HAUSA NOVEL

JASEENA COMPLETE HAUSA NOVEL

Wani d’aki ya nuna mata ta sa hannu ta bud’e ta shiga da murmushin ta zainu na biye da ita ,shima murmushi yayi sannan ya juya ya fice daga wajen yayinda ta bishi da kallo kamar Yar k’auye.

????????????????  ????????????????

Yau kwanan Jaseena uku a Wannan gari wanda ko ita kanta bata san sunan garin ba ,Haidar kuwa kusan kullum da safe sai ya lek’o don ya duba lafiyar ta ,haka take wuni ita kad’ai sai zainu yana d’ebe mata kewa kasantuwar Haidar bai cika dawowa da wuri ba in ya dawo ma sai gari ya waye yake duba su….” Yau kam sai na fita na zaga gari!!” Cewar Jaseena kenan tana ta faman gyara zaman dogon rigar da ta saka ,sai duba kanta take ta madubi don bata saba saka irin kayan nan ba ,ita kanta ya mata kyau ,sannan ta dauki mayafin wanda da shi da kwalin tata duk d’aya ta yafa a kanta ta nannand’e ta fice zainu na binta a baya kamar yadda ya saba , tana tafiya tana faman tattare riga don yadda yake Jan ‘kasa a haka har ta bar fada ,tana ta kalle kalle ta tsaya can ,ta ta6a wancan , tana cikin haka har tayi nisa da masarautar a can nesa ta hango wasu mata guda uku kowacce da tulu sun sha ado sai ture -turen juna suke a kan hanya suna ta raha……

Cikin sauri Jaseena ta k’arasa inda suke ,tana iskesu ta sa hannu ta ta6a kafad’ar daya daga cikin su duk suka juyo suka k’urawa Jaseena ido sai kuma suka bushe da dariya suna nuna ta da yatsa ???????? hakan yay matuk’ar bawa Jaseena haushi ta yamutsa fuska tace ” toh me nayi kuke min dariya !!????. A tare suka tsare kamar da gaske sannan suka sake bushe wa da dariya ,wata Yar siririya sosai tace ” ke kuma Wacece haka !? Ko rigar ma bata iya sak’awa ba Yar k’auye kawai!! Suka juya suka ci gaba da tafiya yayinda ita kuma Jaseena ta tsaya Kallonsu har suka shige ta daina hango su ma……………????

????Jeeddah ja’o????

[3/18, 9:58 AM] Jeeddah ja’o????: ⚔????JASEENA????⚔ 2016

????????jeeddah ja’o????????

3⃣1⃣⏭3⃣5⃣

Duk Wannan abun da ya faru Haidar na tsaye yana kallon ta ,shi ma kanshi ta bashi dariya kawai ya tsare ne,kwata – kwata rigar baibai ta saka shi bayan haka kuma gaba a baya ,duk da hakan da tayi yay matuk’ar yi mata kyau amma ba daidai bane shi yasa matan ke mata dariya….

????Nan ta nemi k’ark’ashin wata y’ar bishiya ta zauna tana ta 6ata rai harda d’an hawayen ta ,tace ” ai yanzu da baba ne bazai min dariya ba cewa zai yi yayi min kyau !! Toh ma miye laifin kayan nan tunda dai ba tsiraici na bari a fili ba!!!Mtsew!!!” Take ta zabura ta mik’e tace” Baba!!!”

????????????????????????????????????????????????????????????????

Kwance yake cikin wani matsatsen d’aki mai duhun gaske duk ruwan datti ta nan yake biyo wa ,ya tashi ya mik’e tsaye sai kai kawo yake a d’akin yana cizon le6e ,duk tunanin shi ya koma kan y’ar sa Jaseena addua kawai yake yi Allah ya sa Kar su gano ta ,Allah yasa basu kamata ba duk da yasan k’arfin damtse na y’arsa da kuma wayo irin nata. ” HAMEED!!! K’iran da waziri Zakar yayi masa kenan , hakan ya sa shi juyawa cikin sauri fuskar shi a d’aure. ” kamar yadda muka kamoka kamun wulak’anci haka zamu kamo d’iyar ka da kake tak’ama mai k’arfi ce mu wulak’anta ku a bainar jama’a !!! Hhahhah !!!!! ” Zakar kenan yayi Wannan magana ,bai ankara ba yaji an shak’e wuyan shi har saida idanuwan shi suka fito kwala kwala ,ya kasa magana. Hameed kenan !! Yana cikin kurkuku ma amma k’arfi na nan !!????????. Wasu masu gadin gurin su biyu ne suka tunkari inda suke da ‘kyar suka cire waziri daga rik’on da Hameed yay masa sukayi waje da shi ,yayinda shi kuwa gogan ya koma ya zauna yana maida numfashi ????………….

????.  ????

A tsayen da take tana tuna halin da mahaifin ta zai shiga a Kalahari taji durowar abu ta bayanta tuni ta zari wata y’ar wuk’ar ta ta juya zata kai hari ,hannu ya sa ya tare ,wuk’ar ta yanke shi a hannu. Tana juyawa taga ashe Haidar ne ????ta zare ido,a rikice ta cire gyalen da ta rufe

kanta ta raba gida biyu ta d’aure masa yankan da tayi sai bashi hak’uri take yi ,ga dukkan alamu bai ji zafin ciwon ba sai murmushi yake mata ,jiki a sanyaye ta nemi guri gefen bishiyar ta raka6e tana y’ar hawaye….

Wata murya mai dad’in gaske da ratsa zuciyar duk wani mai sauraro taji yace ” Jaseena!! Ai barin kashi a ciki baya maganin yunwa ,inaga lokaci yayi da zaki sanar da ni matsalar ki wata’kila na nema miki mafita ko in taimaka miki!! Kinga dukkan mu nan ko wanne yanada matsalolin da yake neman mafita amma 6oye su bazai amfane my da komai ba har lokaci ya k’ure mana !! A firgice ta juya tana neman inda akayi maganar amma ta rasa domin ta lura babu Kowa a gurin sai Haidar da har Lokacin murmushi kawai yake yi rik’e da hannun shi yana kallon ta da kuma mamakin yadda ta rikice tana neman wanda yayi magana………

Ta dawo gaban Haidar tana kallon cikin idon shi tace ” bakaji wani yayi magana ba ? Baka ga wanda yayi ba?” Murmushi ya sake yi sannan yace ” ni nayi miki magana Jaseena !!” Nan ta tabbatar tabbas shi ne yayi magana ,kafin ta ce komai ganin yadda ta saki baki kamar wawuya yasa ya fisge hannun ta yabi wata hanya da ita sai cikin wani daji dake gefe da gurin ,kan wani gungume ya nuna mata ta zauna ,yace ” eh nine nayi magana ! Kuma ke kad’ai ne kika san hakan ko sarki bai sani ba ,kuma ina so ki rik’e shi a zuciyar ki ,duk Lokacin da kike buk’ata muyi hira to kizo nan amma Kar ki kuskura wani yasan ina magana !” Kai kawai ta girgiza mishi cike da mamaki har lokacin ta kasa nutsuwa…,……….????

????Jeeddah ja’o????

[3/19, 12:16 PM] Jeeddah ja’o????: ⚔????JASEENA????⚔ 2016

????????jeeddah ja’o????????

3⃣6⃣⏭4⃣0⃣

“Dama kana magana ne?” Shine tambayar da ta fara fita daga bakin Jaseena. Haidar yayi wata Kyakkyawar dariya yace ,ina magana amma banda iyayena babu wani mahalukin da yasan hakan ko sarki Hasheem da kika gani bai sani ba ,duk da shine silar dawowa ta hakan !! Duk Wannan maganganu da yake yi babu abunda Jaseena ta fahimta duk ya dagula mata tunani , Ta mik’e tace in na fahimce ka ,kana so ka ce min kai ba d’an Wannan sarkin bane ? Kuma akwai abunda kake 6oye masa a matsayin sa na wanda ya yi rainon ka?

Wata dariya ya saki mai ban mamaki yace ” Jaseena duniyar tamu zagaye take da azzalumai masu bak’ak’en zuciya da son abun duniya !! Zan baki labari na da kuma dalilin da yasa na zama haka ,amma kafin na baki labari ina so ki min alk’awari babu wanda zai san ina magana a cikin masarautar nan ko da wasa ne! ” Jaseena ta furzar da iska daga bakinta tace ” inshaa Allah bazan bari Kowa ya san da Wannan zancen ba !! Sirrin ka zan killace shi kuma na bashi mazauni na musamman a zuciya ta !!” Murmushi yayi yace na gode !! Amma yanzu muje in nuna miki gari ,gobe zan sanar da ke tarihi na in Allah ya yarda ” Jaseena ta d’an 6ata rai tace” me yasa bazaka fad’a min yau ba? ” murmushi kawai yayi yace ” muje ” ya tashi ya mik’e ita ma tabi bayan shi har ta sa k’afa zata tafi sai tace ” kai ka je !! Ni zan gyara riga na, ba tare da ya tanka ba yayi tafiyarshi ita kuma ta juya rigan ta gyara tsaf sannan ta fito daga duhuwar da take …

Tsaye ta same shi a gefen Wannan bishiyar yana jiranta ” na gama mu tafi” shine maganar da ta ratsa kunnen sa ,ya juyo ya k’ura mata ido kamar ya had’iye yace ” muje” ya fara tafiya ta bi bayanshi sai fama da doguwar rigar takeyi duk ta mata nauyi ta tattare rigar har guwiwa hakan yasa ta bata sauri sai ta d’an ruga ma take iske Haidar duk da ya ga yadda take fama da rigar wanda hakan ya bashi dariya matuk’a amma ya kafse kamar bai san ma tana yi ba .

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button