INTEESAR 4

.
Aliyu ya dan yi shiru snn yace “dama so
nake don Allah ki taimaka kiyi ma Fateema
magana ta koma dakinta, don xata fi jin
maganarki,” momy tayi masa wani mugun
kallo tace “lallai ka cika mara kunya, kasan
da warce kke magana kuwa, to fice min a
falo tun kan na baka mamaki,” ya sunkuyar
da kansa ya dan yi murmushi bbu yabo bbu
fallasa yace “ae dae don Allah nace,” cikin
tsawa tace “ka fice min a falo tun banje na
hadaka da ubanka ba, da can ni na raba ku
da xan hada ku ynxu, lallai ka cika fitsararre
mara tunani” ya mike yana murmushi ya fice
daga falon, tayi tsaki ta shige bedroom
dinta ranta a bace. Sashin inna ya koma,
inna na xaune da inteesar tana shafa mata
bayanta wae xuciyarta na tashi, daga bakin
kofar yana kallon inteesar yace “in har kika
koma gidana to baki cika yar halak, kiyi ta
xama gidanku, cikin ma in kinga baxa ki iya
ba kya iya xuwa ki xubar da shi ynxu,” ya ja
dogon tsaki ya sake labulen ya juya yyi gaba,
inna da ta kasa rufe baki ta mike da sauri ta
bi shi tace “ka dawo ka bata takardarka don
uwarka, idan ba kaddara ba me xae kaita
auren mahaukaci,” ya juya yana kallon inna
yace “sae dae in ku ne ke hauka,” yyi gaba
abunsa. Inteesar da komai nata ya tsaya ta
kasa cewa komai sae hawayen da take, inna
ta shigo tace lah meye abun kuka, ki rabu
da dan iska wllh na kashe aurenku ynxun
nn, ya ya kuma ki haifesu ki bani na kai
masa ya basu nono, inteesar dae bata ce
komai ba amma duk jikinta yyi sanyi, ta bar
inna na ta surutunta har kusan karfe goma
snn tayi mata sae da safe tayi bangarensu
jikinta a mace, momy bata yi bacci ba tana
xaune falo, ta shiga daki ta kwanta ta
lumshe idonta duk da tasan ba bacci xata yi
ba, momy ce ta kirata ta fito falon ta xauna
tana kallonta, momy tace “kina ji na
fateema,” ba hka nn momy ke kiran sunanta
ba don hka ta nutsu tana sauraran me
momy xata ce mata, momy tace “duk me
xan ce maki a nn kar kiyi min musu, yhu
obey b4 complain kinji” kai kawae inteesar
ta gyada mata.
Momy tace “ki shirya ki koma dakin ki gobe
da safe,” inteesar ta tsaya kallonta da
mamaki, nn da nn hawaye ya cika idonta,
xata yi magana momy tace “ban son naji
abinda xaki ce, ba don bana sonki nace ki
koma dakin ki ba fateema, sau biyu Alhaji
yana min magana nake shashantarwa don
har cikin raina ban son aurenki da yaron nn,
but ynxu ina da dalilin cewa ki koma dakin
ki, kiyi hkuri kinji inteesar Allah xae shige
mana gaba, kuma ga matan gidan nn sae
yada ki a waje suke wae ae ya sakeki, hkn
ne ma yasa Alhaji yyi min magana nace maki
ki koma dakin ki, idan lkcn haihuwarki yyi
sae ki dawo gida ki haihu, ki kwantar da
hnkalinki inteesar lkcn da ni da kaina xan
bukaci Alhaji yyi masa magana ya baki
takardarki na nn xuwa don ko bayan raina
ni ban yrda kici gaba da xama da Aliyu a
matsayin mijinki ba, ” inteesar tayi shiru ta
kasa cewa komai jikinta yyi sanyi jin furucin
momy na karshe, ta tabbatar da ta gaya ma
momy irin cin mutuncin da yyi mata daxu da
baxata fara cewa ta koma gidansa ba, sae ta
samu kanta da kasa gaya ma momy abinda
yyi mata, ta mike a sanyaye tayi ma momy
sae da safe ta shiga bedroom ta kwanta,
duk da ta so tayi kuka ko xata ji sanyi amma
sae ta nemi kukan ta rasa. Washegari da
safe karfe takwas ta gama shirinta ta dauki
dan hanbag dinta tunda ba wani kaya xata
dauka ba, momy ta bata dubu daya kudin
mota, momy tace “kije kiyi ma inna sallama,”
tace mata “to” snn ta fita Momy tayi mata
Allah ya kiyaye, sae ta samu kanta da rashin
son xuwa gun inna don kar ta hanata tafiya,
kasa xuwa yi mata sallaman tayi ta fita daga
gidan kawae ta taka har babban titi snn ta
tsayar da tricycle ta gaya masa inda xata ta
shiga, suna isa ta fito ta mika masa kudinsa
ya bata canjinta snn ta yi hanyar gate ta
danna bell mai gadi ya bude mata ta shiga
gidan, a sanyaye ta karasa balcony ta murda
kofar falon taji shi a rufe, ta kai minti kusan
goma a tsaye snn ta rumtse idonta ta danna
bell, safeena ce ta sauko bude kofar
kyanwar da a cewarta ta dauko daga
gidansu don tana mugun son mage na biye
da ita a bayanta, shi dae Aliyu ya rasa yanda
xae yi da ita da magen ne amma har ga
Allah baya son mage, ta juyawa taga magen
a bayanta sae wani tsalle yake ta sa kafa ta
hauresa ya koma sama da gudu, Aliyu yyi
tsaki ya maida dubansa ga TV, duk da
ofcourse tasan ko waye a bakin kofar sae ta
shiga cewa “kai bala sae ynxu ka ga daman
xuwa kai da nace maka tun karfe takwas,
ynxu da bbu kwata kwata ya kke son nayi
gashi baya cin komai sae potatoe da safe” a
fusace take maganar kmr gske, inteesar ta
dan koma baya ta bude kofar, safeena tayi
turus a bakin kofar tana kallon cikin
inteesar tana dan murmushi, kallo daya
inteesar tayi mata ta dauke kanta, wasu
shegun kayan bacci ne jikinta sae mayafin
da ta yafa kuma a hka take shirin fitowa
gun driver don rashin sanin ciwon kai, shi
kuma da yake bae damu da ita ba bae
hanata ba, gefenta inteesar tabi xata wuce
ta bangajeta ta tare hanyan tace “ina kike
tunanin xaki hka,” Aliyu dake kwance kan
kujera yana kallonsu don shima yyi
mamakin ganin inteesar yace “ki kyaleta kila
kayanta ta xo kwasa,” inteesar ta kasa cewa
komai don takaici, hawaye ya cika idonta
amma bata bari safeena ta gani ba, safeena
tace “ayyo,” snn ta matsa daga bakin kofar,
da kyar inteesar ta shiga gidan tayi hanyar
stairs xuciyarta na raya mata ta kwashi
kayanta kawae kmr yanda yace ta koma,
safeena ta bita da kallo tana murmushi
mugunta don sarae tasan da xuwanta, da
sauri Aliyu ya mike yana kallon safeena yace
“kin goge ruwan sama ne,” safeena ta dan
yatsine fuska tace “to ni na xubar,” yayo
waje da ido yyi hanyar stairs da sauri har
yana bugewa yana kwala ma inteesar kira
ta tsaya. Gano abinda yake gudu Safeena
tayi ta bisa da sauri gabanta na faduwa don
mugunta a xuciyarta tace kai abu biyu xae
hade mata knn da sauri kan ya haura sama
tace “kai wasa nake na goge,” ya juya yana
kallonta amma hankalinsa bae kwanta ba,
xae yi magana yaji inteesar ta fasa wani
raxanannen ihu a sama, ya haura sama da
sauri yana cewa “innalillahi wa inna ilai hi
raji’un,” safeena ta doka uban tsalle ta shiga
kiran uwarta hannunta na rawa, uwar ta
daga tace “wayyo momy mutumin nn ya iya
aiki ta xo wllh,” da sauri Hajiyar tace “to
magen fa ta ganshi,” safeena tace “ba dole
ba ae mutumin ca yyi yana jin kamshinta
xae fito yana jiranta da na xo bude mata
kofa kar ki ga yanda ya biyo ni da gudu,
wato yaji kamshinta, na sa kafa na hauresa
ya koma sama ya jirata a can, ae ko da gudu
ya koma momy har wani rawa jikinsa fa
yake, kuma kinsan me momy abu biyu ya
hade mata Aliyu ya xubar da ruwa sama
yana jira in goge naki gogewa kinga tana
hawa sama tsantsin ruwan xae kwasheta
sae kuma ga aljanar magen ma na jiranta,
ae ciki kam kema kinsan sae lbri momy” ji
tayi Aliyu na kwala mata kira a rude, safeena
tace “xamuyi waya anjima momy gashi can
yana kirana,” ta katse kiran xuciyarta fal
murna ta haura sama cikin muryan tashin
hankali da tsoro take cewa “me ya faru
Honey ruwan bae gogu bane,
.
Aliyu na rungume da inteesar dake ta kuka
tana shisshigewa jikinsa safeena ta hauro
sama, cikin tsawa yace “me kika ce min,” da
sauri ta sauka kasa ganin yanayinsa, ya
dago inteesar yana girgixa kai cikin tashin
hankali yace “ta ina kika fadi fateema,” kin
bude idonta tayi amma jikinta sae rawa