Uncategorized

HAJNA 21-22

 ♻️♻️♻️HAJNA♻️♻️♻️

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

PAGE 21-22

***********************

Fira suka taɓa ita da Umma, sannan ta tashi ta koma ɗaki, tabbas zata yi kewar Umma, cikin dare da misalin ƙarfe 10:30 ta ji Baffa ya shige ɗaki, dama shine lokacin da yake kwanciya , har ƙarfe  12:30 sannan ta fito, bata ɗauki komai ba, hijab kawai ta saka, a hankali take tafiya har ta kai ƙofar gida, Alhamdulillah dama Baffa baya rufe ƙofar gida da sakata, kawai addu’a yake, dan yayi imani ba wanda zai iya shigo masa gida, amma be taɓa tunanin watarana wani a gidan sa zai fita ba, kamar yadda Hajna tayi yau. 



     Ta lugun dake tsakanin gidan su, dana Fahna tabi ta wuce, a bayan gidan su ta  ga wata mota baƙa mai tinted black, fitowa Fahna tayi daga cikin motar, suka shiga, direct gusau suka nufa kai tsaye. 




********************************

Washe gari da safe. 


Baffa yayi sallah ya fita, ƙofar gida, har ƙarfe 10:30 Hajna bata fito ba, shigowa yayi yace “Aminatu! “Baffa ya kira sunan Umma, “na’am malam”umma ta faɗa, Baffa yace “wai kin duba Hajna kuwa?”, “a’a malam, me ya faru”, Baffa yace “duba ta dan Allah duk yau bata fito ɗakin ta ba “, murmushi Umma tayi tace “to kai kasani ko bata tashi ba, kasan fa bata sallah”, Baffa yace “to shikenan, ki barta wataƙila a gajiye take “, Umma tace “to shikenan”. 



**************GUSAU*************



Hajna ce zaune duk abun duniya ya dame ta, Qaseem ɗin da ta gudu saboda shi baya ɗaukar wayar ta, gashi tun da safe Fahna ta fita, ita bata ma san inda Fahna ta nufa ba. 


    Da misalin ƙarfe 12:00,Fahna ta shigo ɗaki ta sami Hajna zaune tayi taguma, “ke banza tashi dan Allah muje parlor “Fahna ta faɗa, Hajna bata musa mata na ta bita, Hajna tayi matuƙar mamaki da taga Qaseem, zaune ta same shi  wanda hakan ba ƙaramin daɗi ya mata ba, nuɗe hannun shi yayi ta faɗa jikin, ya mayar ya rufe, a tare suka sauke wata ajiyar zuciya, Qaseem yaji daɗi ba kaɗan ba, ganin Hajna dan be yi tunanin ganin ta ba, ko Fahna bata faɗa mishi ba, kawai ce mishi tayi yazo gidan ta zasu yi wata magana akan Hajna, “Favorite one, am so happy to see u “, murmushi tayi amma bata ce komai ba, ita bata da ta cewa, dan ta san duk yadda zata faɗa bazai gane ba, har yanzu tana kwance a jikin sa ita bata ce komai ba, kuma bata tashi daga jikin sa ba, kallon Fahna yayi yace “ya aka yi tazo nan”, Fahna tace “kirana tayi wai baka ɗaga wayar ta saboda Baffa ya hanata fita, shine na je na ɗauko maka ita “, murmushi yayi yace “ gaskiya kin kyauta”, kallon Hajna yayi yace “dama haka kike so na? “

, “hmmmmm” kawai ta iya furtawa, wayar shi ya zaro daga aljihu, nan take Fahna taji alert ɗin 2million, sai jin ƙarar alert tayi, zare ido tayi ta kalli Qaseem tace “ 2million duk nawa “, murmushi yayi yace “a’a na kawo Hajna da kika yi ne, yanzu zan wuce sokoto na hau jirgi, yau zan koma abuja, saboda kira na da kika yi shiyasa ban wuce ba, kinga bazan bar Hajna nan ba tare za muje”, Fahna tace “to shikenan Allah ya tsare hanya “, “ameen ya rabbi” ya faɗa, Fahna tace“to ke hajiya sai ki tashi ku tafi”, tashi tayi suka wuce.


     A ɓangaren su Umma kuwa har aka yi azahar Hajna bata fito ba, Umma tace “ni kam bari in shiga ɗakin yarinyar nan, nasan dai ciwon nan ne ya matsa mata”, ɗakin ta  nufa, ta buɗe mamaki ya kamata lokacin da ta kalli ko ina na ɗakin amma bata ganta ba, gashi ɗakin ba wani guri da za’a ce mutum ya ɓoye, gashi komai nata lafiya ƙalau ba’a taɓa, fitowa tayi tana salati, Baffa da shigowar  sa kenan, a firgice yace “ lafiya dai Umman Hajna, me ya faru “, Umma tace “banga Hajna ba”, Baffa yace “wace Hajna? “, Umma tace “wace Hajna  kasani, bayan ƴar ka” ta faɗa cikin ruɗani, Baffa yace “duba ta dai ko ta shiga banɗaki “, Umma tace “ina waje fa tun ɗazu ban motsa ba, yaushe ta fito da bangani ba”, Baffa yace “ke dai ki duba ta, ki gani ko kina gyangyaɗi ta shiga “, Umma tace “hmmm, gyangyaɗin me zan yi, bari dai na duba”, Baffa yace “ke dai ake ji, nace ki duba ta kin tsaya wani zance”, toilet Umma ta nufa, ta duba bata ganta ba, kuka Umma ta saka “Innalillahi wa’inna ilaihir raju’un, an sace min yarinya “, Baffa cikin ruɗani yace “wai da gaske baki ganta ba”, “to na taɓa maka irin wasan nan ne? “Umma ta faɗa, tare suka dinga duba gidan amma ba Hajna ba labarin ta, kuka Umma ke yi Baffa na kwantar mata da hankali, “ki zauna bari na fita waje naji ko wani ya ganta”, Umma tace “ni ba zaka barni nan ba “, dole suka fita tare suna tambaya ko wani yaga Hajna, amma ba wanda ya ganta, Umma sai mita take yi wai laifin Baffa ne da yake barin ƙofar gida buɗe, gashi nan an shigo an sace mata ƴa, har aka yi la’asar suna yawon neman Hajna, Baffa ne yace “Aminatu muje na raka ki gida, ni zan dawo na cigaba da ciyar ta, har Allah yasa a dace, ko wani ya ganta “, a hanyar su ta komawa gida suka haɗu da wani, gaisawa suka yi da Baffa, yace “Malam lafiya ku ka fito”, Baffa yace “lafiya dai, wallahi Hajna ce muka nema muka rasa, bata gida “, mutumen da suke magana dashi wanda ake cewa Audi yace “to jiya cikin dare ba ita bace naga ta fito daga gidan ka ba”, “ina? “baffa ya faɗa, Umma tace “ba dai Hajna ba kam, ƴata bata yawon dare”, Malam Audi yace “to wataƙila ban gani da kyau ba, amma jiya naga wata ta fito daga gidan ku, ta lugun dake tsakanin gidan ka dana marigayi Habu naga tabi ta wuce, nayi jiran in ga dawowar ta ban gani ba, na gaji na tafiya ta gida “, Baffa da yake jin ƙamshi gaskiya a maganar yace “ to shikenan Allah ya bayyana ta”, wucewa suka yi, a ƙofar gida suka haɗu da wani mutum “kaine Mahaifin Hajna”mutumin ya faɗa, Baffa yace “eh nine”, yace “ni da farko ina da shago ne bayan gidan ku, yanzu labari ya same ni kana neman Hajna, shine nazo na faɗa maka, jiya cikin dare na ganta, ita da ɗiyar aminin ka Marigayi Habu, sun shiga wata mota “, Baffa yace “ina suka nufa?”, mutumin yace “labari ya same ni cewa wata mota ta wuce gusau cikin dare ana tunanin ko ƴan fashi ne, ta nufi gusau, ni kuma da yake nasan su waye sai nace musu ba ɓarayi bane, ƴar malam Ibrahim ce da marigayi Habu”, Baffa ya dafe kai yace “nagode sosai”, Umma ma, mutuwar tsaye tayi, kuka kawai take, dan yanzu kam ta yadda Hajna ta gudu ta bar gari, kuma ita Umma bata ganin laifin kowa sai na Baffa, “duk da baka tsananta mata ba, har ka hana ta fita, duk da baka hanata fita ba, ai da yanzu tana gidan nan, shi yaro ba’a tsananta mishi “, Baffa yace“ko kuma sakaci irin naki ba, da kina sa mata ido ai da bata gudu ba, Allah ya gani nayi iya yina, amma tunda ta zaɓi irin rayuwar Fahna, taje ga duniya nan, duniya zata koya mata darasi”, Umma kuka kawai take yi. 



Anan zan dasa aya…….. ✍️



Haɗin gwiwar : Queen Nasmerh & Rabiatul Adawiyya 


ALQALAMI YAFI TAKOBI ✍️????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button