INTEESAR 4

dauke kanta, suna nn xaune a hka har na
kusan minti sha biyar ya juya yana kallonta
yaga robon ruwan wasu mutane kawae
take kallo, ya kamo hannunta yace “xaki sha
ruwa ne inteesar” kai ta gyada masa ya
koma baya da mamaki yana kallonta, da
sauri ya mike yace “ina xuwa bari na kawo
maki kinji bata sake cewa komai ba yyi
hanyar stairs da sauri yana waiwayota
xuciyarsa na bugawa ya haura sama dauko
mata ruwa, tsam ta mike ta fara kalle kalle ta
bi hanyar da taga mutane na bi, da sauri
take tafiyar kmr ana turata, har ta isa gate
masu gadi suka bita da kallo don bbu
uniform din mahaukata jikinta, ta fice tayi
hanyr hagu duk da tafiya ce mai shegen
nisa tana ta tafiya har ta daina hango
asibitin, Aliyu ya sauko rike da ruwa da kofi
a hannu ya ga wajen wayam bbu fateema,
kalle kalle ya shiga yi a rude bae ga alamarta
ba, ya hango faruuq ya karasa gunsa da
sauri yace “fateema fa,” faruuq yace “wace
fateemar ba nn na bar ku tare ba,” ya dafa
faruuq ganin kafafuwansa sun kasa
daukansa yce “wlh nn na barta naje dauko
mta ruwa” cikin tsawa faruuq yce “wat?
Don me xaka barta ita kadae” tare suka
shiga xaga asibitin suna nemanta ta ko ina
amma basu gnta ba sune har gate duk Aliyu
ya birkice kmr wani xautattce, sae ga Anty
Nafeesa ta shigo asbitin rike da abinci da
mamaki ganin yanda suka tara jama’ah tace
“me ya faru” faruuq yy karfin halin cewa
“bamu ga fateema ba” kmr kar faruq ya fadi
hka sukaji Aliyu ya saki wata irin kara ae sae
da asibitin ya dauka sae kawae suka ga ya
sulale wajen.
Hajiya ta shigo asibitin rike da kayan
tsarabar da tayo ma yan Nigeria barin
safeena da uwarta tana dan rera wakarta,
jikin wani ward taga Nafeesa tsaye tana
kuka ssae ga wani likita da alamar dan
Nigeria ne yana lallashinta, da sauri ta
karasa kusa da ita tanakallonta tace “me ya
faru Nafeesa,” da kyar Anty Nafeesa na
girgixa kai tace “bamu ga inteesar ba,”
Hajiya tayi shiru tana kkrin boye murnar ta,
can kmr warce ta tuna abu da sauri tace
“Aliyu fa,” Anty Nafeesa ta kasa cewa komai
sae kuka, Hajiya ta juya a rude tana kallon
likitan dake gaban Anty Nafeesa tace “ina
da’na,” da sauri ta bude ward din da
inteesar take mai xata gani, Aliyu yana
dambe dalikitocin dake kansa sae Fateema
yake kira, hajiya ta fito a guje tayi kan Anty
Nafeesa a rude tace “me ya samu Aliyuna,”
likitan ne ya bata amsa “suma yyiya farfado
a hka shima ana ga kmr ya samu matsala a
kwakwalwa,” Hajiya ta fasa ihu tace”hauka
Aliyu yake yi hka,” kuka ta fashe da a rude ta
ciro wayarta ta shiga danne danne tana
gunjin kukasae rawa hannunta yake ta kara
a kunne, “hello salame kina jina maxa ku je
ku karya asirin nn da kuka yi ma inteesar ya
koma kan dana wllh,” ta katse kiran a rude
tana rusa kuka sae kallonta Anty Nafeesa
take da mamaki, cikin kuka tace “wlh
Nafeesa safeena ce da uwarta suka
haukatar da inteesar su suka haukatar da
ita suka gaya min,” Anty Nafeesa ta dafe kirji
ta kasa cewa komai ta fashe da kuka tayi
waje, Hajiya ta bita ita ma tana kukan kmr
mahaukaciya, Faruuq ya shigo asibitin a jike
don anyi ruwa ssae, bbu inda bae xaga ba a
india amma bae ga inteesar ba, ynxu ma
daga gidan talabijin da redio yake, duk ya
xama kmr wni mara lfya, ganin inda su Anty
Nafeesa ke kuka yasa da kyar yace “Aliyu fa,”
cikin kuka Hajiya tace “wllh ya haukace
faruuq ku ceci rayuwar da’na ku nemo
inteesar, ina inteesar ta shiga don Allah a
nemota,” ta fashe da wani matsanancin
kuka ta xube wajen, sae kallonsu ake
gwanin ban tausayi, faruuq ya dafa bango
ya kai minti kusan biyar a hka da kyar ya
haura sama ya shiga ward din da inteesar
take, duk alluran da suka dinga yi ma Aliyu
bae nutsu ba don hauka karara ya dinga
gwada masu, duk aka fita aka kulle dakin
aka barshi shi daya ya dinga buge buge
yana jijjiga kofar abun dae ba ddin ji,
likitocin suka hana faruuq shiga ya jingina
jikin bango hawaye ya cika idonsa da kyar
ya ciro wayarsa ya shiga neman layin
Haisam, muryarsa na rawa yace “Haisam
abu ya baci Haisam inteesarta fita daga
asibitin, Aliyu baya cikin hankalinsa shima
brain dinsa ta samu matsala, ka sanar da
Abba baxan iya gaya masa ba” bae jira me
Haisam xae ce ba ya katse wayar sae
hawaye. Inteesar kamnata tafiya abunta sae
dae idan taji kmr an mintsileta a mararta ta
xauna ta huta snn ta ci gabada tafiya ko ina
tabi sae an kalleta, hadari ya hadu garin
ssae tana ta tafiya abunta kowa nata kkrin
ganin ya isa gidansa, har daga karshe ruwa
mai karfi ya sauka ta xauna kan wani dakali
ruwan ya dinga dukanta amma bata damu
ba, har ruwan ya tsagaita bayan kmr awa
biyu, ta mike da kyar ta ci gaba da tafiya
tana rawan sanyi, kasa ci gaba datafiyar tayi
dae dae wai babban plaza ta dalilin wani
mugun ciwo da taji mararta da kugunta
nayi a tare da kyar ta ja kafa ta samu wani
gefen mota ta durkushe gaban plazan tana
rike da kugunta sae rawan sanyi take tana
yarfe hannu alamar axaba, indiawa sae
kallonta suke suna wuce ta, don su dama
basu gaji taimko ba ko a tsakaninsu, kuka ta
shiga yi ganin ta kasa daure ciwon Abbanta
ta shiga kira tana juye juye jikin motar da
take taji an bude motar ta koma baya da
sauri, da ganinsu matada miji ne, matar na
kallonta da yaran india tace “keme kike yi a
nn,” kai ta daga tana kallonsu bakaken fata
ne kmr ita amma da gani xasu Haifeta, ta
mike da kyar tana rike da kugunta xata bar
wajen matar tace “amma ke yar Nigeria ce
kuma bahaushiya ko,”ko kallon matar bata
yi ba taku daya biyu ta xube wajen tana
wayyo cikinta, matar ta juya tana kallon
mijinta dake tsaye kmr wani tsoko yana
kallonsu tace “Abbanmu kalli fa yar uwar mu
ce ga kuma alamar bata da lfya mu taimaka
mata,” bata jira me xae ce ba ta karasa kusa
da inteesar da sauri ta dago ta tana kallonta
tace “sannu kinji yan mata daga ina kike
hka,” inteesar bata ce komai ba sae girgixa
kai da take don axaba, matar ta dagota da
sauri ta saka ta bayan mota ita ma ta shiga
tace”mu je Abbanmu,” ya shiga motar ya
tada suka bar wajen, ihu ta dinga masu a
mota duk ta rikice jin axaba na neman
kasheta matar na rike da ita tana tofa mata
addua, mijin ma duk ya rude yace “asibiti
xamu ko,” tace “A’a muje gida kawae xan
karbi haihuwar,” babban gida ne ssae,
matar tace “ka taimaka min mu fito da ita
Abbanmu,” ya xagayo yana kallon inteesar
da ta gama fita hayyacinta ciwo ya ci
karfinta, tace “help me mana Abbanmu,” ya
koma baya da sauri har lkcn yana kallon
inteesaryace “baxan iya ba, bari na kira
maku yan aiki,” yyi cikin gidan da sauri sae
gashi ya fito da yan aiki suka taimaka mata
ta shiga ciki da inteesar
.
.. Da taimakon matar Inteesar ta Haifo
santala santalan yaranta maxa biyu, ba
karamin wahala ta ci ba, matar ta tausaya
mata ssae, babban likitace don hka tayi
mata duk abinda ya kamata snn ta kaita
bedroom dinta ta kwantar da ita kan ta
hado mata tea har tayi baccin wahala, mai
gidanta kuwa kasa xaune yyi har sae da
inteesar ta haihu, snn hankalinsa ya kwanta,
matar ta gyara yaran ta kaisu gefen uwarsu
ta kwantar dasu gashi gaba dayansu basu
da lfya, inteesar bata farka ba sae can tsakar
dare matar na xaune gefenta rike da dayan
yaron dake ta kuka ta kwantar dashi tana
mata sannu, kai kawae inteesar ke gyada
mata, ta kira yan aiki su kawo mata tea,
suka kawo suka ajiye, matar tace maxa ki
sha ki basu nono yunwa suke ji kuma duk