INTEESAR 4

tunkuyarta take kkrin fitowa da xata je
daura
ruwan wanka, inteesar na hawaye tace
“inna
don Allah kice ma Abba su barni na je gun
ya Aliyu tunda……” inna ta dakatar da ita a
fusace tace “kina danyan jegon xaki tafi gun
wani mahaukaci can,” inteesar ta fashe da
kuka tace “ni ki daina ce masa mahaukaci, ki
taimaka min kiyi ma Abba magana ” inna
tace “to baki isa ba don ubanki,” ta fice da
katuwar tukunyanta tana kwala ma kursum
kira ta siyo mata itace, inteesar ta xube kan
gado tana ci gaba da kuka, ta kai kusan awa
daya a hka taji ihun Husaini ta fito da gudu
ba tare da ta shirya ba, taga inna ce ke
masa wanka sae kunya ta kamata ynda ta
fito a rude, Anty tayi dariya tace “wanka ake
masa ba wani abu ba maman biyu,” inna ta
tabe baki tace “ki rabu da gantalalliya tana
danya da ita wae gun wancan mahaukacin
xata ya buge min ita a bnxa, shi fa ya janyo
ma kansa yar nn, wata shegiyar karuwar
mace me xubin kafurae ya auro suka dinga
walakanta min jikata sae ga shi wae har sun
haukatata ban sani ba, gashi ynxu Allah yyi
mata sakayya abunsu ya koma masu, ni dae
Alhmdllhi tunda jikata ta dawo lfya, miko
min tsummar can” inteesar ta juya ta koma
daki a sanyaye hawaye na bin kuncinta,
kursum ta shigo tana kallon inteesar tace
“Abba yace kije,”
.
….A hankali Inteesar tayi sallama ta shiga
falon Abba, ta xauna kasa tace “Abba gani”
Abba yace ta koma kan kujera, ta mike ta
xauna kan kujera tana kallon Abbanmu
dake ta bin ta da kallo, tayi murmushi ta
sunkuyar da kanta kasa, Abba yyi shiru snn
yace “ina yaran,” xata yi magana sae ga
kursum ta shigo rike da Hassan, Zainab na
biye da ita a baya rike da Hussain, duk Abba
ya amshesu yana kallonsu yana murmushi,
kmr ba jarirae ba suma idonsu kyar a kansa,
sae da ya tofa masu addua gaba daya snn
ya kwantar dasu kan kujera ita dae inteesar
kanta na kasa, Abba na kallon Abbanmu
yace “dota dinka knn ko Alhaji Umar ko,”
Abbanmu yyi murmushi yana kallon Zainab
yace “eh ita ce diyata ta farko,” Abba yyi
murmushi yace “Allah sarki sae naga suna
kama da inteesar,” Abbanmu yyi dariya yace
“hka ne kam,” kursum suka fita tare da
Zainab snn Abba yace “kina jina fateema,” ta
gyada masa kai yace “idan kin huta xaku
koma can india dasu Antynki amma fa sae
idan kina son komawa baxa mu takuraki ba,
nasan dae kina sane dae Aliyu bashi da lfya
ko,” kai kawae ta gyada masa tana hawaye,
Abba yace “ba kuka xakiyi ba, Addua xakiyi
masa,” a hankali tace “Abba ni na gama
hutawa mu tafi yau kawae,” Abbanmu yace
“yauwa fateema ashe kina da hankali gwara
kije gun mijinki tunda rashin ki ya jawo
masa wnn lalura,” bata ce komai ba Abba
yace “shknn fateema Allah yyi maki albarka,
amma ki bari gobe ku tafi sbda yaran nn kar
suyi xaxxabi je ki ki kira min momynki,” ta
mike ta fita daga falon, Abbanmu yace
“xanje gun wani abokina dake nn gadon
kaya,” Abba yace “to shknn Alhaji sae ka
dawo,” Abbanmu ya mike ya fita yana kiran
Anty a waya ya sanar da ita xae dan fita,
bayan fitarsa da minti biyar inteesar suka
shigo da momynta, Abba yyi mata bayanin
abinda suka tsara da Abbanmu kan cewa su
koma can india da inteesar gun Aliyu, momy
tace “hkn ma yyi, Allah dae ya basa lfya,”
Abba yace”Ameen don son Annabi,” inteesar
ta mike ta fita ta bar masu falon ta koma
falon inna, kmr ba jego take ba garau take
jin kanta, a bakin kofa ta tar da inna tana
masu lafiyayyan girki inna tace “Allah sarki
Aliyu, wae wani irin ciwo aka ce yake yi hka,
a dawo min da jikana gida kawae na nema
masa magani,”ko kallonta inteesar bata yi
ba ta shiga falo Anty ta sata gaba ta shanye
kunun da inna ta dama mata don har lkcn
bata yi wani break din kirki ba, kasa sukuni
tayi ranar Allah Allah take kawae gobe yyi ta
je ta ga Aliyu duk hnkalinta yyi gunsa,
momyce ta dawo da yaran daga gun Abba
suna kuka ta bai ma mamarsu su ta fita,
wajen karfe uku Anty ta tafi bangaren
momy inna kuma ta tafi nemo ganyen
darbejiya, inteesar nata fama da Hassan
dake ta yi mata rigima kursum na rike da
Hussaini, kursum tace “wae sunansu knn,”
inteesar tace “A’a ba a rada masu suna ba
har ynxu ae, wae ina su khadija” kursum
tace “khadija na gidan Zainab bata da lfya,
rahma kuma na can gidansu mamarmu”
inteesar tace “Allah sarki Zainab, Hajiya da
umma fa,” kursum tace “hajiya tayi tafiya,
umma kuma tana can gidansu Fadila ta kara
kashe aurenta, shine Abba yace su tafi su
bar masa gidansa,” inteesar tayi shiru da
mamaki tana kallon kursum, can tace
“yaushe hkn ya faru,” kursum tace “kusan
wata biyu knn, inna ce tace Abba ya koresu
ko ita ta bar masu gidan,” inteesar bata
sake cewa komai ba amma ko kadan bata
jin ddin abinda inna ke yi, fira suka dinga yi
da kursum har inna ta dawo duk ta hada
xufa da darbejiyarta tace “da kyar na samo
wnn, maxa ki tube ki shiga bayi ki jira ni na
juyo ruwan,” inteesar ta mike da sauri tace
“ke dawa, wllh baxa kiyi min wanka ba da
girmana kuma da wnn abun, to wae ca nayi
maki banyi wanka bne,” inna tace “yau naga
tsiya, har wani wanka kike yi dubi ynda kike
tafiya kmr wata rubabbiya, wa ya sani ma
ko da ruwan sanyi ake maki wanka a can”
ko kallonta inteesar bata yi ba ta fice daga
falon tayi gun momynta. Washegari har
airport Abba ya kai su a motarsa aka bar
Zainab gun momy don xasu dawo, inteesar
bata ji ddin rashin fitowar da momy tayi ta
rakasu ba, basu samu jirgin da xae je india
ranar ba a Aminu kano don hka sae da suka
fara xuwa lgs snn suka kama hanyar india
.. Da yamma inteesar da Abbanmu suka
kama hanyar asibitin da Aliyu yake bayan
sun huta can gida, a motar Abbanmu suke
tafiyar sae bin ko ina take da kallo india yyi
mata kyau ssae, Anty na gida da yan biyu
don xaxxabi ssae suke tun bayan saukansu
da safe, suna isa asibitin gaban inteesar ya
shiga faduwa suka yi parkin, suka fito
Abbanmu ya shiga kiran Anty Nafeesa kmr
ynda Abba yace masu, ta fito da sauri ta
rungume inteesar tana hawayen murna ita
ma kukan ta fara yi, a hka ta jata suka shiga
asibitin, Inteesar taje da gudu ta rungume
Haisam da hawaye ya cika idonsa ganinta ya
ma rasa me xae ce, da kyar ya iya cewa “ina
yaran inteesar,” ta goge hawayen fuskarta
tace “suna gun Antyna,” ido hudu suka yi da
Hajiya dake rabe wani lungu kmr marainiya
Hajiya ta taso tana hawaye ssae ta rungume
inteesar ta kasa cewa komai, kuka ssae
inteesar take, murya na rawa Hajiya tace “ki
yafe mani inteesar ba don halina ba,” kasa
cewa komai inteesar tayi sae gyada mata
kai take, Haisam ya gaida Abbanmu dake
tsaye, hka ma Anty Nafeesa da Hajiya duk da
basu sansa ba suka basa kujera ya xauna,
inteesar sae kalle kalle take, taji ba a ce mata
komai kan Aliyu ba, cire kunya tayi tana
kallon Haisam a hankali tace “ya Haisam, ya
Aliyu fa,” ya dan yi shiru snn yace “xaki
gansa akwae likita a dakin ne ynxu,” ta
gyada masa kai jikinta a sanyaye, Anty
nafeesa tace “ina yaran inteesar, Abba yace
da su kuka taho” inteesar tace “suna gun
Antyna a can gida,” bbu wanda ya sake
cewa komai cikinsu har likitan dake dakin
ya fito, Haisam ya mike ya bisa da turanci
yake tambayarsa xa a iya shiga a gansa,
likitan yace xa a iya shiga amma kar wanda
yaje kusa da shi,” inteesar ta mike da sauri
gabanta na faduwa nn da nn hawaye ya
cika idonta, tayi hanyar kofar Haisam ya
dakatar da ita, da kyar ta juyo tana kallonsa,
Haisam ya karasa yace ta koma baya, ba dan