INTEESAR 4

ni ai gun inteesar nace xanje ba Aliyu ba,” to
kawae yace mata don takaici ya fice daga
falon, inna aka shiga shirya kaya ba ji ba
gani har da su kitso, Abba kam da sassafe
ya bar gidan ranar da tace xata tafi lgs din,
bayan ya gaya ma momy abinda ake ciki da
kuma inteesar da basu gani ba don yaga
boye mata bashi da wani amfani, momy
batanuna masa komai ba, amma ba karamin
kukan tashin hankali tayi ba bayan fitarsa,
inna ta daga kai da sauri xata fara masifar
waye ya bude mata kofa ba sallama, suka yi
ido hudu da inteesar, inna ta yo waje da ido
ta mike da sauri tana kallon yaron hannunta
tace “me xan gani hka ni Rahmatu, har kin
haihu ban je ba kuma ban sani ba,” kawae
sae ta fashe da kuka tace “Amma Allah ya isa
tsakanina da yan gidan nn gaba daya, ynxu
anyi min adalci knn” takaici ya ishi inteesar
ga Anty a tsaye, gskya inna bata yi ba,
shigowa tayi ta xauna Anty ta kasa shigowa
sae kallon inna take, inna ta ciro waya tana
huci tace “maxa nemo min layin Bukar,”
kursum da gaba daya hankalinta na kan yan
biyu ita ma da mamaki ta karbi wayar takira
mata Abba ta mika mata, cikin daga murya
tace “amma Allah sae yyi mana hisabi da ku
Bukar, ynxu yarinyar nn ashe har ta haihu
ban sani ba, tun yaushe nake cewa a kai ni
aka ki kaini,” ta karashe maganar da
matsanancin kuka ta jefar da wayar,
Inteesar da haushi ya cika ta tace “Anty ki
shigo mana,” ganin har lkcin Anty na tsaye
tana kallon inna, Anty tayi murmushi ta
shigo falon ta xauna, wayar inna ya shiga
ringin kursum ta mika mata tace Abba ne, a
fusace tace “share mara mutunci kawae,
uwar me xae gaya min, maxa kije ki kira
min Zainabu don uwarta ita ma” inteesar
kam kunya ne ya isheta kawae, da ta sani da
gun momy kawae ta tafi, inteesar ta
kwantar da yaron hannunta ta bude fridge
ta ciro ruwa da lemotunda sun karya a
lagos, ta ajiye ma Anty snn ta dauko kofi
mata ajiye mata, Anty tace “da kin bar shi
kawae inteesar, cikin yyimaki sauki ynxu
ko,” inna ta mike da sauri tace “cikinta ke
ciwo,” inteesar ta galla mata harara bata ce
komai ba, kursum ta shigo rike da wayar
momy tace “inna wae Abba xae maki
magana,” inna tace “da’alla ni a rabu dani
me xae ce min,” ta fixge wayar ta kara a
kunne tace “me xaka ce min Bukar,” wace
inteesar din kasani, ae ni sae Allah ya saka
min gata nn da yan biyunta sun xo da wata
doguwar mata fara me dogon hanci, yo ina
xan sani Bukar,” ta katse wayar ta ajiye, tana
kallon Kursum tace “baki ce ma Zainabu ina
kiranta bne,” kursum tace “tana xuwa,”
inteesar na kallon kursum tace”kursum
Abba fa,” inna tace “yace yana xuwa,”
inteesar ta daure fuska tace “tare da bako
muke a waje inna,” inna tace “toki shiga da
shi falon Abban naku,” inteesar ta mike ta
fita ta yi kofar gida tace “Abbanmu ku
shigo,” har falon Abba ta kai sa, Zainab na
biye da ita a baya, ta bude fridge ta ciro
masa lemo da ruwa ta ajiye masa da kofi, yyi
mata godiya snn ta kama hannun Zainab
suka fita daga falon, a sanyaye momy ke
tahowa daga bangarenta duk da kursum
tace mata inteesar ceta xo sae ta kasa yrda
bayan ga abinda Abba ya fada mata jiya,
suna hada ido da momynta ta ruga a guje ta
rungumeta cikin farin ciki, ji tayi kmr ta fi
shekara rabonta da ita, momy kasa cewa
komai tayi sae hawaye, hkn ya ba inteesar
mamaki jikinta yyi sanyi tace “momy me ya
faru,” momy ta kasa cewa komai sae kallon
Zainab da take, da kyar momy tace “wacece
wancan,” inteesar tace “parent dinta suka
dawo dani gida momy suna da kirki ssae,
momynta na falon inna, muje ki ganta”
momy bata ce komai ba suka yi bangaren
inna.
Suna shiga falon inna, inna ta fara ma
momy jaraba, “ynxu abinda kuka min kun
kyauta knn Zainabu,” Momy bata tanka inna
ba ta shiga gaida Anty, Anty ta amsa da
fara’arta, inna tace “magana nake maki
Zainabu,” Anty tace “mama bana tunanin
sun san da Haihuwar inteesar fa,” inna ta
galla mata harara tace “ya xaki ce min hka,
ke me kika sani,” Anty tayi murmushi tace
“to mu a india muka tsinci inteesar tana
nakuda sati biyu da suka wuce, a hannuna
inteesar ta haifa yaran nn, kuma bayan ta
dawo hankalinta na tambayeta gun wa taxo
a india, tace ita ma bata san wa ya kawota
ba, satin ta kusan biyu a gidanmu muka
maido da ita nan Nigeria da mai gidana,”
inna tayi tsaki tace “ni ban gane
shirmamman hausan nn naki ba, uwar wa
inteesar ta sani a india da xa ki ganta a can,
da ma lagos kika ce min, wnn karya kike yi”
sallamar Abba ne yasa inna yin shiru tace
“ka xo kaji min karyar bnxa Bukar wae a
india aka ga inteesar tana yawo,” Abba ya
shigo falon yana kallon inteesar da mamaki,
ya xauna ba tare da ya shirya ba ya sauke
wani ajiyar xuciya ya dafe kansa yace
“Alhmdllhi,” inna tace “ta me,” kasa ba inna
amsa yyi yana kallon Anty yace “baiwar
Allah a ina kuka ga wnn yarinyar don Allah,”
Anty tace “a new delhi ni da mai gidana
mun
fito daga wani plaza,” Abba yace “Allah
ubangiji ya taimake ku kuma kmr ynda kuka
taimakeni ya saka maku da alkhairi,” inna
tace “yau naga tsiya, wae me ke faruwa ne,”
Abba ya juya yana kallon inna yace “baaba
yau kusan wata uku knn Fateema bata cikin
hankalinta bamu gaya maki ba, mu ne har
india daga lgs nemo lafiyarta satinmu uku a
india aka nemeta aka rasa yau sati biyu da
kwanaki knn da muke nemanta a india……”
inna ta katse sa da sauri tace “kmr ya bata
cikin hankalinta, hauka take ko me,” Abba
yace “kwarae kuwa baaba amma wa ya
bamu karfin gwiwan xuwa mu gaya maki
wnn mummunan lbrin mara ddin ji , baaba
na shiga damuwar da ban taba shiga ba a
rayuwata, ynxu hka Aliyu na can a asibitin
shima ba hankalin tun bayan da muka nemi
fateema muka rasa, su Nafeesa da Haisam
ae duk suna can” tunda Abba ya fara
magana inteesar ta tsaya da mamaki tana
kallon Abba, wae ita ce tayi hauka, maganar
Abba ta karshe yasa ta hawaye, inna ta mike
jikinta na rawan bala’i tace “waye ya
haukatar min da jikata a gaya min don
bamu
gaji hauka a xuri’armu ba,” Abba ya sauke
ajiyar xuciya bae ce komai ba, kuka ssae
inteesar take, hka ma momy, Anty kam
jikinta yyi sanyi, don bata san a haukace
suka tsinci inteesar ba, kuma bata ga alamar
hkn ba, inna ta dinga ihu da kuka a gidan
wae a kaita gidansu safeena tasan baxae
wuce aikin asiri ba su suka mata asiri, Abba
ya mike bae bi ta kan inna ba ya fice a
xuciyarsa yana hamdalar bayyanar inteesar
da gaggawa hka, wae bayan komai ya lafa
inna ta sani amma dubi reactions dinta
yasan bae yi kuskuren rashin gaya mata da
bae yi ba, yana fita Nafeesa ya fara kira ya
sanar mata snn ya shiga falonsa ya tarar da
Abbanmu xaune yana kallon news, yace
“ashe bako gareni basu sanar da ni ba,” ya
bashi hannu suka gaisa snn ya shiga yi
masa gdya kafin yyi masa bayanin abinda
ya faru. Momy ta mike ta fita tayi
bangarenta ganin irin haukan da inna take
ba ji ba gani, Anty na bata hkuri, “ki kyaleni
nayi yarinya, a haukatar min da jika bata yi
masu komae ba, kuma nayi shiru, ae da
wani
abu ya sami inteesar a duniyar nn da kowa
kashinsa ya bushe a gidan nn, shi kuma
Aliyu ya karata da haukansa tun da shi ya
siyar ma kansa dama na sha gaya masa shi
mahaukaci ne,” ta karashe maganar tana
huci ta shige daki, inteesar dae sae kuka
take duk hnklinta na gun Aliyu da Abba yace
ke hauka sbda ita, Anty ta shiga hada ma
Hassan dake kuka abinci, inteesar ta mike ta
bi inna daki jikinta a sanyaye, katuwar