HAUSA NOVELINTEESAR 4

INTEESAR 4

basa jin ddi, inteesar bata ce komai ba

matar ta taimaka mata tamike xaune snn ta

mika mata tean ta shiga kurba a hankali,

maigidanta ya shigo ya xauna yana kallon

inteesar yace “sannu baiwar Allah ya jiki,” ta

dago kai tayi shiru tana kallonsa, wata

yarinya ce da baxata wuce shekara goma

sha biyu ba ta bude kofar ta shigo ta karaso

kusa da inteesar da harshen hausa tace

“Sannu Anty,” inteesar tayi murmushi tace

“na gode” yarinyar ta xauna tana kallon

bbies din, ba karamin kama suke da

inteesar ba iyayen sae kallonsu suke, daga

karshe Abbanmu ya mike ya bar dakin,

inteesar ta ajiye tean hannunta matar tace

“har ya isheki,” ta gyada mata kai tace “na

koshi,” matar tace “bari a kawo maki abinci

ki ci kinji,” inteesar bata ce komai ba matar

ta mike ta fita, inteesar na kallon yarinyar

tace “ya sunanki,” yarinyar tace “sunana

Zainab,” inteesar tayi murmushi tace “nyc

name, wa ya kawo ni gidan nn,”yarinyar

tace “mum nd dad ne suka kawo ki daxu,”

inteesar tace “wani gari ne nn,” yarinyar

tace”india,” inteesar tayi shiru bata ce komai

ba gabantana faduwa ranta a dagule, india

kuma, me ya kawota india

.

. Ba karamintashin hankali kowa ya shiga ba

rashin ganin Inteesar har na kwana biyu,

barin ma Abba don shi ba ma ta Aliyu yake

ba, ta yar mutane yake, Hajiya dae ta dage

kowa ta gani tace su safeena ne suka yima

inteesar asiri ta haukace ita ma dae ta xama

kmr mahaukaciyar, idan ta gaji da gantalin

don bbu wanda ke kulata kowa abinda ke

damunsa yafi karfinsa sae ta dawo ta xauna

bakin kofar inda Aliyun yake tayi ta rusa ihu

tana kuka har aka fara tunanin ko ita ma

haukan xata yi ne, Aliyu kam ya xama abun

tausayi ba shi da aikin yi sae na kiran

fateema duk ya xama wani iri haukan nasa

ma sae yafi nata shi dae a bashi fateemar

shi, kullum sae an xubar masa da hawaye

don tausayi, gashi kullum su Faruuq sae sun

xaga india neman inteesar bayan sanarwar

da suka bada gidan talabijin da sauransu,

Bbu abinda yafi daga ma Abba hnkli irin

ynda xae tunkari momy yace basu

gainteesar ba ba a ma maganar inna da ta

dage xata xaman jego, hka kowa ya xama

kmr mara lfya a asibitin bbu me xama yaci

kwakkwaran abinci, inteesar kam na xaune

hankali kwance gidan bayin Allahn da suka

tsinceta ita da yaranta, sae dae fa yaran duk

basu da lfya kusan kullum allura ake masu

barin hassan din, duk da rashin lafiyar tasu

hkn bae hanasu ci ba kmr me, shegen ci ne

dasu ssae basa koshi ko kadan ko da

yaushe bakinsu motsi yake, suna mugun

takura inteesar gashi ruwan nonon ma bae

wani cika ba, hkn yasa matar tasa Abbanmu

ya siyo masu madaran jarirae take dama

masu ta basu, shknn inteesar ta samu

kwanciyar hankali, ko kadan ba ita take

rainonsu babarin ma ba iyawa tayi ba,

matar ce take masu komai nata kadae ta

basu nono, nonon ma ita ta koya mata

yanda xata dinga basu, kuma suna sha tana

ihu wae xafi take ji, ba karamin dariya take

ba matar ba, matar tace “amma ke yar fari

ce ko,” ranarda suka cika kwana biyar ne

Abbanmu da matarsa da suke cema Anty

suka sa inteesar gaba suna tambayarta me

ya kawota india, inteesar tayi shiru ta rasa

me xata ce tunda ita ma ganinta kawae tayi

a india, a hankali ta fara magana “wllh Anty

nima bansani ba kawae na gan ni ne a nn

bn san wa ya kawo ni ba,” duk suka yi shiru

suna kallonta da mamaki, Anty tace “a

Nigeria wani state kike to” inteesar tace

“kano,” Anty tace “to mai gidanki fa?” tace

“shima a can yake,” duk suka yi shiru suna

kallonta, Anty tace “kin tabbata gskya kike

fada mana inteesar,” inteesar kmr xata yi

kuka tace”Allah gskya nake gaya maku

Anty,” matar tace “to shknn bari ki kara

kwari sae mu kai ki gida,” inteesar dae bata

ce komai ba, Abbanmu ya dauki Hussaini

yana kallonsa yace “wnn kmr Husainin

muko Antynmu,” Anty tace “wllh kuwa baka

ganin ita ma inteesar kmr su kusan daya da

Zainab, Allah mai iko,” duk suka yi dariya

Abbanmu yace “baki da nmbr kowa can

gida ne kada hankalinsu ya tashi dayawa,

koma dae kuna da yan uwa a nn india ne?”

inteesar tace “nima ban sani ba,” Antynmu

tace “ka bari Abbanmu nn da sati daya ae

xamu je Nigerian,”Abbanmu yace “to shknn

Allah ya kai mu,” snn ya mike ya fita, Anty ta

shiga hada masu madara don sun fara

mutsu mutsun yunwa, kmr ba jarirae ba

yaran, Antynmu tace “yaran nn dae da

yunwa kike barinsu suna cikin ki, yara da ci

hka tubarkallah,” inteesar tayi murmushi

bata ce komai ba ta tsura ma yaran ido,

farare ne ssae kmr ita amma bbu abinda

suka bari na Aliyu, idonsu, bakinsu

hancinsukomai nasu na Aliyu ne, yaran kmr

yaran larabawa ga lips dinsu pink gwanin

sha’awa, tayi murmushi ta kauda kanta, ko

wani farin ciki xae yi idan yaga ya’yansa

masu kama dashi, Antyn mu ta dauki dayata

shiga bashi feeder ita ma ta dauki dayan ta

daukinasa ta fara basa don ta fara koyan

yanda ake yi gun Anty, Anty na da kirki ssae

tunda ta haihu a bedroom dinta take, kayan

da suka dinga siya ma jariran sae ka rantse

kace sun taba saninta, komai nasu enuf a

gidan suma autansu yan biyu ne masu

shekara takwas, kusan duk yamma sae

Zainab ta shigo da frnds dinta daban daban

wae su xo su ga Antyn ta mai kama da ita.

Inteesar taji kmr tayi ta xama a gidan don

tana jin ddin xama da su ssae. Abba na

xaune abun duniya ya ishesa Anty

Nafeesana gefensa ita ma ba um ba um um

sae uban tagumin da ta rafka, wayar Abba

tayi kara ya fito da shi yana kallon mai

kiransa, inna ce, ya kasa dagawa har sae da

ya kusan tsinkewa, kmr xata fasa masa

dodon kunne yaji tace “helo Bukar ne,” yace

“eh nine baaba,” “to wae wnn wani irin

tafiya ce kayi Bukar kasan da cewar wnn ne

watan Haihuwar inteesar har yau an rasa

wanda xae kai ni, tun yaushe kace na hada

kayana amma kayi min shiru to ni ynxu xan

sa kursum ta raka ni gidan, ynxu hka ma a

bakin gate nake wllh da jakata” Abbaya

girgixa kai ya rasa me xae ce mata, da sauri

ya samo abun cewan yace “kiyi hkuri baaba

gobe xan dawo sae nasa a kaiki, kuma su

dinma ae basa nn suna lgs,” tace “yo ae can

din dama xani,” Abba yace “to shknn baaba

ina nn dawowa gobe ki koma ciki,” ya katse

kiran ya dafe kansa cikin tashin hankali yace

“ban san ya xanyi ba Nafeesa,”

 

..Karfe tara na safiyar lahadi inteesar suka

sauka kano daga lagos, Antynmu na rike da

Hussaini ita tana rike da Hassan kmr yanda

suke ce masu, Zainab na rike da wani yar

jakan kayan abincin yaran don da ita aka

taho aka bar yan biyu a india gun yan aiki,

Abbanmu kuma na janye da trolley din

kayan twins din, taxi suka dauka har kofar

gida, Abbanmu ya ba shi kudinsa, snn

inteesar ta shiga gaba Anty na biye da ita

abaya Abbanmu ya tsaya daga waje shi da

Zainab, hka kawae taji gabanta na faduwa,

sae gidan yyi mata kmr tayi shekara bata

ganshi ba, bbu kowa tsakar gida kuma

dama sae da tayi wnn addu’ar a xuciyarta,

direct bangaren inna ta nufa Anty na biye

da ita a baya, har suka isa ta bude kofar a

hankali, inna na xaune ita da kursum dake

mata kitso tana ta bala’i Hajiya tayi tafiya ba

tare da saninta ba sae jiya ta lura bata

gidan, nn kitson xuwa gidan inteesar ake

mata don jiya Abba ya dawo shima daga

india ta sa shi gaba ko yaki ko ya so gobe

xata tafi lgs gidan Aliyu, rasa me xae ce

mata yyi, ita don tsabar masifa bata lura da

yana cikin tashin hankali ba, a nutse ya fara

mata magana yace “inna Aliyu fa bae da

lfya……” da sauri tace”Allah ya basa lfya kuma

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button