JARIRI COMPLETE HAUSA NOVEL

JARIRI COMPLETE HAUSA NOVEL

[10/10, 11:53] Ameera Adam????: ☀️ FIRST CLASS WRITERS ASSO☀️

{Home of qualities and trusted writer’s of The nation}
https://www.facebook.com/groups/856755331683130/?ref=share

         ???? JARIRI  ????

Labari da Rubutawa: AMEERA ADAM

SADAUKARWA GA ƳAN GROUP ƊINA NA AMEERA ADAM FANS GROUP

       GARGAƊI 

BAN YARDA A SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.

    1&2

Fuskar Halifa ɗauke da damuwa yace, “Inno gaskiya zuwa gidan Nusaiba da matsala saboda ko kaɗan banasan tayi nesa dani, na shaƙu da matata banasan ko nan da cen taje kawai kuyi haƙuri ku barta a nan” Inno ido ta zura masa tana ganin rashin kunyar ƴaƴan zamani ido biyu, kafin tayi magana Goggo ta karɓe zancen da, “Ka ji mun yaro da sabuwar salawaitun fitsara ido biyu, mu zaku gwadawa fitsara da rashin kunya? Munga tantabaru ma wajen soyayya yaran yanzu da komai sai sun nuna rashin kunya a ciki, mun ƙi mu bar maka ita sakarai kawai” Inno ta ce, “A’a barshi Hansai ya nuna mana ya kusa haɗa kafaɗa da mu, tunda ya kusa ajje ɗa kinga mun haihu shima ya haihu ai mun zama ɗaya da shi, fitsararre mai idanun marasa ɗa’a dubi yadda yake fiƙi-fiƙi saboda ɗiban albarka” Nusaiba da ke gefe ta zumɓuri baki gaba ta ce, “Ni dai gaskiya Inno ku ƙyaleni a nan inyaso wani a cikinku yazo ya zauna mun”

Nusaiba na rufe baki Goggo ta ce, "La'ilaha'illallahu Muhammada ɗan Abdullahi, Inno kinji ɗibar albarka da yarinyar nan zatayi mana irin ta yaran zamani, kinji Nusaiba ta zaɓi miji akan gidan ubanta, ke dan Ubanki ni zaki nunawa rashin kunya ido biyu, idan ban kwashe miki albarka ba kice bani bace?" Halifa ya ce, "Goggo abun fa bai kai haka ba, saboda Allah zuwa gidan nan yayin haihuwa ba fa dole bane ku barmun matata a gida mana, ina jin ɗumunsu ita da abinda zata haifa amma kunzo sai kwashe mana albarka kuke, a haka zan barta taje wanka gida kuna kwashe mata albarka? Haba ina dalili." 

Wannan karan Inno ce ta kuma rafka salati ta ce, “Tir da wannan halin naka na rashin ɗa’a amma dai Halifa na sai na kwashe maka albarka, wato jarabar taka ido biyu har agabanmu dan rashin ɗa’a? Wato mu bar maka yarinya inyaso ko arba’in bazatayi ba ka nuna rashin ɗa’a mujita da wani cikin ko?” Halifa hannu biyu yasa ya rafka tagumi saboda tsofaffun ba ƙaramin caja masa kai suke yi ba, cikin damuwa ya ce, “Inno wai dan Allah me yasa kunfiya matsala ne? Ni fa shiyasa wani lokacin ko ziyararku banaso saboda ba’a kwashewa ta daɗi da ku”

Inno daƙuwa ta watsa masa ta ce, "Ubanka Salisu shine me matsala, kuma wallahi kamar a kunnensa zan kira uban naka a waya naji ko shi ya baka lasisin da zaka ɗebe mun albarka"  tashi yayi ya fice daga falon dan yasan indai ya cigaba da biye musu to tabbas zai hau sama da su.

Nusaiba da sauri ta tashi tabi bayan mijinta bisa tsautsayi ta harɗe ta faɗi, nan take ta fara naƙuda ba shiri suka fara ƙwala masa kira, hankali a tashe ya dawo suka kamata suka sakata a mota suka wuce asibiti.

Zuwan su asibiti da awa guda Allah ya sauki Nusaiba lafiya ta haifo ɗanta namiji kyakkyawa da shi, Nurse ɗin data karɓi haihuwarce ta fara goge jaririn amma wani abu daya ɗaure mata kai, yadda jaririn ya ƙura mata idanu ba kiftawa har hannu tasa ta rufe masa ido amma ƙir idanunsa a kanta, idan ba musu idanunta suke yi mata ba kamar ma harararta ta ga jaririn yana yi. A haka ta samu ta gama gyarashi da gurin aka sa masa kaya Nusaiba ta rungume abinta suka koma bacci, kafin wani lokaci tuni ƴan uwa sun cika asibitin kowa xai zo hannunsa ɗauke da kullar abinci yake shigowa, gudun hayaniyarsu yasa nurses suka hanasu shiga ɗakin da Nusaiba take saboda karsu hanata bacci.

Bayan wani lokaci, Nusaiba ce ta tashi gabaɗaya yunwa takeji cikinta kamar anmata yasa, batasan da kawo abincin da akayi tana bacci ba dan haka ta ƙwalawa Nurse kira, tana zuwa tace ta kira mata su Inno da sauri ta fita ta sanar musu da saƙon Nusaiba, su Inno tare da sauron ƴan uwa ne suka shigo ɗakin fuskarsu ɗauke da farinciki, wasu daga ciki ne suka ɗau jaririn, Nusaiba a shagwaɓe ta ce, "Inno yunwa fa nake ji ku haɗa mun ruwan tea" Inno ita da goggo da ƙarfinsu suka nufi wajen kullar amma tunkafin su buɗe sukaci karo da tsottsatssen ƙashi da wanda aka taune akan murfin kular, suna buɗe ƙatuwar kular abinci yace ɗaukeni inda kuka ajiye.

Ledar ƙaton buredin ma cen ƙarƙashin gado suka hangota, da alama anciye biredin iskar fanka ce ta tura shi cen ƙasan gadon, mamaki ne ya kamasu amma babu wanda ya magantu a cikinsu, Inno ce ta ɗakko flask ɗin shayi shima ta jishi shafal ba komai a ciki, a hassale ta fara magana. "Yau naga rashin ɗa'a ido biyu ni za'a gwadawa ɗiban albarka. Waye ya cinye abincin da shayin gurin nan?" Goggo ta ce, "Gane mun hanya yarinya ta haihu madadin taci ta ƙoshi gashi wasu ƙarti sun cinye"

Da mamaki Mahaifiyar Nusaiba ta ce, "Inno duka abincin kulolin aka cinye? To Nusaiba ko kinci abinci ɗazu?" Nusaiba ta girgiza kai, Inno ta ce, "Banda rashin ɗa'a Nusaiba duk cinta ai bazata iya cinye cooler uku ta abinci ba, maza kiramun masu fararen kayan cen gabaɗaya sai na kwashe musu albarka banda su babu me aikata wannan rashin ɗa'ar, yara sai rashin ɗa'a da ɗiban albarka kamar ƴaƴan mayunwata." Mami mahaifiyar Nusaiba ta nufi mazaunin Nurses ɗin ta kira suka taho tare dan su a tunaninsu wani abun ne ya samu Nusaiba, suna zuwa Inno ta kalle su ɗaya bayan ɗaya ta ce, "Ina kuka kai abincin gurin nan saboda ɗiban albarka yarinyar nan ko loma ɗaya batayi ba, idan sha'awa ya baku basai ku tambaya a baku ba amma zaku nuna mana halin rashin ɗa'a wato sai kunci na Allah ya isa ko?" kallan juna suka farayi kamar haɗin baki suka ce, "Wane irin abinci ana zaune ƙalau kamar wasu mayunwata" Goggo kulolin ta janyo tana cewa, "Gasu naga ɗazu ke kika taya ni shigo da wata" ɗan zaro Ido sukayi suka ce, "Duka abincin cikin kular aka cinye" Inno ta ce, "Kiji mun shakiyyan yara marasa ɗa'a tambayarmu ma kuke yi, wallahi ko ku fito dashi ko na ɗebe muku albarka ku bi duniya"

Ɗayar nurse ɗin ce ta ɗan fara ɗaukan zafi ta ce, "Iya wai me kuka ɗauke mu ne saboda kuma muna ma'aikatan jinya duk wata ƙura aka ɗebo sai a watsa mana..." Inno a hassale ta katseta. "Amma kedai wannan yarinyar anyi maras ɗa'a wallahi idan baki rufen baki ba zan kwashe miki albarka ki ɓalɓalce " ganin abun na nema zama faɗa Mami ta sasanta tare da yin waya gida akan a ƙara kawo musu wani abincin.

 A yammacin ranar aka sallami Nusaiba ita da Jaririnta, tun a asibiti ake taƙaddama akan zaman Nusaiba a gidan ita Mami ma shiru tayi saboda yadda su Goggo suke ja'ina da Halifa amma fir yaƙi yarda. A hassale Goggo ta ce, "Rakiya wai dole sai mun bi ta yaron nan ne? Shi da ita duk jikokinmu ne me zamu zauna muna bi ta tasu, ni idan ya bari idanma bai bari ba zan ɗauke ta na wuce gurina da ita." Inno sheƙeƙe ta ce, "Hansai au ke zaki tafi da Nusaiba? Wallahi bazan yarda da wannan ɗiban albarkar ba nice na haifi Uban Halifa ni nake da iko da wannan maganar" Goggo ta ce, "Rakiya wallahi baki isa ba nina haifi Uban Nusaiba dan haka nina fi dacewa da tafiya da ita" Inno ta ce, "Ahayye Allah na dawo inji kishiyar me yaji, wallahi baki isa kizo mun da wannan rashin ɗa'ar ba,  ninan gurina zan wuce da ita." Halifa ne ya shigo yaji yadda suka fara hawa sama a tsakaninsu dukda sun kasance ƴan uwa kuma aminan juna, Halifa ya fahimci sarai inda maganarsu ta dosa yace,"Nifa gaskiya babu wanda zai ɗaukarmun mata wai magana ɗaya ayita yinta har a asibiti ina dalili, idan fa kuka takura zau ɗauke matata na kaita wani gidan nawa inyaso na samu wacce zata dinga kularmun da ita " Inno ta ce, "Oh La'ilaha'illallahu muhammad rasulillahi sallallahu'alaihi wasallam, oh ni ɗiyar mutum huɗu ba ko ɗaya naga abinda ya tsirewa kakata Laure ido, yanzu ɗibar albarkar da zaka mun kenan Halifa wani bari ubanka ya zo ya shata mun layi da kai, kai anya ma wannan ba'a sauyawa Salisu kai a asibiti ba?"  Mami ce ta ce, "Inno dan Allah kuyi haƙuri ku bar masa matarsa tunda har yace bayasan taje gida wanka, shawara ɗaya zan bayar gabaɗaya kuje ki zauna mata ai ina ga hakan yayi?" gabaɗaya sun aminta da shawarar Mami, Inno ta ce. "Hansai kinga gwara da akayi hakan dan kinsan ni yanzu bana iya aiki a bakin wuta, na dinga kula da aikin cikin gidan kina ɗora garwan wankan mejego da jaririnta idan ba haka ba kar naxo na aikata rashin ɗa'a" Goggo ta ce, "Eh kuma fa hakane Rakiya kinga zamanmu bibbiyunma zaifi."

Da wannan shawarar suka tarkata zuwa gida tare da ƴan uwa da abokan arziki.

 A daren ranar da suka koma da daddare kimanin karfe biyun dare Inno ce ta fito fitsari ahanyarta ta dawowa, ta hango ƙaƙanin abu na tafiya idan yayi gaba sai ya dawo baya ya rangwaɗa kai gefe. A ɗan tsoroce Inno ta ce, "Toooo yau wacce irin ɗiban albarka nake gani da tsohon daren nan" ta ƙarasa magana tana haskashi da ƴar fitilarta.


A zabure ta ja baya ganin jaririn Nusaiba ne tumɓur ko wando babu, washe mata baki yayi ya dafe ƙeya yana wani irin layi kamar wanda yasha ya maku, cikin wata irin murya ya cafe irin maganar Inno yace, "Tooo yau wacce irin ɗiban albarka nake gani da tsohon daren nan" tana faɗa yana wani irin tsalle kamar zai faɗo kan Inno, wurgar da butar tayi saboda tsoro ta fara gudu. Tsalle yayi ya caɓe zanin Inno har ya taɗe ta ta faɗi da rarrafe ta dingan rarrafawa tana ƙwala ihu, lokacin da ta ƙarasa ɗakinsu tuni ta daɗe da wurgar da zani daga ita sai ɗan fatarinta.

UMMOU ASLMA BINT ADAM????

FIRST CLASS WRITERS ASSO☀️

ANYA BAIWA CE?

         Na

AMEERA ADAM

LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, GAME BUƘATAR VIP POSTING SAU BIYU A RANA ZAI BIYA 400, GABAƊAYA ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM ZA’A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 0706 206 2624,DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI.

FREE PAGE 1

   Tafe take tana ɗan waige dan gudun kar wani ya ganta ko taci karo da wani a hanya, saboda abin da ta gano take san zuwa ta isar da shi ko ta samu ɗan alheri, aikuwa batayi aune ba tana shiga soron tsakiya suka yi gware da mutum a zabure ta ja da baya tana sauke ajiyar zuciya kamar wacce tayi tseren gudu, kallan tsaf yayi mata yana karantar yanayinta yasan tabbas akwai abinda ke ƙunshe cikin bakin ta, aɗan diriri ce ta kalle shi ta ce.

    "Yautai mugun tsuntsu masha miyarka sai yayi dare" 

    Kallanta yayi sai da yayi murmushin gefen baki yana ƙara karantar yanayin ta sannan ya ce, " Tauraruwa mai wutsiya..., Kura kike ga tsoro ga ban tsoro. Ina zaki kike sauri kina ta juye-juye haka? " Sai da ta juya hagu da dama ta kuma leƙa soron ƙarshe tana mai miƙa wuya cikin ƙasa da murya ta ce, " Gobara daga teku maganin ta sai Allah, wata ƙura ce take ƙoƙarin kunno kai a cikin gidan nan amma karka ce kaji daga baki na " ta ƙarasa magana tana kuma duba gabanta da bayanta.

   "Jakadiya Kubura kenan, ay harbi ga ɗan jaki gado ne, kuma iya ruwa fidda kai gayamun ina sauraron ki kowa ya biya allon sa ya wanke " ya faɗa cikin son jin labarin.

 Sunkuyowa tayi dabda shi sannan ta ce, " Kasan koda girgiza kurna tafi magarya, mai tsoron a mutu shi yake maho " Ƙara gyara tsayuwarta tayi sannan ta ce, "  Ƙaramar kyauta tafi babbar rowa " ta ƙarasa faɗa tana miƙa masa hannu alamar ya bata wani abu.

Ya gano abinda Jakadiya ta ke nufi, dan haka ya sa hannu cikin aljihu ya ɗebo mata silallah ya zuba mata akan hannun ta yana faɗin, " Ke dai ciki kike mai manta kyautar jiya, kuma Kura kike mai manta alherin baya" 

Juya su tayi cikin jindaɗi ta kunto bakin zaninta ta ɗauresu tana faɗin, " Domin rana ɗaya ba'a ƙin zuguri, kuturu da kuɗinsa alkaki sai na ƙasan langa, buɗe kunnen ka yanzu zaka sha labari, ashe Fulani Zaliha ciki gareta har ya girma, kasanta da shegen nunkufurci ba ta cika bada fuska a shiga sashenta ba " zaro idanu yayi waje shima yana waigen bayansa sannan ya ce, " Lallai tsugunne bata ƙare ba ansai da kare an sayi Mage, naji daɗin wannan albishir naki jeki anjima zan neme ki " ya faɗa yana yin gaba abinsa.

    Jakadiya Kubura ta fahimci sarai inda maganar Galadima ta dosa har yaje bakin ƙofa ta ce masa, " Injunan ka sammako wani tafe ya kwana, kuma hargagin ɗan damisa bashi tsorata Namijin zaki, ka taka a sannu kasan Fulani Maryama ba kanwar lasa ba ce " kamar bazai bata amsa ba sai kuma ya juyo ya ce mata, " Tabbas inkaji mutum na tsoron dare ba'a ɗaure shi ya ƙwance bane, Ki bar ganin allura ƙarama itama ƙarfe ce, dan haka bazan ce miki komai ba mu zuba mu gani kowa tasa ta fishsheshi " yana gama faɗa ya sanya kai ya fice daga cikin soron.

  Bin bayansa tayi da mugun kallo sannan ta ce, " Mai ƙafa huɗu ma ya faɗi bare mai biyu, ajuri zuwa rafi wata ran tulin zai fashe " tana faɗa ta juya ta cigaba da tafiya, kai tsaye sashen Fulani Maryama ta nufa.

  Tana shiga ta zube ƙasa cikin salon kirari ta fara magana, " Barka da hutawa Uwargida na bango madafar bayi, uwar marayu uwar mara gata mai iyayenma kin gamai musu komai, Ƴar sarki jikar sarki Matar Sarki kuma gaki  Uwar Sarki, Allah ya ƙara girma ya raya mana Yarima mai jiran gado, Mulki da Sarautar Masarautar Kano gaba ɗaya ta ku ce, Mai Uwa agindin murhu bazai ci miyarsa lami ba... " murmushi Fulani Maryama tayi saboda jin daɗin kirarin da Jakadiya tayi shiyasa ma ta katse ta da faɗin, " Jakadiya anjima zan turo da saƙon maɗi mai ke tafe da ke??  " russunar da kai Jakadiya tayi tana mai sauya yanayin fuskarta cikin damuwa ta ce, " Tuba nake Uwar gijiyata banzo dan isar da mugun labarin nan dan wata manufa ba sai dan ki tashi tsaye ki ɗau mataki kuma asan abin yi, Kaicona da tuntuni ban ankare ba har lamarin ya girmama, amma dukda haka ba za'a rasa abinyi ba dan ba'a rasa nono a riga, ina mai neman gafarar ki saboda labarin bamai daɗi bane ranki shi daɗe " 

  Tunda Jakadiya ta fara magana Fulani Maryama gabanta ya yanke ya faɗi saboda tasan labarin bazai mata daɗi ba, shiyasa a hargitse ta wurgo mata tambaya, " Jakadiya banasan Kewaye-kewaye tafi kanki tsaye, Me yake faruwa ne?" 

 Jakadiya kara sauya muryarta tayi ta ce, " Ina neman gafararki da jin kalamai na dama Fulani Zaliha ce ke da juna biyu, kuma ayanayin dana lura har yayi ƙwari..." cikin tsananin tashin hankali Fulani Maryama ta ƙunduma wani ashar sannan ta ce, " Aikin me kike tun tuni baki sanar dani ba tunda wuri? "

 Jakadiya ta bata amsa da, " A gafarce ni Uwargijiya ta kinsan Yarinyar da nunk..."

  Katseta Fulani tayi cikin tsawa ta na faɗin, " Ya isa haka, Lallai Fulani Zaliha ta ɗebo ruwan dafa kanta, Samun sararin kuturu gaɗa a cikin rama, wato haka ta miƙe ƙafa da yawa? Lallai abinda ya faru a shekarun baya dole ya ƙara faruwa yanzu, tabbatas dole labari ya ƙara maimaita kansa, Aikuwa kowa yaci tuwo dani miya yasha, tashi kije Jakadiya anjima zan neme ki bayan Sallar Isha'i " 

   Jakadiya najin  haka ta kuma rissinawa ta ce, " ALLAH ya huci zuciyar Fulani, Ramin kura da wuyar shiga a gayawa kare yayi hankali, tabbas bakin rijiya ba wajen wasan makaho bane wace ce Fulani Zaliha da zata iya haɗa sahu da Uwar ɗakina, ni mai bin Umarnin ki ce akowanne lokaci " Jakadiya na gama faɗa ta tashi ta fice zuciyarta fess saboda tasan ba ƙaramin alheri zata samu ba.

     Tunda Jakadiya ta fito daga ɗakin, Fulani Maryama ta kasa zaune ta kasa tsaye sai kaiwa da komawa take, abun duniya gabaɗaya ya isheta, ita kaɗai sai saƙa da warwara ta ke tana san nemarwa kanta mafita, Jaririnta ɗan kimanin wata biyar da ke kwance ta je tasa hannu ta ɗauke shi tana juya shi cikin zuciyarta da shawarar da ta yankewa kanta.

 A fili ta fara surutai kamar wata zautacciya,  " Yarima yanzu kai ake shirin yiwa kishiya a gidan nan, tabbas bazata yuwu ba tunda ban bari wata ta haifi namiji ba dole na dakatar da cikin Zaliha "

     Jakadiya tunda ta fito daga sashen Fulani Maryama kai tsaye sashen su ta wuce tana zumuɗin sauraron kiran da Fulani Maryama ta ce zata yi mata, kamar wacce a ka mintsina tashi tayi ta fito daga sashen bayi wani gida ta faɗa bakin ta ɗauke da sallama, " Balaraba matar Ciroma dake tankaɗe ta amsa mata sallamar tana faɗin.

" Yau kuma Jakadiya ce da doshin magariba haka?? " Kujera Jakadiya ta janyo ta zauna sannan ta ce, " Eh ko bakya maraba da zuwan nawa ne?? " cigaba da tankaɗenta tayi ta bawa Jakadiya amsa, " Ni na isa nace banten Sarki yayi ɓurtu, ai hanyar lafiya abita da shekara, meye labari?? Dan nasan bakin ki baya rasa motsi?? "

Murmushi Jakadiya tayi ta ce, " Ai dama ni kujera ce dole a zauna dani, kuma abokin cin mushe ba'a ɓoye masa wuƙa, wai kuwa kinsan Fulani Zaliha na ɗauke da juna biyu?? Wa ya sani ma itama ko Namijin zata haifo ni zanso ma ta haifo Namijin naga yanda Fulani Maryama zatayi "  ta faɗa tana ƙasa-ƙasa da murya.

 Da sauri Balaraba ta saki rariyar Hannunta waigawa bakin ƙofa tayi sannan ta cewa Jakadiya, " Da gaske kike wannan maganar?? aikuwa muddin zancen nan yaje gun Fulani Maryama kinsan bazai mata daɗi ba, kuma kinsan dole wani abu ya biyo baya" 

  Jakadiya ƙara matse bakin zanin ta tayi ta ce, " Ai a bakin wawa akanji magana, wai da kunne yaji muguwar magana wuya ya tsere, kinsan dai ai ciki badan tuwo akayi shi ba, bayan ke babu wanda yasan da wannan maganar " 

  Tsuke fuska Balaraba tayi da alama bataji daɗin maganar Jakadiya ba dan haka ta maida mata da martani, " Tafasar tukunya bata gefe ɗaya bace, haka nan abinda baki ya ƙulla hannu bashi iya kunce shi, idan kinji makaho ya ce ayi wasan dutse to tabbaci haƙiƙa ya taka dutse, Jakadiya koma dai mene ne daga bakinki wannan maganar ta fito kuma ni nan da kika gani na iya taku na"

Miƙewa tsaye Jakadiya tayi tana gyara ɗaurin zaninta ta fara takawa har sai da taje wajen bakin ƙofa sannan ta juyo ta ce, " Mutum fari ne shi ke rina kansa ya zama baƙi, bakinki dai ƙanin ƙafarki kuma harshenki linzaminki " bata saurari mai Balaraba zata ce ba ta fice daga gidan.

UMMOU ASLAM BINT ADAM????
[10/10, 11:53] Ameera Adam????: ☀️ FIRST CLASS WRITERS ASSO☀️

{Home of qualities and trusted writer’s of The nation}
https://www.facebook.com/groups/856755331683130/?ref=share

         ???? JARIRI  ????

Labari da Rubutawa: AMEERA ADAM

SADAUKARWA GA ƳAN GROUP ƊINA NA AMEERA ADAM FANS GROUP

       GARGAƊI 

BAN YARDA A SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.

    3&4


 Inno kan katifar da Goggo take kai ta faɗa jikinta na ɓari tana ƙoƙarin fisgar bargon saboda ceton  ranta, Goggo wani uban salati ta rusa wanda yasa Nusaiba miƙewa zumbur ta tashi zaune, Inno banda ihu babu abinda takeyi tana kabarbari.

Cikin magagin bacci Goggo ta ce, ” Oh nikam na shige su yau me nake ji kwarto da tsohon daren nan, yo ni Allah na tuba banda lalacewar kwaratan zamani me zai yi da tsohuwa? Gabaɗaya komai ya saki kamar robar wando…” bata ƙarasa faɗa ba Inno ta ruƙunƙumota sakamakon buɗe bargon da tayi sukayi ido huɗu da jaririn da yake ta washe mata wawulan bakinsa yana ƙara dafe ƙeya, haɗe da wata irin tafiya me tafe da rangwaɗa.

Goggo ta kuma mirtsike idanu ta ce, “A’uzubillahi minasshaɗanirrajim Rakiya tashi kiji yau za’a nuna mun salawaitun iskanci ido biyu, oh ni ɗiyar Mahammadu ka rasa wacce zaka afkawa sai ni tsofai-tsofai da rai wannan ai sai dai ka kasheni da raina.” Nusaiba ce ta janyo wayarta da ke ƙasan fulo ta haska gurin su Inno. Ganin Goggo da Inno kaɗai a gurin Nusaiba taja tsaki ta ce, “Dan Allah Goggo da tsohon daren nan zaku dinga mana ihu ba sai a zaci da gasken kwarto bane ya shigo” Firgigit Goggo ta mirje ido raɗau ta kai kallanta kan Inno, a hassale ta fisge bargon ta ce. “Rakiya wani sabon salawaitun kika samo zaki hau wani fisge-fisge cikin dare?” Inno tana ƙoƙarin ƙara danna kanta cikin bargo ta ce, “Karki buɗe ni Hansai yana nan bina yake wallahi aljani ne ba mutum ba” Goggo ta ce, “Yo nikam yau na gode Allah Inno wai ko gamo kikayi ne?”

Inno ta gyaɗa kai har lokacin jikinta rawa yake ta ce, “Wallahi Jaririn Nusaiba ba mutum bane aljan ne shi ne ya biyo ni” Da mamaki Nusaiba ta kalli jaririnta dake kwance yana shaƙar bacci ta ce, “Wai Inno ko dai mafarki tayi ne take mana magagin bacci har da sumbatu?” Goggo ta ce, “To gane mun hanya dai ƴar nan?” Nusaiba zata yi magana Halifa ya shigo sanye da jallabiyya da waya a hannu yace. “Nusaiba lafiya nake jiyo ihun Inno?” Goggo ta ce, “Ina fa lafiya gamu a zaune cikin taraddadi da salallami” zaro ido ya yi yace. “Me yake damunta?”

Goggo ta ce, “Wai jaririn cen ta gani ya biyota shine ta zo ta shige bargo ni bansan wane irin salawaitu bane, ace jariri ya taka ƙasa kwana ɗaya da haihuwa.” Halifa yace, “Ruɗewa ce kawai irin ta Inno amma wannan ko ɗan goye ai bazai yarda da abinda ta ce ba. Ku rarrasheta kunsan dai halinta da raki” Inno ta ɗago da kai ta ce.

“Halifu wallahi wannan ɗiban albarkar baza’ayi dani ba, maza ka kira mun ubanka Salisu a daren nan yazo ya ɗauke ni mu tafi gida, wannan rashin ɗa’ar har ina?” Halifa yace, “Haba Inno kinsan me kike faɗa kuwa karfe biyun dare fa. Gaskiya ni bazan kira Daddy yanzu ba haka kawai a tayar musu da hankali, ki dinga abu da lissafi mana” Inno hawaye ta fara yi ta ce, “Halifa ni kake gayawa haka saboda nazo gidanka ko? Yoo wace uwa ce ma a gidan naka gida kamar akurkin kaji, kasan gidan Salisu ya zarce naka ɗari bisa ɗari har kake wulaƙanta ni saboda ɗiban albarka. Har abada bazaka ƙara ganina a gidanka ba, ai laifin Salisu ne da na dage zan zauna wankan jegon nan ba sai ya mun nasiha ba a matsayinsa na ɗana, Allah na tuba tsofai-tsofai dani banda rashin imani wane irin zaman wanka zanyi yanzu, ai Halifa kaine ma babban mara imani na tabbata da uwarka Halima ce ta kai shekaruna bazaka bari tayi wannan aikin wahalar ba, wallahi idan baka kira mun Ɗana ba sai na kwashe maka albarka a daren nan kowa ma ya huta.” Halifa ya tsuke fuska yace, “Inno dan Allah dare ne fa yanzu karki tashi moƙota ki bari zuwa safiya inyaso duk yadda za’ayi sai ayi, amma sai magana kike da ƙarfi haba dan Allah dama akwai wanda ya miki dole ki zauna ne?”

"Hansai dan Allah ki ɗauko madoki ki bashi duka na kawai ya rage kayi Halifa, wallahi duk masifarka babu mai hanani tafiya a daren nan shima uban naka zan kirashi idan yace bazai zo ba nayi tafiya ta cikin duniya. Dama wa nake da shi Allah na tuba daga Allah sai ma'aiki" Nusaiba cikin ƙosawa ta ce. "Inno dan Allah kiyi haƙuri zuwa safiya idan fa aka kira Daddy yanzu sai ya ɗauka wani abun ne kinsan yana da hawan jini, kar a tayar masa da hankali a samu matsala"

 Inno sakin baki tayi lokaci ɗaya ta ɗauki wani salati gabaɗaya suka tsaya suna kallonta, sai da ta dire ta ce,"Nusaiba amma Allah wadaranki ke kam anyi gantalalliya bansan wacce irin yarinya bace me mugun alkaba'i, aniya bi aniya. Aniyarki ta biki Salisun kike ja wa wannan mugun ciwon saboda ɗiban albarka, to bakinki ya faɗa kanki muguwa kawai anya ke jinina ce kuwa kike nufina da sharri amma dai anyi maras ɗa'a" Halifa ya shigo ɗakin cikin takaici amma sai ya tausasa murya saboda yasan indai ta haka ne sai su kwana Inno bata daina musu sababi ba yace.

“Inno waya hallicemu wa muke bautawa?”

Inno ta kalleshi baki a sake ta ce, “Halifa kafurta ni zaka yi to wallahi ko Ubanka da addinin ya ganni bare kai gantalalle” Halifa bai kulata ba ya cigaba da cewa.

“Ki dubi girman Allah Inno kiyi haƙuri zuwa safiya kinsan dai Allah yafi kowa, na haɗa ki da shi ki bari zuwa safiya mayi maganar”

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12Next page

Leave a Reply

Back to top button