Uncategorized

SAMEEHA P

????SÂMÊÊHÂ????_*

            (P)

“”Do so tabarmar dake cike da maza dam sukayi a ɗan risine momy ta shiga gaisawa da jama’a haɗe dayi musu gaisuwa gaba ɗaya jama’ar suka amsa suna mai yiwa Sameeha gaisuwa da ban baki akan haƙurin rashin abba da kowa yayi,ban da kuka babu abinda Sameeha keyi har wani shassheƙa take hawaye na ambaliyi daga idanuwan ta har suka nufi cikin gidan kai tsaye.

      Mona na ɗakin Umma taji an ɗauki yiwa Sameeha gaisuwa da gudu mona ta miƙe ta fito ta rungume Sameeha gaba ɗaya suka kuma dasa wani sabon kuka a tsakar gidan gida ya kuma kicimewa da koke koke musamman da ita umma ta fito gaba ɗaya suka rungumo ta suna kuka suna kiran Abba umma dake basu haƙuri ita ma ta fara share hawaye wani na kuma sako mata Momy ma da ke gefe matsa ƴar ƙwallar take dafe da kafaɗar sameeha tana””


“”Dota haƙuri a ke yi ana yiwa mamaci Addu’a kowa da haka zai tafi duk jiran lokacin mu  muke kuyi haƙuri Addu’arku Abba ke buƙata ba kuka ba kinji ke ce babba kiyi haƙuri dan Allah ki dena kukan ya isa haka nan ɗiya ta.


nan jama’a suka amshi batun aka shiga lalaɓa su Sameeha da mona da ƙyar mona ta iya haɗiye kukanta amma idanuwan ta basu fasa fitar da ƙwalla ba Sameeha kuwa jin momy ta ce tayi shiru taja bakin ta tayi tsit sai mis mis da baki takeyi azumar Addu’a bata ma san me take furta wa ba idon nan ya kumbura yayi jajir dashi???? 


*INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIRRAJU’UN,Allah a baki a zuci kuma babu Allah kwata kwata momy aranki????*


Mona ce riƙe da hannun Sameeha kamar wace zata gudu ta barta duk inda momy tayi Sameeha zata bita haka mona ma har umma tayiwa momy iso zuwa ɗakin da take zaune da sauran ƴan uwa da abokan arziƙi,momy ta dubi umma ta ce”


   “ƴar uwata ayi haƙuri rashin zuwan Sameer wlhy bashida lafiya amma insha Allah………Umma ta dakatar da momy da”Haba momy nasan bashida lafiya maimuna duk ta faɗa mana halin da yake ciki a yau ɗin nema Abba yake faɗin in yadawo zamu zo mu dubashi ashe ma Abba ba mai dawowa bane,Umma ta share ƙwallar data cika mata ido momy ta karɓi maganar da”



Allahu Akhubar kana naka Allah na nashi kai duniya Allah yasa mugama dake lafiya.


ɗakin ya ɗauka da.



“Amin.


Har kusan yamma Momy ta kai a gidan ana amsar gaisuwa da ita duk wasu kayan abinci da nasha ruwa komai sai da momy tasa aka aje a gidan su Sameeha a cewar Sameer ne ya kira ta yace gasu nan ya turo a kawo, kowa yayi mata godiya banda yaya jummai da ko kallon kirki bata dubeta dashi ba sai wata harara dake haɗasu da zaran sunyi ido biyu da momy gaba ɗaya hankalin momy ya koma kan yaya jummai har yaya jummai ta ƙosa da kallon da momy ke nata ta zarowa momy ido haɗe da miƙewa tsaye ta bar cikin ɗakin gaba ɗaya.

    momy ce ta buƙaci ko zasu koma da sameeha gida a ranar mona ta fashe da matsanancin kuka haɗe da roƙon momy ta bar mata yaya sameeha ta har ayi bakwai sai ta koma idanun mutane yasa momy amincewa tayiwa kowa sallama haɗe da miƙawa sameeha kuɗi ko za’asiya wani abu,hankalin umma ne ya koma kan Sameeha ganin wata muguwar rama da tayi gashi gaba ɗaya ta chanja a yanda take a da ko magana batayi daga umm sai aa ta takure kanta kamar bata san kowa ba har yaya jummai sai da ta lura da hakan ta ja sameeha gefe ta tambaye ta yaya zaman nasu sameeha tayi shuru duk juyin duniyar da ya jummai tayi ta magantu abin yaƙi tira a dole yaya jummai ta barta ta zuba mata ido tana kallon ta.


     momy na barin gidan da wasu awanni zazzaɓi me zafi ya rufe sameeha har karkarwa take tana sambatu maganin zazzaɓi aka siyo da sauri aka ɓalle aka bata,sameeha na haɗiyewa ta dawo dashi nan fa amai yace bisimillah gaba ɗaya hankali ya tashi asume aka kwashi sameeha aka nufi asbiti mafi kusa da gidan ya jummai ce a riƙe da sameeha sai yaya asabe da mona dake ta faman kuka tana Addu’ar Allah yasa ya Sameehan ta ba mutuwa tayi ba.



  cikin kulawa likita ya karɓe su gadan gadan aka shiga bawa Sameeha taimakon gaggawa da fari likitan ya tambayi dalilin faruwar abin daga bisani ya sake dawowa ya tambayi ya jummai sameeha budurwa ce ko kuma matar aure ce?


jiki a sanyaye ya jummai ta ce”


“Amarya ce ko wata biyar batayi ba.


likitan ya saki ɗan murmushi haɗe da””



“”Masha Allah ku ɗin ya ya kuke da ita?


kaga malam sai tambayoyi kake mana har da wani murmushi kasan me yake damun mu zaka ringa mana dariya shin dariya mukazo kayi mana ko,ko duba mana yarinya?


gaskiya ne ya jummmai ko farfaɗowa bamu ga ƴarmu tayi ba sai yaƙe mana haƙora kake yi kana mana tambayar rainin hankali kamar wasa mukazo yi asibiti,cewar ya Asabe.

 




“Dan Allah kuyi haƙuri akan aikina nake banyi hakan da wata manufa ba,sannan tambayoyi danake muku dole ce tasani dan sanin ta inda zan faɗamuku matsalar ƴar ku kuma Alhamdulillah naji daga bakin ku ƴa take a wajanku to albishir gareku ƴarku ba wani abu bane yake damun ta ilah *JUNNA BIYU* dake tare da ita.


yo ba sai ga murmushi daga fuskokin su ya jummai ba mona kuwa rungumo Sameeha dake kwance tayi ta kuma sakin wani sabon kuka Aunty asabe ta ce da likitan.


“Dan Allah kayi haƙuri bawan Allah duk hankalin namu ne atashe ga mutuwa ga kuma rashin lafiyar Sameeha.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); likitan yayi murmushi akaro nabiyu ya ce””



babu komai hajiya muna fuskantar irin haka har finsa kuma a halin da kuke dole ku furta haka sannan zaku kula da ita sosai a kan abinci masu gina jiki da ƙarin lafiya da abinsha kar kuma abata ko wane irin magani indai ba likita ne ya rubutashi ba naji kunce kafin ku zo kun bata na zazzaɓi (feaver),dan Allah aringa lura za kuma ta farka insha Allah lafiya lau laulayi sai a hankali komai zai koma dai dai (Normal).



in sha Allahu za akiyaye mun gode likita.


    yaya jummai da Aunty asabe suka furta atare kamar haɗin baki,ba aɗauki dogon lokaci ba Sameeha ta farka daga dogon barcin karku so kuga kulawa da lallama da nan nan da kowa ke mata yaya jummai ce ta sheda mata abinda likita ya furta sai gashi ma yazo ya ƙara duduba sameeha da wasu shawarwarin ga masu ciki da magunguna ya bada sallama bayan sun biya duk (chajis)ɗin da akayi musu sukayo gida,Alhamdulillah ana jimamin mutuwa ga kuma ƙaruwa an samu *KAƊAN DAGA IKON ALLAH*,inji umma kowa yayi farin ciki yabi Sameeha da Addu’a umma ma taji daɗi tabi ɗiyarta da Addu’ar Allah ya sauketa lafiya ya bata zuri’a ɗayyiba,yaya jummai ce ta kasa ta tsare sai an kira momy an faɗa mata umma ta ce Aa ba ayi haka ba cikin fari ai a karanta idan Sameeha ta koma gida sa gani ko suji daga gare ta nan rai yaso ya ɓaci ta inda yaya jummai ke shiga bata nan take fita ba da kanta umma tasa saratu ta kira momy asanar da ita,hakan kuwa akayi an kira momy an faɗa mata murna kamar zata fito daga cikin wayar har kuka tasaka wai Allah ya kawo mata abinda ta jima tana jiran gani ta ƙara da a kular mata da ɗiyarta sosai abata duk abinda take so kar kuma abari ta kuma zubar da hawaye dan Allah.


Saratu ta katse wayar kowa na yaba irin hali na momy suruka me kirki da mutunci ga sanin ya kamata Addu’a da fatan alkhairi momy tasha shi har ta gaji a ranar.


       a ɓangaran momy kuwa tana kashe wayar ta doka ƴar banza da ƙasa tsabar baƙin cike tambayar kanta, ta shiga yi da””

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button