JASEENA COMPLETE HAUSA NOVEL

????bayan shekaru goma sha shida(16 yrs ltr)????
Zaune yake a fadar sa, su waziri sai zuba fadanci ake , wasu maza wad’anda da ka gansu kasan cewa magidanta ne sanye cikin kayan da basu fi a k’ira su da tsumma ba suka shigo fada gami da zube wa ‘kasa suna kwasar gaisuwa duk jikin su sai 6ari yake yi d’aya daga cikin su yace ” Allah ya baka nasara sarki !!! Mun kawo k’arar Yerima !! Ya takurawa y’ay’an mu ko diban ruwa basa iya fita saboda da ya gansu sai ya fasa tulun,shine muk………….kafin ya k’arasa yaji sauk’ar mari Tas!!!! Hakan yasa ya mik’e a firgice yaji an sake kwarfe shi ta k’afa take ya zube ‘kasa warwas !! Sarki ya ja tsaki Mtsew!! Yace ” ni zaku dubi tsabar idona Ku zo min da zancen banza Wai kun kawo karar Yerima? Toh baku isa bah !! Wato har an fara sa mishi ido kenan ? Ina so ku sani ,Rizwan Jini ne na sarauta yana da ikon taka duk wanda ya so kuma babu mai tanka masa ” ya dubi sarkin yak’i yace ” me kuke jira ne Amjad?!!! Aje a rufe min su a kurkuku da kuma horo mai tsananani!! Da sauri sarkin yak’i Amjad ya kama hannayen su ta baya ya tisa ‘keyar su suka bar fada yayinda Jalalud-deen ya koma kan kujerar sa yana maida numfashi kamar wani damisa ????
Sarkin yak’i Amjad yana fita da su yayi hanyar kurkuku dasu ,murya ‘kasa- ‘kasa yace sai dai ku yi hakuri da irin Wannan zalunci da ake muku ni na tabbatar cewa akwai ranar da zata zo idon Jalalud-deen sai ya raina fata kuma sai ya zama wulak’antace a idon jama’a!! Yayi d’an murmushin takaici dai dai lokacin sun iso mashigar kurkukun ya wuce chan ciki da su ,sun dad’e suna tafiya kafin su iso d’akin da za’a sa su ,ganin masu gadin na kallon sa ya sa ya hakad’a su ciki a fusace ,gami da rufo k’ofar ya juya idonsa cike da k’walla ya fice Daga kurkukun…..
????????????????????????????????????????????????????????????????????
Gudu take a kan dokin sanye da bak’in dogon wando mai fad’in gaske ta sama , ta ‘kasa kuma a tsuke,rigar jikinta na cikin dogon hannu ne da shi kuma sak’awa akayi da auduga na saman kuma da fata akayi shi bak’in mayafi ne rataye a kanta wanda har ya zagaye fuskar kamar wanda tasa nik’ab baka ganin komai sai girar ta ,idon ta da kuma saman zirin karan hancinta , takalmin k’afarta ma na fata ne ,ta rataya wata y’ar jaka a jikinta sai wani dan biri da ke zaune a kafad’ar ta yana ta fama da ayaba????…..
” Hyaaaa!!!” Ta fada gami da bugan dokin ta baya ,yayin da shi kuma ya kara gudu. Sun dad’e suna tafiya kafin su isa mashigar garin tana isa ta sauk’a daga saman dokin ta kama linzamin suka ci gaba da tafiya basu zame ko ina ba sai kasuwar garin nan ta wuce gun wani mai saida ganyeyaki na magani ta mik’a masa jakar , ya karba ya Ciro kad’an daga ciki ya shinshina sannan yayi murmushi ,yace ” yayi kyau Jaseena !! Wannan na’a na’a mai kyau ne !! Ya sa hannu cikin aljihun shi ya Ciro sulalla ya muk’a mata ta kar6a ta juya abunta ba tare da ta ce k’ala ba ……..
Cikin kasuwar ta sake kutsa kai tana ganin yanda Kowa ke gudanar da alamuran sa cikin kwanciyar hankali ,kai tsaye ta nufi gun mai shinkafa ,ya auna mata ta kar6a kawai ta jiyo hayaniya bata ankara ba ta hango dawakai kusan biyar sun dumfaro inda suke ,da wasu matasa a kai sai 6arna suke ,guda daya daga cikin su ya sha ado da kaya irin na alfarma shi ya fi Kowa ma ta’adi a cikin su suna ta buge mutane ,suna zubar musu da kayayyaki ,ta gefen Jaseena suka wuce gami da banke wata mata mai juna ta fad’i ‘kasa kayan marmari da ta siyo ma duk suka zube ,a fusace Jaseena ta dubi mai shinkafan tace “Wannan kuma su waye haka kamar mahaukata ??!!! Mai shinkafa ya zaro ido yace ki rufa ma kanki asiri baiwar Allah!! Wannan shine Rizwan d’an sarki Jalalud-deen !! Ta juya ta sake kallon hanyar da suka wuce tana wani irin murmushi na k’eta ” a ranta tace lallai yau kakarta ta yanke sak’a!!! Mai shinkafa ya ce ” amma baiwar Allah kina garin nan kice baki san Yerima Rizwan ba? Murmushi kawai tayi ta d’auki shinkafan ta sa a Jakarta ta juya ba tare da ta kalle shi ba balle ma ta bashi amsa ,ta nufi gun matar da ta fad’i kasa wanda duk an zagaye ta ana kallo kuma babu wanda ya ma je kusa da ita don ya taimake ta…………….????
Jeeddah ja’o????
[3/3, 10:16 PM] Jeeddah ja’o????: ⚔????JASEENA????⚔
????????jeeddah ja’o????????
1⃣6⃣⏭2⃣0⃣
Kutsawa tayi cikin taron mutanen da k’arfin hali ta samu ta shige inda matar take ta d’aga ta tana yi mata Sannu yayinda sauran mutanen suka watse daga gurin Kowa ya fara tattare 6arnar da akayi masa amma da ka gansu kasan a tsorace suke duk da Jaseena ta fuskanci hakan bai sa ta ko girgiza ba ta d’aura matar kan dokin ta sannan ta ja akalar dokin suna tafiya matar na mata kwatance har ta kaita gidan ta, ta kuma taimaka mata har cikin gida ,wanda ba girma gareshi ba amma sai tsafta ,wani gadon kara ne gefe guda ta hango ta ja matar har gurin ta zaunar da ita sannan ta tashi ta nufi d’ayan 6angaren gidan don nema wa matar ruwa, akayi sa’a ta samu ta d’ebo mata….
Bayan ta tabbatar matar ta samu nutsuwa sai ta tashi zata fice ,hannun ta matar ta rik’e ta ce ” nagode baiwar Allah !! Amma yaya sunan ki ? Ta juyo da murmushi tace ” “Jaseena ” matar ta d’an jinjina kai ta ce ” amma ke bakya tsoro labari yaje kunnen Yerima Rizwan cewa kin taimaka wa wanda ya wulak’anta? Zai ce kin raina mar hankali ,sannan ya sa a miki horo mai tsanani ,kuma gashi ke yarinya ce bai kamata kina k’arama ki jefa kanki cikin had’ari ba !!! Murmushi kawai Jaseena ta sake yi tace ” Kar ki damu umma !! Ni ma ba kanwar lasa bace !!!in yana ji da sarauta nima ina ji da ita !!???? ke dai ki kula da kanki kuma ki daina fita ke kad’ai domin hakan ba k’aramin had’ari bane” tana kai Wannan ta juya ta fice gamida rufo k’ofar gidan ,matar ta bita da kallo ,a ranta tace ” yau naga mace mai kamar maza!! Yanzu har a masarautar Kalahari akwai macen da zata iya tsallake dokar Yerima ?? Ta girgiza kai ta koma ta kwanta.
???? kasuwar ta k’ara komawa ta gama saye-sayen da zatayi sannan ta juya ta bar garin , da la’asar ta isa kogon su ta shige ta nufi inda tasan kullum mahaifan ta yake motsa jiki da yamma ,wani d’an fili ne ya zagaye da itatuwa a nan ya ke koyawa Jaseena dabarun yak’i ,da gudu ta nufi inda yake ta zari wani sanda suka fara fad’a cikin raha har suka gaji suka bari.
????wuta suka hura tana taya shi gasa kifi sai zuba take yi don duk abunda ya faru a Kalahari sai da ta zayyano masa shi dai bai ce ‘kala ba ya ci gaba da gasa kifin ,ganin ba sauraron maganar ta yake ba ta mik’e ta nufi wata duhuwa mai siriryar hanya ,gaba kad’an ruwa ne ke sauk’a ta saman dutse birin ta wanda take k’ira da suna Zainu yana nan kan kafad’ar ta yayinda take Kutsawa cikin duhuwar ???? kukan damisa ta jiyo hakan ya sa ta wata Yar siriryar dariya ta kama wata reshe kamar biri tana lek’o inda taji kukan ,domin takan ji kukan ne tun tana Yar yarinya amma bata tab’a yin gaba da Wannan gurin ba kasantuwar daga Wannan dutsen mai ruwa babu wani guri a gaba balle ta ce ko daga chan ta jiyo k’ara. yau de ba Jaseena bace zata fita ,mahaifin ta Hameed ne zai fita duk da ranta bai so ba amma tasan bata isa hana shi fitan ba ,kamar kullum ya debi ganyeyaki a jaka ya ja Zabil suka fice …..tana cikin wasa da zainu su kama Wannan reshen su saki wancan Kwatsam ta sake jin Wannan kuka na damisa ,ai kuwa nan ta k’udiri niyyar sai ta gano duk inda Wannan ‘kara ke fitowa !!! Diro wa tayi daga saman bishiyan tabi hanyar da ta jiyo karan kamar kullum de bakin dutse take riskar kanta amma yau tace bazata juya ba sai taga menene a bayan ruwan da yake zuba kuma zata nemo inda Wannan damisa take