HAUSA NOVELINTEESAR 4

INTEESAR 4

baxa kiyi post utme bne,” tace “ohh na

manta, a nn xamuyi registration din” yace

“ehh,” nn suka gama komai cikin minti

ashirin snn suka tafi banki ta jirasa a mota

ya biya kudin registratn din ya fito, taga sun

kama hanyar gida, a hankali tace “ya Haisam

asibitin fa,” bae kulata ba ya ci gaba da

tukinsa har suka isa gida, ranta yyi mugun

baci, yana gama parkin ta bude mota tayi

cikin gida, ya bita da kallo ya girgixakansa

lallai Inteesar ta girma, tana shiga falon inna

inna tace “ya har kun dawo, amma abun ba

wuya, amma bbu xafi inji dae,” inteesar ta

xauna ta rungume hannayenta fuskarta a

tamke tace “kokai ni ma yyi,” inna tace

“sbda me, ina kuka je to,” inteesar ta tabe

baki tace “wae wani registratn ya kai ni,”

inna tace “kyaleni da shi,” snn ta mike ta fice

a fusace tayi bangarensa, ranta a bace ta

dawo tace “ki rabu da yan iska so kawae

suke ki mutu da dattin ya ya a cikin ki, yara

duk sun bi sun rainani don ina wasa da su,

ki rabu dasu kawae gobe da sassafe xan

rakaki muje a wanke maki, tunda dae ni ba

nakasashiya bace bare wani ya kawo min

rainin wayo don na aikesa. Washegari da

safe Abba ya aiki kursum ta kira masa

Inteesar, inna tace “me xata yi masa da

sassafe hka,” inteesar da gabanta ya fadi

tana kallon kursum tace “ni kuwa,” kursum

tayi tsaki tace “ni,” snn ta fice, inna tace

“maxa saka hijabi muje,” inteesar ta dauki

Hijab dinta inna na biye da ita a baya suka

kama hanyar falon Abba, suna shigowa

Abba ya hade rae ganin inna a bayanta, inna

ta shigo falon ta hakikince kan kujera

tace”kace a kira maka Inteesar Bukar, ga ta

nn” Abba yace “to fisabilillahi baaba don

nace a kira min ita sae ki biyo ta, wae

meyasa kike yin hka ne baaba,” inna ta mike

ta marairaice tace”Allah ya baka hkuri,” snn

ta fice daga falon kmr xa tayi kuka, yyi tsaki

yana kallon inteesar yace “daga yau bana

son kina kwana a bangaren inna, kina ji na,”

ta sunkuyar da kanta ta kasa cewa komai,

ganin yy shiru yasa ta gaishesa a sanyaye,

ya amsa snn yace “fateema kinje walakanta

abinda Allah ya baki sae ga shi kuma ya

nuna maki ishara, nakan yi mmkin

sauyawan ki lkci guda Fateema, ynxu abinda

nake so dake shine ki koma gun ummar ki

ki xauna bana son xaman ki tare da inna,

snn wani asibiti da take cewa xata kai ki kar

ki kuskura don ciki na nn jikin ki,” inteesar

ta dago a sanyaye tana kallon Abba gabanta

na faduwa, hawaye ya cika idonta, wani

cikin kuma bayan ta xubar, Abba ya katse

mata tunani ta hanyar cewa “jiya Aliyu ya

shigo ya sameni ya kuma badahkuri akan

yana son ki koma dakin ki, though ban

nuna masa na amince da hkn ba don ina

son na fara jin ta bakin ki, kina sha’awan

komawa dakin ki?” inteesar ta share

hawayen da ya gangaro mata tace “Abba

don Allah don Annabi ka sa shi ya sallameni,

ni bana son auren kuma ka yi mani adalci

abba,” Abba yyi shiru yana kallonta snn yace

“to kiyi hkuri ki bari har sae kin sauka lfya,

na maki alkawarin xan sa ya baki takardarki

ko yaki ko yaso,” muryarta na rawa tace

“ngdd Abba,” Abba yace “kya iya tafi amma

bana son xaman ki tare da inna, ki koma

gun ummanki ynxun nn kuma,” kai kawae

ta gyada masa ta mike xata fita, Aliyu yyi

sallamaya shigo falon, ta hade rae ta bi ta

gefensa ta fice, ya bi ta da kallo snn ya

xauna inda ta tashi, ya gaida Abbansa, Abba

ya amsa yana duba newspaper, yyi shiru na

dan lkci snn a hankali yace “Abba kayi mata

magana,” Abba ya dago yana masa mugun

kallo yace”wani maganan xan mata,” Aliyu

ya sunkuyar da kansa bae ce komai ba,

Abba yace “ae ni na gaya maka baxan mata

dole ba, kajekayi xamanka da dayar matarka

tace baxata koma ba,” Aliyu yyi shiru da

ganinsa bae ji ddin maganar ba, ganin Abba

ya maida hankalinsa kan abinda yake yasa

yace “to Abba kayi mata maganarkar ta sake

yunkurin xubar min da ciki,” Abba yace

“tashi ka ban waje, nonsense kawae” Aliyu

bae ce komai ba ya mike yyi masa sallama ya

fita daga falon ba tare da Abba ya amsa ba.

Dakin Haisam ya nufa, ya samesa ya gama

shiri xae fita office, Haisam yace “daga ina

da sassafe hka,” Aliyu yace “taimako nake

son ka min Haisam, kasan yarinyar nn na jin

maganarka don Allah kace mata ta yi hkuri

ta koma dakinta, ni wllh bana son wani abu

ya sami yaran nn ne, kasan yarinta yyi mata

yawa, ga inna kuma ba tsohuwar arxiki ba

ko ita xata rakata su fake idon Abba suce

xasu je cire cikin kuma” haisam yyi yar

dariya yace “da knn Inteesar ke jin

maganata ba ynxu .

Aliyu ya dafasa yace “plss ka gwada kaga Haisam,

wllh

bana son xamanta a gidan nn,” Haisam yace

“shknn xan gwada yi mata maganan ltr idan

na

dawo,” Aliyu yace “thank yhu,” a tare suka

fita da

Haisam kowa ya kama hanyarsa. Inteesar na

komawa falon inna, inna ta mike da sauri ta

dawo

kusa da ita tace “me Bukar din yace maki,”

inteesar tayi shiru da ganin idonta kasan

tayi

kuka, inna ta mike a fusace tace “xan ko ci

mutuncinsa, da wnne xaki ji,” tana fadin hka

ta

fixgi mayafi a fusace tayi waje, da sauri

inteesar

ta bi ta ta riko hannunta tace “ni inna bbu

abinda

aka min kin wani kwashi kafafuwa ina

xaki,” inna

tace “to kukan me ki ke yi ba ayi maki komai

ba,”

inteesar tace “ni ki rabu dani,” ta shige

bedroom

ta bar ta nn tsaye, inna ta bude baki tace

“au”

can ta tabe baki ta ci gaba da aikinta. Karfe

tara

saura tace ma inna xata gun momynta, inna

tace

“yau kuma, to ki tsaya ki sha kunun da na

dama

maki tunda kin ki shan tean” inteesar tace

“xan

dawo inna,” snn ta fice daga falon tayi

sashinsu a

sanyaye duk sae taji bata jin ddin jikinta,

wanke

wanke ta tarar momynta nayi a bakin famfo,

ta

karasa tace “sannu da aiki momy, kawo na

karasa maki,” momy tace “A’a bar shi

kawae,”

inteesar bata ce komai ba ta shiga falo ta

karasa

bedroom din momynta tayi kwanciyarta,

duk

jikinta a sanyaye yake wae mayen cikin nn

na

jikinta duk axaban da ta sha, hawaye ne ya

shiga

bin kuncinta, ta dde tana kuka a hankali

daga

bisanni bacci ya dauketa, karfe goma momy

ta

shigo dakin ta tada ta tace “kin karya ne,”

inteesar ta gyada mata kai tace “ehh” momy

ta

juya ta fita daga dakin, baccinta ta ci gaba

da yi

har kusan sha biyu, xaxxabi ya fararkar da

ita,

sanyi ssae ta dinga ji ta mike da kyar ta

dauko

bargo ta lulluba, biyu saura momy ta shigo

dakin

tace “kinyi sllh ne,” ta girgixa mata kai da

kyar

tace “ynxu xanyi,” momy ta karaso jikin

gadon

tana kallonta ganin yanda ta takure kanta

tace

“me ya same ki,” da kyar inteesar tace “bana

jin

ddi ne,” momy bata ce komai ba ta fita, can

bayan kmr minti goma ta shigo dakin rike

da

kulan abinci tace “ki tashi ki ci abinci, kina

shan

magunguna ne,” kai kawae inteesar ta

gyada

mata ba don tana shan maganin ba, ta

sauko da

kyar momy ta xuba mata abincin ta fita,

tuwan

shinkafa ce da miyar bitter leaf tayi mata,

inteesar ta mike da kyar ta shiga bayi ta

kurkure

bakinta ta wanke hannu ta fito ta jawo

tuwan

gabanta ta shiga ci a hankali, loma uku

kawae ta

ci taji xuciyarta na tashi ta rasa inda xata sa

kanta, lkci daya aman ya xo mata ta mike da

gudu ta fada bayi ta shiga kwarara amai,

momy

dake falo ta shigo dakin da sauri ta shiga

bayin

tana kallonta, har ta gama aman snn ta

taimaka

mata ta gyara jikinta suka fito, momy tace

“ina

magungunan da kike sha,” ta kwanta tana

girgixa

kai ta kasa cewa komai sae mayar da

numfashi

da take, momy ta shiga bayin ta gyara inda

tayi

aman ko da ta fito inteesar tayi bacci, don

hka ta

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button