JARIRI COMPLETE HAUSA NOVEL

JARIRI COMPLETE HAUSA NOVEL

    11&12

Goggo shiru tayi tana raba idanu sai kuma ta juya ta kallo ɗan Jarirn dake kwance saboda tsoro take a barsu su biyu daga ita sai shi a ɗaki, Inno haushi taji ganin irin diriricewar da Goggo takeyi cikin ƙufula ta ce. “Hansai magana nake kina ta wani waige-waige saboda rashin ɗa’a yanzu inba ɗiban albarka ba me zaki mun a banɗaki tsofai- tsofai da rai, Allah na tuba me zaki gani sabo da baki sani ba? Anya hanyar da kika ɗauko me ɓillewa ce Hansai haka kawai ki kai kanki ga halaka yoo halaka mana duk wanda zai ga tsiraicin wani ai hau ta hau shi” Inno ta ƙara tamke fuska ba alamar wasa ta ce. “Hansai tun ban kai kukuna gurin Ubangiji ba ki fice ki bani guri, wallahi banda ma ina duba zumuncin Allah mu biyu muka rage da tuni na kwashe miki albarka kowa ma ya huta” Goggo gabaɗaya ta tsure ƙasa tayi da murya ta ce. “Wallahi Inno tsoro nake ji ina gudun salawaitun da zai ƙara samuna ni kaɗai a ɗaki” Inno ta keɓe baki ta ce. “Hansai me ye gamunmu dake? Uban me zan miki da kika biyo ni ke tsohuwa ni tsohuwa me zan iya yi miki? Yoo Allah na tuba duk ɗiban Albarkar da za’ayi mana me zan iya? Ki fice mun ki bani guri kar fushin Allah ya sauka a kanki ki jaza mini salalan tsiya” Goggo tayi ƙasa da murya saitin kunnen Inno ta ce. “Wallahi Rakiya Jaririn cen nake ji” Inno wata shewa tayi harda tafa hannu ta ce. “Allah na dawo inji kishiyar me yaji. Wallahi Hansai idan baki fitar mini daga bayi ba sai na kwashe miki albarka kowa ya huta, ke da kika ce Jaririn ya fini sau dubu a gurinki to ahir ɗinki karki kara kusantoni, yoo to Allah na tuba ma wacece ke wacce alaƙa garemu Hansai? Allah ya jiƙan me salati dai nasan Mahaifinmu ne sai Mahaifiyarmu Kande banda wannan ki gaya mini dangantakarmu? Wallahi tun muna mu biyu ki fice mini tun kafih nayo yekuwar neman agaji” Goggo tuni idanunta suka ciko da ƙwallah a hankali ta fara takawa ta fice daga banɗakin tana leƙe-leƙe.

Inno ta ci gaba da mita tana cewa. "Ke kiji mace haka kawai kina gidan jikana ki butulcemun saboda yana da abun duniya, sai da kika kwasowa kanki ɗiban albarka zaki tuno da ni, Astagafirullah ina zaman zamana zata jamin masifa da fushin Ubangiji ta sani magana a banɗaki ban shirya ba, banda ma Allah yana kareni da kariyarsa da tuni Sheɗanu basu nuna mini rashin ɗa'a da ɗiban albarka ba, cen kije ki ƙara ta keda ɗan ƙundalon ya yi duk abinda zaiyi kiki ma, Allah na tuba ka yafe mun wannan zunubin da na ɗauka" Inno ta gyara tsayu ta ci gaba da cewa. "Allahumma inni'azubika minal kubisi walkaba'isi, yoo wayasani ma ko dama cen Hansai ta saba ɗiban albarkan a banɗakin Allah na tuba ko ta iya addu'ar shiga banɗakinma oho" Inno ta ci gaba ƴan ƙananan maganganun sannan ta fara wanka.

Goggo kamar wacce ta haɗa gurmin gulma haka ta dinga sunne kai ƙasa tana juye-juye har ta nemi guri ta zauna, a hankali ta fara satar kallon Jariri da ƙyar tayi ta maza ta ɗauko shi ta fara shafa masa mai, tana cikin saka masa kaya Inno ta fito daga wanka tana watsawa Goggo wani kallo. Wayar Inno ce ta fara ringing da sauri ta ɗaga tana faɗin. “Salisu me kakeyi har yanzu baka ƙaraso ba?” Daga cen ɓangaren aka ce. “Wai ke babu me kiranki a waya sai Salisu ne, ɗazu kin kirani ina hanya kike ta kawo ƙorafi gani na shigo gidan Halifan.” Inno ta taɓe baki ta ce. “Wai Ado ne?” aka ce. “Idan kin fito kya gani da idonki” Inno ta katse wayar ta ce. “Yara sai tatalar ɗiban albarka saboda bani na haife su ba sun baidani kamar yawun bakinsu sai abinda suka ga dama zasu gaya mini, kai Allah wadaran naka ya lalace bantaɓa sanin zan samu marasa ɗa’a a zuri’a ta ba. Hansai kiyi ki kintsa mu tafi asibitin nan naji ance ba’a san yiwa yara bbc ɗin nan idan rana tayi” Goggo dai bata kula Inno ba ta gama shirya Jariri ta wuce banɗaki a fakaice take watsawa Inno harara, babu jimawa Goggo ta fito lokacin tuni Inno ta gama shiryawa cikin fallelliyar atamfarta, mayafinta ta ɗauko ta fito falo tana zuwa ta sameshi a zaune shi da Halifa suna hira. Riƙe baki Inno tayi ta ce.”Ado ashe da gaske kaine wallahi na ɗauka waya ce ta mun ƙarya da naji kamar muryarka ce” Ado yace. “Inno sauri nake fa na biyo dan nasan idan ban zo ba zaki ɗagawa su Daddy hankali ne ana zaune ƙalau” Inno kan kujera ta hau tana watsawa Ado harara ta ce. “Wannan dai ba halin Muntarina ka ɗauko ba wallahi dama nasan sai iyayenku sunyi muku huɗubar tsiya akaina, Allah ya mun tsari da mugun halinka wato iyaka zaka yi mini da ƴaƴana ko? Tashi ka fice Ado ka ɓalɓace bazan kuma magana da kai ba bansan da wane mugun abun kazo ba” Ado ya miƙe tsaye yace. “Brother gaskiya kana cikin hazo waɗannan kayan ciwon kan haka kake fama dasu” Halifa ta gyaɗa kai fuska ɗauke da damuwa yace. “Bro Adam ya na iya? Haka zanyi haƙuri har lokacin tafiyarsu yayi” Inno baƙin ciki ya cikata jin maganganun dasu Halifa suke yi ta fara matsar ƙwalla ta ce.

"Wallahi yadda kuka kwashe mun albarka tass sai a kunnen iyayenku, tun da uwa ta haifeni ba'a taɓa cin zarafina irin wannan ba, kuma tunda tsiyar da kake mun kenan Halifa zamana a gidan nan daram zanga uban da zai fitar dani kuma zan Kira Salisu ya kawo mun sauran kayana, yooo dama waye gatanka  Halifa idan bani ba Allah gatanka nice gatanka tunda ko ubanka da uwarka Salmai basa ƙaunarka kamar yadda nake sanka..." bata ƙarasa magana ba Goggo ta fito fuska a ɗaure ta ƙaraso cikin falon kamar a jefota ta ce. "Zauna zauna Ado babu inda zaka je a gidan nan sai ka mun iyaka da Rakiya maza-maza ka mun iyaka da ita kuma tsakanina da ita babu sulhu, ba dai zumunci bane take taƙama da shi daga yau na datse shi ta yi rayuwarta nayi tawa bazan iya da wannan sabon salon salawaitin rashin mutumcin da take mini ba" Halifa ya kallesu ya dafe kai bai tanka musu ba, Ado ne yace. "Goggo wa zai shiga tsakaninku cen ku ƙarata kunfi kusa mutum yayi magana ku kwashe masa albarka haka kawai" Goggo ta saki baki ta rafka wani uban salati tana tafa hannu ta ce. "Rakiya kin jimun salawaitun da Ado yake gaya mun, yanzu tunda muke mun taɓa kwashe musu albarka yaron nan zai sako salawaitun ƙarya ido biyu" Inno ta kalli Ado sheƙeƙe ta ce. "Hansai kece baki da zuciya tun da kika fito bakiga ɗiban albarkar da suke yi mun ba, kina gani fa da kika yi magana Halifa shiru yayi miki, ki barsu wallahi tarasu nake yadda suka kwashemun albarka sai na tara iyayensu sannan zan kwashe musu albarka da hujja." Ana cikin haka Nusaiba ta fito shirye cikin doguwar rigar atamfa tayi kyau sosai gaisawa sukayi da Adam ta wuce ɗaki ta ɗauko Jaririnta ta fito, Inno na haɗa ido da Jariri ya zaro mata ido yana juya idanunsa sama har wani zaro harshe yake, Halifa miƙewa yayi ya ce. "Inno zamu je kai yaro allura ba daɗewa zamuyi ba zamu dawo." Inno ta saki kabara ta miƙe tsaye ta ce. "Wallahi ko ubanka Salisu bai isa ya hana inbiku asibitin nan ba, Saboda Allah Hansai uban yarinyar nan ba amanarta ya damƙa manan ba? yanzu idan aka kwana biyu aka ga rashin ɗa'a ya bayyana a jikinta wa za' a zaga kina ganin uwarta da ubanta zasu yafe mana? A'a ni bangaji cin amana ba idan ka ga nayi nesa da Nusaiba tayi arba'in, amma baza'ayi haka dani ba ƙafarku ƙafata" Halifa zaiyi magana Adam yace.

"Brother samun kwanciyar hankalinka ku wuce kawai dan waɗannan tsofaffun kasan babu tuggun da bazasu iya haɗa maka ba" Halifa ya juya ya watsawa su Inno harara, Goggo ta ƙarasa tana dungurewa Ado kai ta ce, "Aniyarka ta bika bazamuga tuggu a rayuwarmu ba Batulu ce zata ga tuggu ganin idonta, sakarai mu zaka nunawa salawaitun iskanci da tijara" daga Halifa har Adam babu wanda ya kula su Goggo Adam ne ya fara wucewa Halifa da Nusaiba suka rufa masa baya, Inno da Goggo suka fito kowacce da hijabinta a hannu.

Adam yana fita ya ɗauki mashin ɗinsa ya fice, Goggo da Inno bayan mota suka shiga Nusaiba ta shiga gaba sannan Halifa ya tayar da mota suka nufi asibitin AMINU KANO TEACHINIG HOSPITAL.

Akan titin su na zuwa asibiti a dai-dai wani junction ɗan karota da yake bada hannu ya tsayar da mota su Halifa da ke ƙoƙarin tsallakawa ya bawa ɗaya ɓangaren hannu, Inno ce ta ja dogon tsaki ta ce. "Halifa wane irin ɗiban albarka ne wannan zaka tsaida mota a tsakiyar titi bayan ga sauran motoci cen suna wuce wucewa." Nusaiba ta ce. "Inno baki ga ɗan Karotan cen ne ya tsayar da mu ba?" A hassale Inno ta ce. "Ɗan Karotar banza da wofi da zai tsaida jikana yana tsaka da tuƙi aikuwa me hanani ɗebe masa albarka a duniyar nan sai ya shirya" Inno na gama magana ta buɗe murfin mota ta fice Halifa yana ƙwala mata kira ko waigensa batayi ba, tana fita kai tsaye ta wuce gaban Ɗan Karota ta warce katakon da ke hannunsa ta buga masa a baya cikin masifa ta ce. "Kaci ƙwal ubanka yau ba sai gobe ba sai na kwashe maka albarka a gurin nan" 

_INA FATAN ZAKU SAMBAƊO RUWAN COMMENTS KU DUBI ALLAH KARKU NUNA MUN HALIN RASHIN ƊA’A SABODA KU ƊIN ƳAN AMANATA NE BAZAN IYA ƊEBE MUKU ALBARKA????????????????????

UMMOU ASLAM BINT ADAM????
[20/10, 15:48] Ameera Adam????: FIRST CLASS WRITERS ASSO☀️

{Home of qualities and trusted writer’s of The nation}
https://www.facebook.com/groups/856755331683130/?ref=share

         ???? JARIRI  ????

Labari da Rubutawa: AMEERA ADAM

SADAUKARWA GA ƳAN GROUP ƊINA NA AMEERA ADAM FANS GROUP

       GARGAƊI 

BAN YARDA A SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.

    13&14


 A firgice Ɗan Karota ya ja da baya saboda cikin shammata Inno ta warce katakon da dukan da ta kai masa, sai da ya kuma yin nesa da Inno sosai sannan yace. "Iya lafiya me yake faruwa?" Inno ta kuma tsuke fuska tana gyara tsayuwarta ta ɗaga katakon sama ta kuma cewa. "Ubanka kayi mini! Ni zaka gwadawa ɗiban albarka ido biyu? Uban me jikana ya yi maka da zaka tsayar da shi ko hassada kawai da ƙyashi saboda ka ganshi da shirgegiyar mota, kai kuma kana fama da maras ɗa'ar tsalan wando kamar tazuge. To ahir ɗin ka jikana ya fi ƙarfinka ya sha tabara ya sha yasin kurwarsa kur aniyarka ta faɗa kanka sakarai maras ɗa'a" Ɗan Karotan sai a lokacin ya waiga ya hango motar Halifa da yake ƙoƙarin fitowa, haushi ne ya fara kama shi ganin yana bakin aikinsa ana shirin yi masa karan tsaye, matsowa ya yi gabda ita yace. "Me zanci da jikan naki ko ce miki akayi ni maye ne, kece baƙuwar mota wayasani ma ko duk zuri'arku shi kaɗai ne me mota, amma wallahi ina gargaɗin ki idan kika ƙara buga mini wannan katakon sai na shemeki a gurin nan, sai dai duk abin da za'ayi ayi shi. Ban da ma an rainawa ma'aikacin ɗamara hankali har wata figaggiyar tsohuwa ta isa ta kai hannu jikina." Inno na jin haka ta ɗaga katakon ta kuma sauke masa a ƙeya tana cewa. "Kaci Mai garinku ko uwarka ta isa ta ce mun figaggiyar tsohuwa bare kai saboda rashin ɗa'a, kai wallahi da ba dan ina da zuri'a ba da na kwashe maka albarka kowa ya huta. Amma wallahi bari a kira mini Salisu sai ya kira maka hukuma sun kwashe har danginka"  a hassale Ɗan Karotan ya taso da niyyar sheme Inno da sauri Halifa ya shiga tsakani, dukan da Ɗan Karotan ya kai masa ba ƙaramin shigar Halifa yayi ba har sai da ya yi taga-taga kamar zai faɗi, da gudu Inno ta jefar da itacen hannunta ta faɗa kan Halifa tana kuka tana cewa.

“Jama’a ku kawo mini agaji Ɗan Farota zai kashe mini jika ba gaira babu dalili saboda ɗiban albarka. Wayyo Allah Halifa dan Allah ku ceto mini shi tun kafin na kwashe Ɗan Farota albarka ya bi duniya ya ɓalɓace”

A dai-dai lokacin Nusaiba da Goggo suka ƙarasa wajen, Goggo kutsawa ta dinga yi cikin mutane har ta isa wajen da Ɗan Karotan yake cikin masifa ta ce. “Kai Ɗan Tayota kake kowa? Wani sabon salon salawatin rashin imani zaka gwadawa ƴar uwata, wallahi me rabani da kai yau sai ya shirya duk kuwa salawaitin haƙurin da za’a bani.” Goggo kamar wata ƴar dambe haka ta ɗage hijabi, kicici-kicici ta fara kaiwa Ɗan karota duka har wani nishi take tana ja da baya, ita a dole zata rama abin da aka yi wa ƴar uwarta. Ɗan Karotan na ganin haka ya wawuri Goggo ya cukwikuyeta cikin hijabinta ya turata ciki ɗan gidan da suke shiga idan zasu bayar da haannu. Goggo cikin tashin hankali ta fara rafka salati tana cewa. “Jama’a ku kawo mana ɗauki zai halaka mun nida ƴar uwa da Salawaitin rashin imaninsa, ku agaza mana mutane ko bakwa ji na ne? Ku zo ku fiddani zafin ƙarfe sai gasani yake”

Kafin wani lokaci tuni titi ya kacame da mutane yara da manya, wani mutum ne ya ƙaraso ya fito da Goggo da take nannaɗe a Hijabi a cikin ɗan akurki, tana miƙewa ta fara raba idanu tana neman Inno domin su gudu, banda gumi babu abinda take sharɓawa saboda wahala. Mutanen da abin ya faru akan idanunsu suka fara bawa Ɗan Karotan baki suna bashi haƙuri, waɗanda basu san yadda abin ya faru ba suna ta zaginsa.

Duk sun yi carko-carko sai hayaniya ce take tashi sama-sama, Inno na gurin Halifa tana ta subuaɗiɗin zance. Halifa bai bi ta kanta ba ya fisgi hannunta ya wuce mota da ita, Nusaiba da Goggo ma suka rufa masa baya suka koma mota, Goggo saboda sauri har tuntuɓe take yi, suna shiga cikin Motar ya saka maka lock. Da gudun gaske ya figi motar suka wuce sai da sukayi tafiya me nisa sannan Halifa ya yi parking ɗin motarsa a gefen hanya.

Da ka kalli fuskar Inno zaka fahimci tana cikin ɓacin rai saboda fuskarta ta yi murtuk, Halifa ne ya fara magana cikin ɓacin rai. “Saboda Allah Inno yanzu abin da kuka yi kun kyauta kenan? Wai dan Allah wacce masifar ce tasa bazaku barmu mu kaɗai mu kai Ɗanmu asibiti mu dawo ba? Yanzu ki duba abin da kika yi mana da banje na shiga tsakaninki da Ɗan Karotan nan ba wayasan iya abin da zaiyi miki? Sai kace yau kika fara fita maganar gaskiya ni na gaji wani ne yake auran mata ta da za’a dinga mun bita da ƙulli haka kawai, ni mahaukaci ne bansan hukuncin da addini ya gindaya ba game da matar da bata da tsarki ne? Gaskiya na gaji zan yi wa su Daddy magana idan mun dawo, haka kawai tsofaffi ku dinga kaja mun kai, yanzu da ya lahanki wa kika jazawa idan ba su Daddy ba su yi da kuɗinsu da aljihunsu amma ku komai aka faɗa mutum baisan me yake yi ba sai ku.” Inna na gama jin haka bata furta komai ba ta rushe da wani irin matsanancin kuka harda majina.

Halifa haushi ne ya kuma kamashi ya kalleta da gefen ido yace. “Ba kuka ba ko kukan jini zakiyi Inno sai kun bar mini gidana ke da Goggo.” Goggo leƙowa tayi da niyyar yi wa Halifa masifa suna haɗa ido da Jaririn Nusaiba dake hannunta ya washe mata baki yana gyaɗa kai, ganin ya miƙo hannu yana niyyar taɓa haɓarta Goggo da sauri ta ja baya tana faɗin.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12Next page

Leave a Reply

Back to top button