JARIRI COMPLETE HAUSA NOVEL
"Wallahi Rakiya babu ni babu ke har abada, ki dubi kaina ki gani yanzu idan na koma gida kinsan irin shaƙiyancin da su Kande za su yi mini? Ai ni da zuwa kowanne irin taro ko a lahira albarka." Inno da ta cika fam saboda ta bawa Tarasulu haƙuri taƙi haƙura yasa a hassale ta ce, "Wallahi ƙarya kike Tarasulu kinsan dai dole ki ziyarce taron gangami na lahira, yooo ki tafi mana ba shikenan ba dama ai ba dolr nayi miki ba ƙwaɗayin sharɓar taushe ne ya kawoki." Tarasu da zugar ƙawayenta suka yi ayari suka fice daga gidan suna masifa, musamman Tarasulu da bini bini take shafa molon kanta.
Bayan fitarsu ba daɗewa Inno da Goggo suka fito kowacce ɗauke da jakar kayanta, da mamaki Mummy da Daddy suke kallonsu Daddy yace, “Inno ina zaku kuma?” Inno ta riƙe baki ta ce, “Duniya zamu shiga gwara mu bazama ina dalili wannan ɗiban albarka haka, ko a mafarki ban ta gani aljani ba sai yanzu tsofai-tsofai da rai. A’a gwara na shiga duniya bansan waɗanna irin aljanu ne zasu kuma ɓullowa ba.”
UMMOU ASLAM BINT ADAM????
FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️
{Home of qualities and trusted writer’s of The nation}
https://www.facebook.com/groups/856755331683130/?ref=share
???? JARIRI ????
Labari da Rubutawa: AMEERA ADAM
SADAUKARWA GA ƳAN GROUP ƊINA NA AMEERA ADAM FANS GROUP
GARGAƊI
BAN YARDA A SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.
49&50
????????????????????????????????????
Goggo ta kwaɓe baki ta ce, "Kinga Rakiya idan zaki zauna gara ki faɗa mini na kama gabana dan naga har tsayawa kike sauraron su." Daddy ne ya shiga lallashin ana cikin haka sai ga Adam ya shigo shi da wani Malami, ganinsu ya yi carko-carko a tsaye yace, "Daddy dama Abba ne yace a kira Malami game da Jariri." Daddy zai yi magana Inno ta ce, "Sai yanzu ya ga damar turo shi bayan anci ancinye komai." ta juya tana kallam matashin Malamin ta ce, "Kaima ka ɗebo tsawo kamar daren mutuwa ka biyo shi zugwi-zugwi kamar robar wando, to tuni an gama da taƙadirin." Adam yace, "Inno wallahi tun ɗazu ya gaya mini mantawa nayi na tafi Ball Bichi." Takaici ne ya kama ya kama Inno ta ce, "Da kai da Ball da Bichin idan ban ɗebe muku albarka ba kace na bijirewa Mai salati lokacin da yana raye."
Adam ya ɗaga kaɗa yace, “Yooo wa ya sani tun da dai lokacin bana nan idan ma kin bijire masa ai bazan musa ba” Inno da Goggo lokaci ɗaya suka rushe da kuka suna komawa cikin Goggo ta ce, “Allah na tuba Rakiya ina zamu a wannan salawaitun rayuwar, naka na jininka ma yake cin zarafinka ina ga mun shiga duniya.” Inno ta sharce majina ta ce, “Ban da ɗiban Albarka Hansai wai ni Adamu yake gayawa haka? Wallahi bari Nadabo ya dawo inji ko shi yake karanta masa wannan halin.” suna gama faɗa suka shige ciki, Daddy faɗa ya yiwa Adam akan yadda ya yi wa su Inno sannan suka wuce cikin gida.
BAYAN SHEKARA ƊAYA DA RABI
"Inno to dama har yanzu ba'a samu wanda zai zauna mata ba nace ko ke da Goggo ne zaku je tun da Halifa yace yafisan ta zauna a gidanta..." A hassale Inno ta ce, "Idan naje uwar me zanyi da tsufa na tsofai-rsofai, kinga ni da ƴar uwata babu inda zamu je." Goggo ta shigo tana cewa, "Wai salawaitun masifar me kike yi Rakiya?" Inno ta ce, "Wai kiji ni da ke muje zaman daɓaro wajen nusaiba, ta manta iya shegen da wancen Jaririn ya yi mana" Mummy ta ce, "Allah ya baku haƙuri Inno dama dan kar kuce an kai wata ba a gaya muku ba shiyasa." Mummy na gama faɗa ta fice.
Goggo ta kalli Inno ta ce, “Anya wannan matar nan gaba bazata sa hannu ta dake mu ba kuwa? Dubu salawaitun maganganun da take gaya mana” Inno ta ce, “Barni da ita katuwar banza tana tafe da lafceciyar ƙafa kamar doyar Zariya” gabaɗaya suka bushe da dariya Goggo har da kwanciya, Inno ce ta kalli Goggo ta ce, “Oh ni ɗiyar Mai salati wannan karan ko Tarasulu zata zo mana suna kuwa?” Goggo ta yi mata wani sakaran kallo ta ce, “Kema akwai ki da salawaitun ban haushi, Tarasulu dai kinsan ko kina shure-shure bazata zo ba” Inno ta taɓe baki ta ce, “Ke ta sha zamanta yanzu idan muka gayyace ta kinsan kwaso mana gayyarsu Uwani zata yi su ishe mu da warin ɗiban albarka.” gabaɗaya suka kwashe da dariya.
ALHAMDULILLAH
Anan na kawo ƙarshe littafin Jariri faɗakarwar da ke ciki Allah ya bamu ikon amfani da shi, kuskuren ciki Allah ya yafe mana.
Ina godiya bisa nuna ƙaunarku da bibiyar littafin nan????
Mu haɗe cikin sabon littafi ????
UMMOU ASLAM BINT ADAM