INTEESAR 4

ja motar suka fita daga gidan, har suka isa
gida bae ce mata ba ita ma bata ce masa ba,
gabanta ya shiga faduwa don bata san me
xata shiga ta tarar ba, da kyar jikinta a mace
ta fito daga motar ta jira shima ya fito, bae
ko kalleta ba ya nufi gate xuciyarta na
harbawa da sauri da sauri ta bi bayansa
suna shiga gidan falon abba taga ya nufa,
ita dae tana ta biye da shi a baya kmr jela, a
bakin kofar Abba suka ci karo da momy
xata fito daga falon, inteesar ta koma baya
da sauri kuma a tsorace, momy ta bi ta ta
cafketa, ihu ta fasa a tsorace momy ta shiga
xuba mata mari tana duka kmr an aikota,
kuka ta dinga rusawa tana ihu a gidan Abba
ya fito da sauri yana kallon momy a fusace
yace “kina da hankali kuwa Zainab, meye
hka kike yi,” ko kallonsa bata yi ba sae
jibgarta take tana tumble da ita, ita ko bata
fasa ihu da kukan da take ba, Aliyu ya dauke
kansa ya koma gefe ya tsaya ya lumshe
idonsa, su Hajiya da umma duk suka fiffito
daga dakunansu su Rahma duk sun tafi sch,
duk irin masifar da Abba ya dinga yi ma
momy ransa a bace kan ta sake inteesar kin
sakinta tayi, har sae da ta kai ta kasa, su
Hajiya da umma dae na tsaye sae murmushi
suke, Hajiya na cewa “to wnn abu dae idan
bakintsa mata aka yi ba taya yar mitsitsiyar
nn tasan wani cire ciki” daga nisa suka ji
Muryar inna tana tahowa da gudu tana
cewa “muryar waye nake ji hka kmr ta
Inteesar uban me ake mata,” ta karaso tana
haki, tana ganin abinda momy ke yi ma
inteesar tayo waje da ido ta fasa ihu “meye
hka xan gani Zainabu, akuya kika samu ko
me? kashemin ita xakiyi don uwarki,” sae a
snn momy ta saketa, inna ta fashe da kuka
tana kallonsu gaba daya tace “amma dae
Allah ya isa ban yafe maku ba, ynxu Bukar
har da kai aka taru xa a kashe yar mala’ikan
Allahn nn don ta xubar da wani wahalallen
cikin Aliyu dake neman aikata lahira, to duk
shegen da bae fasa dukanta ba bae haifu
cikin uwarsa ba ” ta dago inteesar dake ta
rusa kuka ita ma tana nata kukan ssae tace
“Allah ya isar maki kuma ciki kin isa ne yasa
kika xubar da shi, mu je ga ruwa can na
daura xan maki wanka” taja ta tana dingishi
suka yi sashinta tana huci, Aliyu ya juya yana
kallon Abbansa da ya bi su da kallo shima,
snn ya girgixa kai kmr xae hadiye xuciya yyi
hanyar fita daga gidan Abba ya kirasa. Allah
sarki Babana Aliyu, but ol d same Allah shi
kara, na ma tuna ko waye kai da.
.
Inteesar na xaune falon inna
tana cin tuwa da lafiyayyan miyan vegetable
da inna tayi mata yaji
nama da kifi da ganda, sae tura abunta take,
ga farfesun kayan ciki
da na kai gabanta ga fura mae sanyi shima
duk a gabanta, inna ko
na xaune gefenta tana tayi mata hira tana
kyalkyala dariya, inteesar
dae hankalinta na kan abincinta har ta
manta rabon da ta ci tuwo
sae indomie kmr mayya kullum, tun safe da
inna ta ja ta tayo sashin
ta da ita bbu wanda yaga fuskar xuwa ya
samesu har Abba, Aliyu
kam Abba ne ya hanasa xuwa don yasan
halinsa, Haisam ma baram
baram suka yi da inna daga yaxo yi ma
inteesar fada, ransa a bace
ya bar falon, sallamar faruuq yasa inteesar
ta jawo hijabinta da sauri
don daga ita sae yar shimi, suka amsa masa
sallaman inna na washe
baki ya nemi guri ya xauna ya gaida inna ta
amsa cike da jin ddi ta
mike ta kwaso masa lemo a fridge dinta,
inteesar ta gaishesa tana
murmushi ya amsa ba tare da ya kalleta ba,
tace “ya faruuq Zainab
fa?” yace “tana lfya,” ta ci gaba da cin
tuwonta inna nata yi masa
hira mara tushe sae binta yake da uhm, sae
da ya jira don kanta tayi
shiru snn ya hade rae yana kallon inteesar
yace “inteesar wajen ki
naxo,” ta dago tana kallonsa hka ma inna,
yace “am vry disappointed
in yhu inteesar, never knew yhu 2 b
foolish….” da sauri inna tace
“meye wnn kke cewa, ka fada wanda xanji
mana,” ya juya yana kallon
inna yace “Haba inna, ynxu abinda inteesar
tayi ta kyauta knn da ba
ki son a mata fada, rae biyu fa ta hallaka dan
wauta irin nata, kuma
ace baxa a mata magana ba” a fusace ya
karasa maganar, inna ta
dafe kirji kmr xata yi kuka tace “rae biyu fa
kace, dama yan biyu ne
knn?” faruuq yace “au ke da duk abinda ake
baki sani ba inna,” inna
tayi narai narai da ido tace “ni ina nasani,
ynxu yan biyu ta xubar
faruuq, ko daya bae rage ba,” ta juya tana
kallon inteesar dake ta
tura tuwanta abunta fuskarta a daure, can
ta juyo tana kallonsa tace
“to hka Allah ya kaddara sae a dau na
annabi, yarinya dae bata gama
mallakar hankalinta ba bare ace xa a mata
fada ynxu, kawae sae dae
ace Allah shi kyauta, su kuma Allah ya ji
kansu,” faruuq don takaici
kasa cewa komai yyi, can dae yace “meyasa
xaki dinga cewa hka
inna, inteesar din ce yarinya ynxu,” inna ta
hade rae tana kallonsa
tace “naga dae alamar kaima ka fara xama
munafuki, tashi ka ban
waje idan har wnn maganar ce ta kawo ka,
to jefar da ita kuke son
nayi kome, dama Allah yyi yaran baxa su
wuce wata uku a cikinta ba,
don hka ku shafa ma jikata lfya” faruuq ya
mike ransa a bace yace
“to inna, Allah ya baki Hkuri ni xan koma,”
tace “eh Allah ya kiyaye,”
ya juya ya fice daga falon, inna ta ja dogon
tsaki tace “munafukan
bnxa kawae, ci ki koshi kije ki kwanta ina
fatan dae jinin ya tsaya
gaba daya ynxu.” Da daddare inteesar na
kwance gefen inna duk da
fankan dake aiki a falon tana tayi mata fiffita
suna hira, Abba yyi
sallama, inteesar ta mike xaune da sauri
tana kallon inna, inna tace
“tsaya tsaya kar ka shigo min,” ta juya tana
kallon inteesar murya
kasa kasa tace “maxa tashi ki shiga daki,” da
gudu inteesar ta shige
daki ta rufe kofa, inna ta rungume
hannuwanta tana sakace hakori
tace “yauwa xaka iya shigowa” Abba ya
shigo dakin da sallamarsa ya
xauna ya gaidata yana kallonta, ta amsa bbu
yabo ba fallasa, yyi
shiru na kusan minti biyar snn yace “baaba
fateema fa” inna ta hade
rae tana kallonsa tace “ya aka yi,” cikin fada
Abba ya fara magana
“haba baaba, ni ynxu kina gwada ma yaran
nn bani da iko da su ne
kome, ya yarinya tayi laifi irin wnn nasa a
kawo min ita gida ki
kunshe ta a daki bbu wani bayani, kuma ke
ba yi mata xaki yi ba,
ynxu kina gwada mata abinda tayi tayi dai
dai knn kome,” inna ta
marairaice ganin yanda ransa ya baci tace
“to wae Bukar maganar nn
bata wuce bane ko me, naga dae ya ya ba
dawowa xasuyi ba,” Abba
ya shiga kiran inteesar a fusace “fateema
fateema,” kmr munafuka ta
fito da hijab har kasa, inna se ca take baxata
fito ba koma inteesar,
Abba yace “maxa ki wuce falona ki jira ni,” a
fusace yyi maganar don
hka bata saurari inna ba ta fice kmr
munafuka gabanta na faduwa,
inna tace “to wllh sae na bi ku,” bae tanka ta
ba ya fice, ta fixgi
gyalenta da sauri ta fice ta bi bayansu,
gaban inteesar yyi mugun
faduwa ganin su Hajiya da ma momynta har
ma da Anty nafeesa da
ta bi ta da harara a falon ashe ta xo gidan,
ko inna ma bata sani ba,
inteesar ta saci kallon Aliyu dake xaune
gefen Haisam, ta rasa inda
xata xauna don kowa haushinta yake ji a
falon, Abba ya shigo ya
xauna yana kallonta ta sunkuyar da kanta
har lkcn tana tsaye, cikin
ikon Allah sae ga inna ta shigo falon tana
haki, tana kallon Hajiya
tace “ke tashi ki ban waje in xauna,” Hajiya
bata yi musu ba amma in
ranta yyi dubu ya bace, ta mike inna ta
xauna tace “xo xauna nn
inteesar,” inteesar ta xauna gefen inna,
Hajiya kuma ta nemi wani
wajen ta xauna ranta a bace. Inteesar ta
daga kai a hankali ta saci
kallon Aliyu taga kallonta yake, duk ya koma