INTEESAR 4

ba’a sanar da ita ba, don naga jarabanta sae
wanda ta manta, ae kuwa tsaf xanje in daga
mata hankali da kaina xan fada mata yau
yau din nn” da sauri uwar safeena tace “ke
Hajiya Aisha don me xakiyi hka, ae magani
xata nema mata ta warke,” Hajiya ta hade
rae tace “ita likita ce da xata nema
matamagani ba kunce suna asibiti a lgs ba,”
Hajiya safeena tace “to bari kiji Aisha mu ne
nn muka haukatar da ita don danki ya koma
gunki, don an tabbatar mana da cewa asiri
uwarta tayi ma Aliyu ya manne ma yar ta
baya jin maganar kowa sae na yar karamar
yarinyar nn, ko baki lura bne? Kuma wnn
ciki ancemana ba na Allah da annabi bne, ba
cikinsa bne so wae suke su ci gadon Aliyu ”
Hajiya da jikinta yyi sanyi lkci daya ta bude
baki tana kallonsa tace “ku kuka Haukatar
da ita knn,” daga safeenar Har Uwarta suka
hada baki “kwarrae kuwa, hkn kadae shine
mafita,” Hajiya ta danyi murmushi tace “ikon
Allah,ina ma nima xan xama kamar ku wllh
kuna burgeni, to amma ya xa’ayi dana ya
dawo guna, tunda dae ynxu suna can tare
kar ma ta shafa masa haukan, shi yasa Aliyu
ya daina daga kirana ashe” Hajiyar safeena
tayi murmushi tace “kar ki damu Hajiya Aliyu
xae dawo gare ki amma fa ba hka nn ba
don asirinsu na nn jikinsa,” hankalin Hajiya
a tashe tace “to ya xa’ayi ya karye,” Hajiyar
safeena tace “ynxu xuwa xakiyi ki lallaba
maigidanki, kawae marairaicewa xaki yi
kice ynxu Alhaji ashe abinda ya samu
yarinyar nn knn kke boye mani, da fa na
kowa ne, kuma dan adam baya wuce
kaddararsa, xaki gajikinsa yyi sanyi hka xaki
ta jan ra’ayinsa kmr ta kirki nn da nn xaki
ga ya baki hkuri, to daga nn sae kice don
Allah kina son yabarki kije ki dubota nasan
xae bar ki, to kina xuwa can akwae wani
magani da xan baki cikin abin sha xaki
tabbatar kin sa ma Aliyu in’sha Allahu asirin
da suka mashi xae karye,kuma kina xuwa
da kwana biyu ki dawo gida, ko sati
baxa’ayi ba xakiga ya biyoki shknn shi da ita
kuma har abada, danki ya dawo hannunki
wa inda suka ga xa su iya jinyarta sae suyi
ta fama,” Hajiya tayi dariyan jin ddin
shawarar Salame tace “shnn salame ngdd
ssae, duk yanda kika ce hka xanyi bani
maganin na wuce, Hajiya salame ta shiga
daki ta dauko mata maganin dake kulle a
leda ta bata, tayi mata gdya cike da jin ddi ta
masusallama ta bar gidan xuciyarta fal
murna shknn Aliyunta xae dawo gareta
asirin matsiyatan mutanan can xae karye.
Tana fita Safeena da uwarta suka tuntsure
da dariya uwar tace”shknn xata je ta dawo
maki da Aliyun ki, ya xama naki na har
abada don ko ita da ta haifesa mantawa xae
yi da ita ke kadae xae dinga gani a duniya,”
suka dinga dariya suna jin jina ma sakarcin
Hajiya da rashin tunaninta. Ita ko Hajiya tana
komawa gida tayi yanda suka ce mata da
daddare a falon Abba, Abba yyi shiru ya
kasa cewa komai amma jikinsa yyi sanyi, ita
ko har da dan hawayenta, ganin ta fara cin
nasara yasa tace “to shknn Alhaji kila kai
kadae kasan dalilinka na rashin son gaya
mana, amma kayi hkuri ka barni naje na
dubota don Allah don Annabi,” yyi shiru na
kusan minti biyar snn daga karshe yace “to
shkknn kya iya xuwa, suna india amma
ynxu hka,” ta dafe kirji da alaman jimami
tace “ohh ni yar nn, wnn wace irin fitina ce
ga ciki” sae kuma ta fashe da kuka Abba
yace “ba kuka xakiyi ba, addua’a xakiyi
mata, amma bana son maganar nn ya fita
daga nn ki bar shi a cikin ki kawae har Allah
yasa ta samu lfya,” Hajiya na share
hawayenta tace “to Alhaji in son samu ne ko
xuwa jibi na tafi tunda ina da visa,” yace “to
shknn,” ta mike tace “Allah ya shigemana
gaba” snn ta fita daga falon Abba xuciyarta
fal murnar xata je ta dawo da danta.
Vidyasagar institute of mental health and
neuro sciences, shine asibitin da su Aliyu
suka sauka a new delhi, babban asibitin
mahaukata ne na india, kuma basu samu
wata matsala ba aka karbesu
.
Kwanansu hudu a asibitin Hajiya ta iso, ynxu
kam haukan inteesar da sauki tunda ta
daina buge buge sae dae kawae ta xauna ta
tsura ma abu ido tana kallo, da yamma
Hajiya ta shigo asibitin bbu wanda bae yi
mmkin ganinta ba barin Aliyu amma bae
nuna ba, kuka ta fashe masu da tana jijjiga
kai tace”ashe abinda ya samu inteesar knn,
bbu dae wanda ya tanka mata ita kuwa
inteesar dama bacci take, ganin sae fa tayi
da gske yasa ta kama hotel nn indian ynda
kowa xae saki jiki da ita yyi xaton jinya ta xo
ganin dari dar ake da ita, duk safiyya da
yamma take xuwa duba inteesar da kayan
fruit, Anty Nafeesa da Aliyu a asibitin suke
kwana wajenta, Faruuq da Haisam kuma
hotel suka kama, likitocin suka mayar da
hankali ssae a kanta sbda cikin da ke jikinta
don at an ytym xata iya haifesu, suna xaune
da yamma ranan Aliyu na bata abinci tana
karba, Faruuq na xaune yana kallonsu Anty
Nafeesa taje hutawa a hotel din da su
Haisam suke, Hajiya ta shigo rike da ledan
fruits dinta da lemo, ta xauna, Aliyu ya
gaisheta hka ma Faruuq, ta amsa tana
tambayar jikin Inteesar, ta mike ta dauko
kofi tayi waje kmr taje daurayewa ta bude
maganin da take yawo da kullum a bakin
xaninta ta xuba kadan, snn ta koma ciki ta
bude juice tacika kofin ta dauka ta mika ma
Aliyu tace “dubi yanda ka rame son, nasan
baka cin abinci yau ma bn ga alamar kasa
komai a cikinka ba ga lemo ka kora kaji
son,” ya rufe abincin da yake ba inteesar
ganin takikarba kuma ya dagata sama yace
“ni naci abinci ae,” snn ya ja ta suka sauka
xuwa kasa don yawanci a kasa suke wuni
gun pool ko flowers. Shi kansa Faruuq bae ji
ddin abinda Aliyu yyi ma uwartasa ba yace
“kawo ni na sha mum,” da sauri tayi
murmushi tace “A’a bar shi kawae,” faruuq
ma yyi murmushin jikinsa dae yyi sanyi ya
mike ya sauko ya samesu a kasa, bakacewa
hauka inteesar take ynxu duk ta nutsu ssae
sae in tayi wani abun ne wani lkci xaka
gane har lkcn haukan na jikinta, kusa da
ruwa ya samesu a xaune, faruuq ma ya
xauna yace”gskya she’s respondin 2
treatment a nn Aliyu naga improvement,”
Aliyu ya dan yi shiru snn yace “hka ne, but
lkcn haihuwarta ya kusa faruuq a hkn xata
haihu bbu hankali tare da ita,”Faruuq yace
“muyi ta Addua frnd kila ma haihuwar ne
xae yi sanadiyar dawowa da hankalinta,”
Aliyu bae ce komai ba sae kallonta yake cike
da tausayi. Yau suka cika sati daya aIndia,
Hajiya kam ta rasa yanda xata yi Aliyu ya sha
maganin da su safeena suka bata, ynxu
xuwanta xae xamo a bnxa knn tayi, da
yamma ne misalin karfe hudu saura Aliyu na
xaune da inteesar kusa da babban pool din
dake cikin asibitin, ga mahaukata da suka
fara warkewa xaxxaune a wajen kowa nata
harkan gabansa, tun safe ya lura inteesar
bata jin ddi, yasan lkcn Haihuwarta ne ya
lura nakuda take duk da bata nuna tana jin
komai ba, shima duk hnkalinsa ya tashi
faruuq kadae ya gaya ma, faruuq ya fita siyo
abubuwan da ya kamata,Anty Nafeesa ta tafi
hutawa a hotel, Haisam jiya ya koma Nigeria,
Hajiya kuwa ta fita yawon xaga gari
xuciyarta fari tas don tana tunanin yau ce
xamansu ta karshe ita da Aliyu a indiadon ta
lura da abinda yake sha a asibitin wani lemu
ne kadae abincinsa ta xuba masa maganin
ciki snn ta bude fridge a ward din da
inteesar take ta ajiye masa hkn yasa taje
xaga garikafin ta tafi anjima idan taga ya
sha, xamowa inteesar tayi daga kan kujeran
da take ta xauna kasa ya lura duk axaban
ciwo ne kesawa tayi hka, shima ya dawo
kasan yana kallonta da damuwa yace “ina
ke maki ciwo fateema,” bata ce komai bata