INTEESAR 4

kmr wani mara lfya, ta
dauke kanta da sauri shima hka
.
A nutse Abba ya kira sunanta “fateemah,” ta
dago a hankali tana kallonsa, ya sauke ajiyar
xuciya yace “ko da yake ma bari na fara ta
kanki baaba,” inna na kallonsa tace “eh ina
ji,” yana kallonta yace “Baaba kar ki fara
magana nn ba tare da ance kiyi ba, duk me
xaki ji a nn don Allah karki bude bakin ki,
idan ana bukatar cewar ki xa’a sanar da ke,
don Allah dae nace,” inna ta tabe baki tana
girgixa kafa, ya maida dubansa ga Inteesar
da ta sunkuyar da kanta yace “fateema,”
wnn karan kasa dagowa ta kallesa tayi, bae
damu ba ya ci gaba “Ashe ke dama mara
hankali ce bansani ba,” inna tayi karaf tace
“kmr yaya,” Abba ya hade rae yana kallonta,
ta daga hannu da sauri tace “to nayi shiru,”
Abba na kallon Inteesar yace “ynxu abinda
nake so dake shine kawae ki gaya min
asibitin da kika je,” Hawaye ya cika idonta ta
kasa cewa komai, cikin daga murya Abba
yace “ba magana nake maki ba,” a hankali
Aliyu yace “ae Safeena ce tayi mata jagora
wae,” a fusace inna tace “ga magana nn
xaku tsaya kuna wani lauyewa, ni dae nasan
jikata baxata iya aikata wnn danyan aikin da
kanta ba” Abba yyi shiru yana kallon Aliyu
snn yace “kae wa yaga maka hka,” Aliyu
yace “ita da bakinta ta fada,” inteesar ta
watsa masa harara tace “ni ba muyi hka da
kai ba, kuma safeena bata yi min ko wani
jagora ba ni da kaina na tafi inda naje,
hasalima bata sani ba,” Aliyu ya yo waje da
ido da mamaki yace “kika ce me?” ta xaro
masa ido tace “ehh” ya dafe kansa yace
“innalillahi wa inna ilaihi raji un, kika sa naje
na ba yar mutane takarda ashe sharri kika
mata” Abba yace “takardar ka kai mata?”
Aliyu ya kasa cewa komai sae kallon inteesar
da yake, a rude Hajiya tace “kana da hankali
kuwa Aliyu, ka saketa fa kace?” Abba yace
“saki nawa kayi mata,” Aliyu ya sauke ajiyar
xuciya yace “daya,” snn ya ciro pen daga
Aljihunsa ya mike ya shiga dakin Abbansa
duk aka bi sa da kallo ya fito rike da farar
takarda ya isa study desk ya duka xae yi
rubutu Abba yace “meye hka kke yi Ali,” ya
dago bbu yabo bbu fallasa yace “ita ma
rubuta mata nata xanyi Abba” Abba ya daka
masa tsawa “kana da hankali kuwa, a
gabana don baka da kunya xaka dauko
takarda kana gaya min maganar bnxa,”
cikin daga murya Abba yace “dawo nn ka
xauna,” Hajiya tace “kambu, ae wlh baka isa
ba Alhaji, ita wancan din da ya saka ance
maka gata ne bata da, ae ita ma Wllh sae ya
rubuta mata nata, na rantse,” Abba ya mike
a fusace yace “fice min a falo Aisha, nace ki
fita,” ta mike tace “ae ko baka fada ba fita
xanyi, amma wllh kmr yanda tayi makirci
tasa ya saki matarsa ta arxiki ita ma sae ya
saketa, ae dama idan bata xama makira ba
sae Allah ma ya tambayeta, abu a jini,” ta fice
tana huci, inna tace “shegiya yar wahala, ae
in Aliyu ya saki Inteesar yau duk kuma sae
nasa dana ya rubuta maku takardarku wllh
wllh,” inteesar ta fashe da kuka tace “Abba
ni ka bar shi ya rubuta min takardata don
Allah don Annabi,” Abba ya daka mata tsawa
a fusace “rufe min baki, stupid” Anty
Nafeesa kam kasa cewa komai tayi sae
kallon inteesar take, momy dama hankalinta
na kan TV, Abba yyi shiru na wani dan lkci
snn yana kallon Aliyu yace “sae kaje ka
mayar da matarka,” Aliyu bae ce komai ba
sae da har lkcin kansa a kasa yake da
ganinsa kasan ran maxa ya baci, Abba ya
hade rae yana kallon inteesar yace “ynxu
dalilin cire cikin jikinki kawae nake son ki
gaya mana gaba daya mu ji,” hawaye ya cika
idon Inteesar tayi shiru kanta a kasa, har
sae da Haisam ya daka mata tsawa, “ba
magana ake maki ba,” a fusace inna ta mike
tace “ohh ni yau naga tsiya xasu kashe min
jika, kuma sun hanani magana ” ta fashe da
kuka xata bar falon, Abba yace “haba baaba
ki dawo muji daliin da yasa tayi hka, ae bbu
wanda yyi mata wani abun a nn,” da kyar
aka lallaba inna ta dawo ta xauna tana
share hawaye, Abba yace “muna jin ki
Fateema,” inteesar ta dago kanta a hankali
tana kallon Aliyun, taga shima kallonta yake,
ta kauda kanta tace “sbda bana sonsa
shima kuma baya sona yasa nayi hkn Abba,”
ta fashe masu da kuka ssae tace “Abba
tunda na taso ya Aliyu ke cutata a gidan nn,
tun ban san kaina ba, ban san me nayi masa
ba ko dan ba gidan ubana bne, ya tsaneni
kuma baya son bude ido ya gan ni cikin
gidansu, ko uwar da ta haifeni ma bae bari
ba, idan an manta randa ya daga hannu xae
mareta to ni ban manta ba, kuma har gobe
baxan manta ba, ban san me muka yi masa
ba, duka bbu wanda ban sha a hannun
Aliyu ba, idan ba a manta ba wani rashin
lfya da nayi na kwana da kwanaki shi shine
sanadin sa, amma ban fada ma kowa ba,
har ka hada mu aure Abba, kuma tunda ka
hada mu abba ko sau daya ban taba jin
ddin xaman gidansa ba, sae nayi sati biyu
ban daura idona a kansa ba, bae san ci na
ba bae san sha na ba, kullum a wahale nake
cikin gidan, to a hka yake son na haifa masa
yara, wllh Abba bana sonsa ka taimakeni
kasa ya bani takardata ynxun nn, biyayya
kawae yyi maka yake xaune da ni gida daya
a matsayin matarsa,” ta fashe da
matsanancin kuka takasa ci gaba, tun da ta
fara magana Aliyu ke kallonta baki bude.
Ganin bbu wanda ya iya cewa komai a falon don duk jikinsu yyi sanyi ya sa inteesar ta tsagaita
kukan
da take ta cigaba “snn Abba ni bada
yardana ya
sake aure ba, hasalima ni ban san xae yi
aure ba
sae ranar da ya kawo ni gunka da daddare
kke
tambayata ko nasani, to a nn ne ma nasan
aure
xae yi, kuma dama tun a hanya yyi threatn
dina
kan cewar ko me xaka tambayeni nace
nasani,
kuma Abba har yau yaki daukar batun
karatuna
da muhimmanci da nayi magana sae ya
dinga
hantarata wae baxan iya course din da nace
nake so ba, kuma Abba da yake cewa na
xubar
masa da ciki a tambayesa ko kula dani da
cikin
yake, Abba sae nayi kwana uku ban gansa
ba
gashi bbu abinda nake iyawa kullum a
wahale
nake kwana nake yini a gidan ga kuma
yunwa,
tunda ba iya girkin nake ba,” tayi shiru tana
share
hawayenta snn a hankali tace “lastly Abba
kayi
hakuri ba rashin kunya nake maka ba,
amma ka
tausaya min kayi masa magana ya sauwaka
min,
don baxan koma gidansa ba wllh na gama
aurensa,” Aliyu ya mike yana mata wani
mugun
kallo yana huci yace “munafuka,
makaryaciya
kawae, ki xo ki shake ni na baki takardar
taki
kuma wllh sae kinyi da kin sanin xubar min
da
ciki,” ya juya xae bar falon Abba ya dakatar
da
shi a fusace, inteesar ta fashe da kuka tace
“wllh Abba kace ya bani takardata bana
auren
kuma, bana sonsa,” Abba yana kallon Aliyu
yace
“dawo ka xauna,” ya kai minti kusan biyar a
tsaye kmr baxae xauna ba, sae da Anty
Nafeesa
tace “ba magana ake maka ba ka tsaya ma
mutane kallon rainin wayo,” ya juya ya
kalleta,
snn ya koma inda yake ya xauna yana ma
inteesar wani irin kallon, da ganinsa kasan
ran
maxa ya gama bacewa, Abba yace “cikin
maganganun da Fateema tayi a nn akwae
wanda
xaka karyata,” ya kauda kansa bae ce komai
ba
sae huci da yake, Abba yace “gud, dama tun
ba
yau ba nasan halinka, na kuma san xaka iya
aikata duk abinda fateema ta lissafo a nn,
kai
kam ban san wani irin mutum bne Aliyu,
kuma
gwara da Fateema ta gaya min abubuwan
da ta
dde tana boyewa a cikinta tana cutar
kanta,” ya
juya yana kallon Inteesar yace “amma
fateema
ke abinda kika aikata a ganin kinyi dai dai
knn,
me xaki ce ma mahaliccinki, ashe dama
karamin
tunani gare ki ban sani ba” inteesar dai
kanta na
kasa tana hawaye ta kasa cewa komai, Abba