonta yace “nashiga uku, oh
my God,” saketa yyi da sauri ya fice daga
dakin, ta dinga ihu tana birgima cikin
axaban ciwo tana kiran Abbanta, ya dawo
dakin da sauri rike da allura, kwance ya
ganta cikin jini, yyi wani kara a rude ya jefar
da alluran hannunsa ya karaso kusa da ita
da sauri yace “ya salam, innalillahi wa inna
ilaihi raji’un, fateema fateema” kuka take
ssae tana juye juye kmr ranta xae fita jini
sae malala yake ta kasanta, ya dagota ya kai
mata wani wawan mari a gigice ya shaketa
yace “kika kashe min yarana, yhu kill my
kids” ta kankamesa tace “wayyo mutuwa
xanyi na shiga uku,” wani marin ya kuma
kai mata ya dagota ya buga ta da bango,
tunda take bata taba ganin yanayin da Aliyu
ya shiga ranan a tare da shi ba, idonsa ya
kada yyi jajur muryarsa na rawa yace “ki
gaya min ubanwa ya baki maganin nn, wani
asibiti kika je,” ya wurgar da ita ya buga
bango da hannayensa biyu yace “ya salam,”
juyowa taga ya sake yi ta fara kkrin fita
daga dakin ya fixgota ya shaketa yana huci
yace “me yarana suka maki kika kashe su
fateema,” ta rike hannayensa biyu cikin
kukan tashin hankali tace “no plss kayi min
rae ya Aliyu cikina xae kasheni,” bugata yyi
da bango da karfi ya fice daga dakin tasan
be gama da ita ba, tayi karfin hali ta rarrafa
ta fito daga dakin da kyar tana neman inda
xata safeena ta fito da sauri ta ja ta suka
shige dakinta ta rufe kofar da sauri, inteesar
ta xube kasan dakinta tana mayar da
numfashi har lkcn jinin dake xuba jikinta
bae tsaya ba
.
Aliyu ya fito kmr wani mahaukaci daga
dakinsa ya shiga nata a rikice bae ganta ba,
ya fito ya shiga buga kofar Safeena da karfi
ganin trace din jini tun daga kofar Inteesar
har nata, alamar nn inteesar ta shiga, cikin
tsawa yace “baxa ku bude min kofar ba”
cikin sanyin murya Safeenah tace “haba
dear ka sa ma xuciyarka ruwan sanyi mana,
so kke kayi kisan kai, ka bar ta da halin da
take ciki mana xaka dinga dukanta kuma,”
ya daka mata wani raxanannen tsawa yace
“na rantse da wanda numfashina ke
hannunsa idan ban hada dake ba kada Allah
ya bani abinda yake nema, baxxa ki bude
min kofa ba” ya karasa maganar yana huci,
ta bude baki da mamaki tana kallon kofa,
A’aaah lallai abun babba ne yau, to fa, ta dan
tabe baki tace “to ni ko sae dae kar ya baka,
don baxan tsaya hka kawae ina ji ina gani
ka kashe yar mutane gabana ba,” bae sake
cewa komai ba ya juya da sauri kmr xae
tashi sama ya koma dakinsa yana huci,
inteesar kam na durkushe dakin sae kuka
take tana juye juye kmr ranta xae fita, kila
karshenta ne ya xo yau, gashi har lkcn jini
bae tsaya mata ba sae bulbulowa yake, duk
kayan jikinta ya baci da jini hka ma dakin
safeena, safeena ta dauko Zaninta da sauri
ta mika mata a xuciyarta tana cewa “yau ai
sae dae jininki ya tsiyaye ki mutu yarinya
baxan bude kofar ba bare ya taimaka maki,”
inteesar ta kasa karban xanin, sae cewa
take mutuwa xanyi, safeena tace “baxa ki
mutu ba,” key suka ji Aliyu ya saka a kofar,
Inteesar ta fasa ihu jikinta na rawa taji kmr
ta sume ynxu ta samu saukin abubuwan
dake faruwa ynxu “wayyo kayi min rae ya
Aliyu wlh yau mutuwa xanyi, don Allah kaji
tausayina” ya afko dakin rike da kwalin tabs
din da ta sha yana huci, idonsa ya koma
jajur kmr gauta, kanta yyi ya fincikota da
karfi ya dago ta, muryarsa na rawa yace
“wllh wllh baki gaya min wanda ya baki
magungunan nn ba, sae na kashe ki kema
yau,” jikinta na rawa ta shiga girgixa masa
kai hawaye na bin kuncinta, ya shaketa da
karfi, cikin tsawa yace “baxa ki gaya min
ba,” ta yo waje da ido a tsorace, da kyar
muryarta a shake tace “xan gaya maka,” ya
watsa mata mari yace “uban me kike jira,” ta
fashe da wani matsanancin kuka ta juya
tana kallon safeena tace “ita ce ta kaini aka
bani,” Safeena ta yo waje da ido ta dafe
kirjinta tace “na shiga uku yarinya xata min
sharri, a ina kika ganni,” cikin kukan Axaba
Inteesar tace “ita ce ya Aliyu, ka tausaya min
cikina kasheni xae yi wllh,” a hankali Aliyu ya
saketa ta sulale kasa ya juya yana kallon
safeena da ta xama kmr mara gskyar gske,
duk ta rude, sae rawa bakinta yake ta kasa
cewa komai, ta fashe da kuka tace “wllh
wllh sharri tayi min Aliyu, a ina ta gan ni yau
da har xan kai ta a bata magani,” wani kara
yyi ya karasa kusa da safeenar kmr xaki ya
shaketa hawaye cike idonsa yace “ku ka
kashe min yarana, me suka maku safeena,”
bae jira me xata ce ba yyi wani irin buga