INTEESAR 4

kam ji tayi kmr ta hadiye xuciya don takaici,
a fusace inna tace “ya hka ina magana kin
tsaya kmr wata sokuwa, ki fita ki mika masa
mana,” sum sum Hjiya ta karasa gate ta
mika ma mai keke napep dari biyar din
ranta
a bace, ta komo cikin gidan, inna ta juya tayi
gaba ba tare da tace mata komai ba,
ummata shige daki ta dinga kyalkyala
dariya, inna
na komawa falonta tace “shegu sun ba
shi,A’aah jinin meye wnn a xanin ki
inteesar” arude tayi tambayar ta karaso
kusa da
inteesar da sauri tana gwale ido.
Inteesar ta juya da sauri
tana kallon xaninta taga duk ya baci da jini,
inna ta saka salati kmr
xata yi kuka xata yi magana inteesar ta riga
ta da sauri tace “al’ada
ce ta xo min a hanya,” inna tace “haba,”
inteesar ta gyada mata kai
kawae, inna tace “to Alhmdllh, ciki kam sae
dae lbri tunda ga al’ada
har ta xo, ynxu Haisam ya dawo ya raka ki
kuje ayi maki wankin ciki,
don naga bbu shegen da ya damu da hka a
gidan tunda ba lfyarsu
bace,” inteesar ta kuma juya mata baya don
ita kadae tasan yanda
take ji a jikinta,” inna tace “to wae ina
kayayyakin naki,” ba tare da
ta kalli inna ba tace “ba kowa a gidan,” inna
tace “shegu, to ki tashi
kije ki gyara jikinki mana kin wani kwanta
kaman rubabbiya ko
gantalallen can ya koya maki kaxanta ne, ni
dae ban san ki da
kaxanta ba sae dae in gunsa kika koyo”,
inteesar ta juya da sauri
tana kallonta tace “kema dae kinsan sharri
kawae xaki masa amma
ya Aliyu karshe ne wajen tsafta,” inna ta
wage baki tana kallonta,
inteesar ta mike da sauri ta shiga daki don
ita ma sae taji xancen yyi
mata wani iri a baki to ina ruwanta ma da
har xata wani kare masa,
wanka ta shiga bayi tayi taga jinin ya tsaya,
ta hada ruwan xafi tayi
wankan snn ta fito ta shirya cikin gown, har
ta kwanta abinda ya
faru daxu ya fado mata, ta lumshe idonta,
can ta mike xaune da
sauri tana kallon bakin kofa tace “inna ina
kika ajiye takardar daxu
da safe?” inna dake ta goge goge a falo tace
“oho kaman yana cikin
durowa, me xakiyi da shi,” inteesar bata
tanka ta ba ta mike ta bude
drawern ta dauko takardar ta koma ta
kwanta, ta dan lumshe ido ta
bude snn ta bude takardar tana kallon
cntent dinsa “Ni Aliyu ynxu na
fara aurenki Fateema, ke din bnxa baki isa
kice na sake ki ba tare da
na sa kaina ba, amma fa ban tilasta ki dole
sae kin dawo gidana ba
kiyi ta xama a gidanku don baki da amfani a
gu na dake da rashinki
duk daya ne a gurina, kuma muna nn da
knki xaki kwaso
kafafuwarki ki xo ki same ni, wawiya kawae
Jahila,” inteesar ta dafe
kanta hawaye ya cika idonta “Allah ya isa
bata yafe masa ba
kusantarta da yyi daxu, ita da tasan abinda
ke takardar nn da
baxata fara xuwa gidansa ba, ta fada kan
gado tana hawayen
takaici, ita ko xata yi maganinsa. Aliyu na
fitowa daga bathroom ya
nemi Inteesar ya rasa duk ya rikice
hankalinsa yyi mugun tashi,
Allah dae yasa yarinyar nn ba gida ta wuce
ba, abinda ya fada knn a
xuciyarsa, yyi sllh da kyar snn ya shirya cikin
three qtr da fara shirt
ya dauki makullin motarsa ya fita daga
gidan, karfe shidda ya isa
gida, ya tarda mum dinsa a tsakar gida
xaune da umma, ya xauna
kan wani dan dakali ya gaishesu, Hajiya tace
“son yana ga duk ka
rame baka da lfya ne,” ya dan sauke ajiyar
xuciya yace “lfyata lau,”
umma tace “to ynxu me ka xo yi gida kai da
sae muyi wata bamu
ganka ba,” Hajiya tace “shi dae na gani,
daga ina kke ynxu,” ya mike
yana ma umma wani irin kallo yace “don
naxo gidan ubana shine
laifi,” bae jira me xasu ce ba ya dan yi tsaki
yyi sashinsa, khadija ya
kira a waya ta shigo sashin nasa yace
“khadee yarinyar nn ta xo
gidan nn?” khadija ta dan tabe baki tace
“ehh ae dama tana nn, ynxu
ma inna ta kira ya Haisam wae ya xo ya
rakata asibiti ayi mata
wankin ciki,” ya yo waje da ido ya mike
tsaye da sauri yace “wani
cikin, ina Haisam din,” khadija tace “ae bae
dawo ba,” ya girgixa kai
cikin tashin hnkli yace “tafi kawae,” ta juya
ta fice, baya san mum
dinsa ta xargi komai shiyasa bae nufi
bangaren inna ba ya shiga
nasa, ya dan leko ko suna nn, yaga kuwa
suna nn xaune har lkcn,
yyi tsaki ya koma. Sae da aka kira Maghrib
snn duk suka shiga
sashinsu, yyi alwala ya fito ya tafi masallaci,
bakwae da kusan
kwata ya shigo gidan ya nufi bangaren
inna, a hanya suka hadu da
Momyn Inteesar ya kauda kansa da sauri
kmr baxae gaisheta ba har
ta wucesa snn yace “ina yini,” bata ko kalli
inda yake ba bare yasa
ran xata amsa, yyi murmushi ya isa kofar
falon inna xae yi sallama
ya fasa, ya je kusa da window yana lekan
falon, inna na xaune tana
dama fura tana ta xuba da kursum dake
kwance tana karatun Novel,
inteesar kuma ta fito daga daki knn ta
durkusa kusa da inna tace
“inna xuge min xip,” inna tace “yau naga
jaraba, me kuma xakiyi ba
daxun nn kika yi wanka ba,” inteesar tace
“ni dae ki xuge min,” inna
ta tabe baki ta xuge mata, inteesar kam sae
bin falon take da kallo,
wayar kursum yyi kara ta mike tace “inna
sae da safe,” ta fice daga
falon saurayinta ne ya kirata, inna ta tabe
baki tace “wnn
mummunan saurayin naki me shegen rowa
da baya shigowa gaida
mutane,” ihu suka ji kursum ta kwala ganin
Aliyu da tayi jikin
window ya galla mata mugun harara ya
daura yatsunsa a labbensa
alamar tayi shiru, da sauri inna tace
“menene” kursum tace “mage
na gani,” snn tayi gaba da saurinta. Inteesar
ta mike bayan inna ta
xuge mata xip din ta cire doguwar rigan
jikinta ya rage daga ita sae
undies, inna tace “bokiti na waje kisa hijabi
ki dauka, da na ce
kursum ta shigo maki da shi, inteesar ta sa
Hijab dinta ta nufi bakin
kofar xata je dauko bokiti
.
.Inteesar na kaiwa bakin kofa tayi still kmr
me tunanin abu, inna tace “me ya faru,” bata
dae ce mata komai ba amma ita kamshin
turaren Aliyu take ji kuma ssae, to duk
yanda aka yi yana tahowa ne, hkn yasa ta ki
fita, shikam kallonta kawae yake yana
murmushi ya gane me yasa ta tsaya, ya
karaso bakin kofa cikin sanda ya bude kofar
da sauri ya fixgota ya fito da ita, ta fasa ihu
a tsorace hka ma inna da tayi waje da gudu
ita ma, tana cewa”na shiga uku waye wnn,”
janta ya shiga yi tana nokewa cikin kuka
tace “wayyo inna kice ya kyaleni,” inna ta
shiga binsu da gudu tana cewa”lahh yau
naga iskanci ina xaka kai min ita don
uwarka, Bukar Bukar,” ganin inna tara masa
jama’argidan kawae xata yi a tsakar gida
yasa ya sake ta tun kan su karaso tsakar
gidan, ta karasa gun inna da gudu tana
kuka, inna na nunasa da dan yatsa tana
kakkane ido tace”Aliyu ka fita harkata Aliyu
ka fita harkata, wae shin ni kakar kace xaka
dinga wasa da hankalina hka ko yaya ne,”
ya harareta ya xo ya wucesu yyi bangarenta,
cikin daga murya tace “Wllh tllh kar ka
shigar min falo, xan fa tara maka jama’ar
anguwar nn da daddaren nn,” dariya kawae
yyi ya shige falonta abunsa, inna tace “maxa
je ki falon Zainabu kiyi xamanki,” inteesar ta
make kafada tace “ni baxan je ba,” inna tace
“to mu xaunamu jira ubansa a nn,” jikin
wani flower ta ja ta suka xauna wae suna
jiran Abba, Haisam ya shigo gidan yana
kallonsu da mamaki yace “me kuke yi a nn
inna,” tace “yo wancan katon bnxan ne ya
shigo mana falo ba dole mu fito mu bar
masa ba, Bukar nake jira yaxo ya fidda min
shi,” Haisam yyi dariyar takaici yyi
bangarensa kawae
.
A wani cafe taga Haisam yyi parkin, tace “ya
Haisam me xa muyi a nn,” ba tare da ya
tanka mata ba ya bude mota ya fita ita ma ta
fito, sae da suka shiga cafe din snn yace “ko