JASEENA COMPLETE HAUSA NOVEL

⚜kasuwar garin ya fara kai ta ,sai kalle kalle take yi ,Kwatsam ya bi da ita layin sayar da tsuntsaye ,su Jaseena an samu abun yi ,nan ta dinga bin keji keji tana ta dariya kamar pagal (mahaukaciya) shi dai haka yake a tsare sai tafiyar shi yake in taga yayi nisa sai ta sa gudu ta taro shi ,ga shegen surutu kamar aku ta sha gaban shi yana tafiya ita kuma tana tafiya da baya baya ,” kai nace ka d’an tsaya mana sai sauri kake yi ko baka ji na ne!! ? A garin ja da baya ta banke wata budurwa ta d’ebo kwai a kwando ta fad’i k’asa kwayayen suka fashe ,a gurin ta daskare ta kasa magana ,budurwar ta mik’e tana karkad’e jikinta yayinda Jaseena ta sunkuya tana kwashe mata wayanda basu fashe ba sai hak’uri take bata. Murmushi yarinyar tayi tace ” babu komai !! Ba kece wadda muka gani dazu zamuje deban ruwa ba?” Jaseena ta d’an d’aga kai alamar tunani tace “???? ” Eh nice !! Ina sauran guda biyun suke?” Yarinyar tayi murmushi tace suna can gida ni sunana Jauda , ke kuma fa?” Ni kuma Jaseena! Shine amsan da Jaseena ta bata .
Ta juya sai dube dube take yi bata ga Haidar ba murya can k’asa tace “toh shi Wannan ina ya tafi ne?!” Murmushi Jauda tayi tace ” tun yaushe ya tafi!! Kizo mana mu tafi tare zamu nuna miki cikin gari ni da yan uwa na !” Da ‘kyar Jaseena ta yarda ta bi ta suka tafi………….
????Jeeddah ja’o????
[3/21, 9:24 AM] Jeeddah ja’o????: ⚔????JASEENA????⚔ 2016
????????Jeeddah ja’o????????
4⃣1⃣⏭4⃣5⃣
Suna tafiya tana mata hira har suka isa wani babban gida ,ginin mai tsayi ne sosai ga kyau kuma tare suka shiga kai tsaye hanyar d’akin girke -girke suka nufa yarinyar ta ajiye kwandon kwai din ,a d’ayan 6angaren kitchen din kuma wayannan yan matan nan ne da suka mata dariya tare da Jauda suna tsaye sun zuba musu ido ,d’ayar tace ” ke!! Benaxir fa ta dawo !!! Kika shigo da Wannan bakya tunanin zata iya 6ata miki rai in ta ganta ko??!” Murmushi Jauda tayi sannan tace ” babu komai Aisha ai zamu fita ta baya in Mun gama aiki !!” Aisha de bata sake tanka mata ba ,Jaseena tace ” Wacece Benaxir har kuke tsoron ta haka ? D’ayar da tun farko bata tanka mata ba tace ” Wannan bai shafe ki ba !!:roll:” a tare Jauda da Aisha suka daka mata tsawa gami da k’iran sunan ta Meenah!!! Wai ke me yasa bakya son mutane ne kin cika bak’in hali !!? ” Aisha ce ta k’arasa maganar……
Jaseena tayi murmushi tace ” ni zan koma ,nagode da kyautata wa da kuka yi min ” Aisha tace don Allah ki tsaya mana yanzu zamu gama aiki mu tafi fada ,yau akwai tseren doki a fada kuma Kowa zai halarci gurin domin fidda gwani a wajen sarrafa doki ,kuma fa har akwai fad’a da zaki ,kowacce shekara yarima Haidar ke gaba a duk fannin.!! Kinsan yarima Haidar da son mutane ! Ai shine ma sadaukin Wannan masarauta Kowa yana karrama shi ,ba kamar mahaifin shi sarki Hasheem ba ,bai d’auke shi a kan komai ba ,Kinsan Haidar abokin mu ne tun muna k’anana tare muka taso har yanzun nan da kika gani ,ko lokacin da muka miki dariya a hanya ma ai shi ya hana mu in ba haka ba da abun ya fi haka ,ko wacce a cikin mu na da labari mai ban tausayi tun yarintar mu kuma labari mai ban tausayi amma da Sannu zaki san komai amma kafin nan ko zaki iya bamu labarin rayuwar ki da yadda akayi kika tsinci kanki cikin Wannan masarauta ta Ramali?? ”
Nan Jaseena ta kwashe duk labarin rayuwar ta ta fad’a musu har yadda akayi ta fito daga dutsen da had’uwar ta da shi Haidar ,duk sun tausaya mata matuk’a , Jauda ta mik’e tsaye tace ” toh ai duk labarin d’aya ne duk fa akan mulki aka k’ask’anta mu kawai don an fi k’arfin magabatan mu toh yanzu zama zamuyi a dinga cin kashi a kan mu ne??!! Aisha ta mik’e tace ” inaaaa!! A’a Sam bazai yiwu ba dole mu kwace hak’k’kin mu da kan mu mu tashi muyi yak’i mu k’watar ma kammu y’anci!!! ” Jauda ta sa hannu tace ” wa yake tare da ni??” Duk suka d’aura hannayen su a kan nata gami da cewa “ni!!” Duk suka maida dubansu ga Meenah da ko motsawa bata yi ba ,ganin duk sun sa mata ido itama ta d’aura nata hannun” Jaseena ta rasa Wannan wane irin hali ne Meenah take da shi kwata kwata batada fara’a a fuskar ta. A tare suka watsa hannayen sama kowannen su yana murmushi irin na masu k’arfi a jika ????????
???????? Jaseena. ????????
Guri ne babba na gaske amma mutane duk sun cika gurin an zagaye makeken filin wanda Hasken farin wata ya cika shi fal! Gurin da mutanen suke hawa hawa ne ga fitilu nan ta ko ina sun haska benen dake sama sosai shine inda sarki Hasheem ke zaune shi da wata Kyakkyawar mata tasha ado na zinare ,gefe d’aya kuma sarakuna ne da matan su wayanda suka zo suma da y’an wasan su ma’ana sadaukai na k’asar su don suma su fafata a cikin gasar ,akwai gefen sarki Hasheem wanda duk cikin guraren ya fi ko ina k’ayatuwa ,wani sarki ne bashi da haske sosai amma da ka ganshi kasan ya dama ya shanye a sarauta ,gefen shi wani kyakkyawan saurayi ne ya sha ado gwanin sha’awa fuskar shi babu almuru ga dukkan alamu d’an sarkin ne ,ga kuma wani ta bayansu a tsaye da alama sarkin yak’in su ne don sanye yake cikin kayan yak’i saidai ya manyanta sosai don dattijo ne….
Toh masu ku biyo ni a episode na gaba don jin wainar da zata toyu a Wannan fili na gasa ,ina godiya masu karatu love you all!!????
????Jeeddah ja’o????
[3/23, 9:15 AM] Jeeddah ja’o????: ⚔????JASEENA????⚔ 2016
????????jeeddah ja’o????????
4⃣6⃣⏭5⃣0⃣
Haidar ne a kan doki suna Jere shi da wasu ,yayan sarakuna ,Jaseena da ke zaune a bene na farko kuma na k’asa ita da su Jauda kawai ta mik’e ba shiri ,su Aisha ma suka mike suna tambayar ta ko meyasa ta zabura haka? Fuskar ta babu almuru tace ” tabbas na san wancan !! Shine Rizwan d’an sarki Jalalud-deen !!! Me kuma yake yi anan ? Duk yadda akayi sarki Jalalud-deen ma yana nan !!” Aisha tace ” kice ba mu muka je neman su ba su da kansu sun kawo ‘kafar su inda ya dace!!” Duk suka bushe da dariya ,chan kuma sai Jaseena tace ” toh amma ai in an gama gasar yau gobe zasu tafi ko ?” A tsare Meenah tace ” sati biyu ake yi ana wasannin lallai muna da dama ” duk suka jinjina kai ,yayin da Jaseena tayi murmushi cikin ranta tace ” lallai Wannan Meenah d’in y’ar ganin dama ne !!.
Tun da aka fara tseren dawakai Haidar ne ke Jan ragamar Kwatsam sai dokin shi tayi wani irin ‘kara ta tik’a shi da k’asa ta yi gaba ,yarima Rizwan wa wuce shi yana masa wata muguwar dariya gami da cewa “Wannan karon kam baka isa ba!!! ” dokin Haidar da ya fita a guje ya zagayo ta inda su Jaseena ke zaune kawai se ta mik’e tayi tsalle ta fad’a kan dokin ” Hyaaaa!!! ” ta sa gudu ,ganin yadda ta kusa cimma Rizwan yasa sarki Jalalud-deen ya mik’e tsaye yana zare idanuwa.
Gudu suke daf da daf da ita yayinda Rizwan ya kasa mai da hankalin shi kan tseren ,abunka da mayen mata ,ya tsura mata ido ita kuwa ta sakar masa da wata hadaddiyar murmushi wanda ya sa sai da ya kusa tsaya wa. Sai da ta tabbatar ya gama rud’ewa kawai taja linzamin dokin ta kara gudu har ta tsallake Jan layin da aka zana ,ta zo na d’aya ,bak’in ciki ya sa Rizwan ya gagara k’arasawa yayin da idon Jalalud-deen suka rine tsabar haushi ace duk shirin da suka yi na ganin sun ci amma hakan bai yiwu ba?
Mutanen gari aka hau ihu ana Jaseena! Jaseena !! Jaseena!!! ,Wannan sunan da aka kira yasa sarki Jalalud-deen d’agowa cikin sauri yana kallon Jaseena !tabbas babu maraba tsakanin ta da mahaifiyar ta ,saidai a tunanin shi wata’kila idon shi ne ke mishi gizo sai yayi tsaki ya juya ya bar wajen ,yayinda Rizwan da sarkin yak’i Amjad suke taka mishi baya.