FITAR RANA 15

FITAR RANA 15
Suna isaga dakin wasimé tayi gudu cikin murna da annashuwa ta isa wajen da aka aje kayayyakin ledojin shoping din,atake tahau bubbudesu tana fiddo su waje daya bayan daya.
tsayuwa bilti tay akanta tana famar lura da yanayinta, she seems soo happy right now,rabonta dataga wasime acikin irin wannan yanayin farincikin harta manta sabida kullum a taƙure take cikin tsoro da fargaban gamuwarta da taheer,”..”bilti bilti zoki ga babyn danake fada miki wanne yafi miki kyau”
murmushi bilti tay snn tace “Kai masha Allah ai dukansu ma sunada kyau,..Tace Allah ko bilti?..Toh Ga alawa ma nan ince dai zakisha?
Su chokolates dinta ta firfitar dasu nutella, choclate creamy, sneakers,fresh up,fantisiya,coco balls cream crckers duk saida ta ciccirowa bilti waidan ta zabà,a cikin surutayya tace bilti,Ingaya miki ko?da mukaje gidansu ba..bilti kinga gidan sun kuwa, wani rangajeje dashi wallhi Allah ai gidan ba irin gidan nan bane yafi gidan nan kato..kuma da akwai wasu yara da mukay wasanmu da su akwai ahmadu,teema,bello..siyama..da shatu…dayan antyn mai hankli ne takaimu mukayita wasa dayan antyn kan hmmmm Bata da kirki,Bilti ta tsaya kallon bakinta da mamki “Au wayanan duk a gidan su saheeb din kuka hadu dasu?,”tace eh man..bilti bakiji ba, wancan muguwar antyn ko sai wani tambayata take wai ni ƙanwar dahiru ne? Kuma Kamar zata hadiyeni fa take magana.
Hmm kawai Bilti taja, toh ya isa haka wasime surutun nan naki yay yawa,maida kayayyakin ki kimtsa wajen in taheer yazo kya nunasa masa sai Kice masa saheeb ne ya siya miki..cikin gwalo idanunta waje tace TAB nikuma sai in gayamai!!
a’a kam,nide wallh bazan je wajenshi ba,kedai kije..ai shi masifa kawai zaimin.
Bilti tace “Masifan me zai miki?ai inkinga taheer yay miki masifa to kece bakiyi dadai ba
Dan dakatawa tay da abunda takeyi snn ta kalli bilti cike da son ta fahimce ta”Amma bilti, ni mena taɓa yi masa yakejin haushi na kullum?yo mesa halinsa ba irinna yaa saheeb ba ne? shifa ko dariya bai taɓa min ba barema ya siyamin dan sweet ko babyn robber..
Hmm kawai bilti tace snn ta sauke boyayyar ajiyar zuciya cikin shashantar da zancen tace “wasime ina fatan dai bake kika roke saheeb ya siyamiki kayan nan bako?
Wani Dafe kirjinta tayi
Cikin zaro idanu waje
“Tace Ni?..wallahi tallahi wabillahillazi ban rokesa ba,shine fa yakaini wajen waidan nace mishi ya dawo dani gida shine mukaje wani babban shago ya sissiyamin wayannan.
Tana dasa aya bilti tace
“Toh nide ina gargadin ki da ki kama kanki Wasime banda roko banda kuma kwadayi,Kai daga yauma inya kara cewa zai siya miki abu ko zai baki kudi karki amsa kice kin gode kawai,inya takura ne saiki karba shima bavkoda yaushe ba..kuma ki tabbata kin kawo gida kin nuna min kowa taheer
Idan ba hakaba duk abunda ya biyo baya ke kadanki zakiji dashi.
Kwadayi ba abunyi bane wasime,kwadayi da son abun duniya yana saurin jefa mutum halaka koda kuwa shi mai imani ne.
Kiyi hankli da rayuwa karki jefa kanki a tsabgar da bazaki iya ficewa ba.
Karkiga waike yarince nitsuwa da sanin yakamata shine kadai girman ba yawan shekaru ba,yakamata kisani ke marainiyar Allah ce wasime kiji tsoron Allah mahaliccin ki kiyaye dorawa zuciyanki kwadayin abun hannun wani..
Wani Shiru wasimen tayi cikin yanayin nitsuwa tanajin abunda din biltin take cewa dan bada wasa taga tanayi mata maganan ba,sosai bilti ta gargade ta ta kuma ja mata kunne sosai musmn akan ƙarban abun duniya a hannun mutane musmmn ma shi saheeb.
Atake Jikin wasime yay sanyi har bilti ta gama maganganunta ta fita bata dago kanta dake kallon ƙasa ba..ajiyar zcya kawai ta sauƙe zcyarta cike da fargaba ta mike tsaye ta cire kayan jikinta snn ta shiga bathrum tay wanka tare da yin alwala,sharp sharp ta idar da sallahnta wanda bawai ta gama iya shi bane,yau kam ma kwata kwata zcyarta da mind dinta gaba daya sun raja’a ne akan kayan wasa.
Tana idarwa ta kimtsa dakin tsaf, snn ta kwaso su teddies da barbie dolls dn ta jerasu akasa daganan kuma ta tsunduma wasan baby bataji bata gani.
A fannin saheeb kuwa fitarsa a gidan ya same su tolu da malam musa awaje sun kasa sun tsare a bakin motarsa suna jiran fitowarsa, haka ya ciro sabbin kudade ya rarraba masu goron sallah kowa yana washe baki, a bakinsu yakejin labarin cewa Taheer yy tafya baya gari,Perfect oppurtunty for him ya gayyace wasime zuwa asalin gidan iyayen sa domin suganta cos in two days time za’a ayi big birthday party blast ma kanwarsa anisa duk dama abun na gidane kawai so shiga wajen sai wane da wane sabida a cikin family house dinsu za’ayi.
Burinsa ayanzu baifi yakai wasime wajen mahaifyarsa ba kodama zasu soma sabawa da junansu, ta inda xata nan gaba zai iya dogara da cewa mahaifyar tasa zata taimaka masa wajen yaƙin kwato ragamar kulawa da rayuwar wasime daga wajen familynta, danso yake ta girma tasan cewa shi yay mata komi na rayuwarta kafin suyi aure.
Mahaifyarsa hajiya mufidat Garba bakare babban jamiar kare hakkin dan adam ce,snn ta karance fannin lauyanci tana da doctorate degree dinta.
Tana kuma bada gudumawa mai matukar
Muhimmanci wajen taimakawa marayu da marasa galihu (humanatarian)a reshen ƙasar amurka.
Washe gari da safe wasime tana farkawa a bacci ta soma lalubar ababen wasanta sanda tay wasa iya isarta snn ta tashi tay sallah
Ahakan ma Saida bilti ta tsawatar mata snn ta aje taje tayi sallahn a nitse,kayan datay fitsarin dasu ma yau kasa wankesu tay ta dukunkuna su kawai ta aje a bayan gida,yau hatta abinci shareshi tayi koda bilti ta tursasa mata a gaggauce taci dan kadan snn ta koma kan ababen wasanta ranan gaba daya bilti bata gane kan wasimé ba.
Washe gari da safe ma hakan abun ya kasance saidai sukayi fada sosai da bilti snn ta nitsu tay ababen dake gabanta wasan sosai ya shige cikin ranta, Duk abun duniya ya dame zucyar bilti ,at around 12am lkcin bilti ta kammala dukkan wani ayyukanta ta fito kenan tana zaune a falo akan kujera riƙe da remote din tv a hannunta tana neman tashar arewa tanata famar scrolling har tazo ta wuce kan tashar bata lura ba saboda harga Allah babu wani cikakken nitsuwa atattare da ita,tunanin rayuwar wasime tasaka agabanta tun jiya,da shi ta kwana dashi ta kuma farka,kuma haryanzu tana kai bata fasa ba.
Tunani kashi biyu ke wanzuwa a kwakwalnta har yanzu dai itama hanklinta bai wani kwanta sosai akan tarayyar wasimé da saheeb ba,koda ma ace babu wani cutarwa acikin tarayyar nasu, amma dai tasan dolene salonshi na kashe mata kudi da bata ababen duniya yaxo ya gurbata mata rayuwarta na nan gaba.
Takanyi duba da yanayib bambaci dake tsakanin su da saheeb,shifa dan gidan masu shine masu fada aji..anan kuma su basu mallaki arzikin komi ba face iya wanda Allah ya basu na rufin asiri.
Toh ta ina kenan zasu iya da wasime nan gaba inhar ta kyaleta ta saba da kalar rayuwar da batata ba?yarinya marainiyar Allah kuma ga igiyar Auren wani akanta.
Kamata yay wasime ta zamto killataciya tun yanzu,ita kanta tarasa dalilin dayasa taheer yaki cewa komi akan tarayyar wasime da saheeb aganinta sam sam bai dace ba, duba da yadda sabo na yau da kullum daa kuma shaƙuwa da juna yakeson ya soma yin tasiri a zukatansu.