JASEENA COMPLETE HAUSA NOVEL

????Jeeddah ja’o????
[3/24, 7:40 PM] Jeeddah ja’o????: ⚔????JASEENA????⚔
????????Jeeddah ja’o????????
5⃣1⃣⏭5⃣5⃣
Haidar kuwa murmushi kawai yayi ya nufo inda take ,kanshi a k’asa yace ” nagode jarumar mata!!! ” Wannan sanyin Muryar tashi ta sa Jaseena lumshe idanuwa tana murmushi ba tare da ta tanka masa ba,shi ma yadda yayi maganar ba wanda zai gane magana yake yi ..
????. Gurin duk an watse Kowa ya koma gida, daga Aisha ,Jauda, Jaseena sai Meenah da Haidar, suna ta hirar su cikin nishad’i Meenah ce kad’ai kamar bata gurin. Jauda tace “Jaseena mu zamu tafi dare na yi sosai Kar Benaxir ta rufe k’ofa Kinsan ba mutunci gareta ba! Nan suka yi sallama suka bar ta da Haidar. Ganin sun share mintina babu wanda ya tanka wa wani yasa Jaseena ta mik’e tana kad’e rigar ta tace ” sai da safe yarima ,idon shi cikin nata yayi mata wani murmushi ba tare da ya tanka ba ,ganin shiru yasa ta juya zata tafi…….
Mahaifina sarki Mahmoud shine mai mulkin Wannan masarautar mutum ne wanda bai yadda ya ci ya sha ba tare da ya tabbatar jama’ar k’asar nan sun wadatu ba kullum burin shi yaga na gefen shi cikin walwala koda shi zai rasa ,hakan ne yasa ya fita daban da sauran yan uwan shi wanda kuma sun kasance ba uwa d’aya suke ba domin shi d’aya mahaifiyar shi ta Haifa kuma halin shi ma babu mai irin sa kasantuwar ,kakan mu mata biyu gareshi…..
Da sauri Jaseena ta juyo ta dawo inda yake ta nemi guri ta zauna don ta jiye wa kunnen ta ……. Yerima Haidar yaci gaba da cewa ” duk mahaifina ne babba a ciki domin mahaifiyar sa itace ta fari daga baya ne zaliha (ta biyun ) ta haifi maza biyu Hasheem ,Hayatud-deen ,da kuma mace d’aya Saleemah. Duk cikin su ukun Saleemah kad’ai ke son baba na don sun shaqu sosai hakan ne yasa tun tana y’ar shekara goma ,mahaifiyar ta Zaliha ta bada ita aure a wani masarauta Wai shi Kalahari aka daura mata aure da d’an sarkin garin yarima Jalalud-deen , wanda hakan yasa bata ‘kara zuwa ko da ziyara nan masarautar ba,Domin shine hud’ubar da mahaifiyar tata tayi mata.
Jin haka yasa Jaseena ta mik’e a razane ta ce ” Kalahari?? Jalalud-deen?!! ” shima Haidar ya mik’e yace “eh! Kin san su ne? Nan ta kwashe labarin rayuwar ta ta fada masa yayinda ya cika da mamaki ” haka Allah yake abin shi!! Shine abunda Haidar ya iya cewa kenan ,ya dubi Jaseena yace “Kin ga yanzu dare yayi ,ki je ki kwanta ki huta gobe in shaa Allah zan sanar da ke dukkan labari na. A nan suka rabu da alkawarin zai sanar da Jaseena komai game da shi washegari……………..
????Jeeddah ja’o????
[3/25, 12:20 PM] Jeeddah ja’o????: ⚔????JASEENA????⚔
????????Jeeddah ja’o????????
5⃣6⃣⏭6⃣0⃣
Tafiya take tana ta fama da y’ar doguwar rigar ta ,tazo wucewa ta gurin fada kenan taji kamar maganar mutane,ta d’an lek’a daya daga cikin tagogin fadar don taga su waye a fadar cikin Wannan dare. Tana lek’a wa idanuwan ta suka yi karo da sarki Jalalud-deen da kuma sarki Hasheem suna tsaye ,koda ta kasa kunne don tajiye wa kunnen ta abunda suke shiryawa……
” Ai Wannan ba komai bane ni a gurina domin a kan sarauta babu abunda bazan aikata ba !!! Ko yarima Haidar da ka gani ban barshi a Wannan masarautar ba saida na tabbatar cewa yana da nak’asa sannan kuma ban daukeshi a kan karon komai ba !!! Duk da ma de Y’ata Meenah bata k’auna ta Sam !! Amma Wannan karagar mulkin da ita ya dace ba Haidar ba!!!” Sarki Hasheem ne yayi Wannan maganar hannunshi rik’e da kofin zinare. Sarki Jalalud-deen ya mik’e yayi wata y’ar muguwar dariya yace ” lallai abokina baka da wayo !! Ai sai da wuta ake shan Zuma!!!domin dan hakin da ka raina shi zai tsone maka ido ,yaran yanzu da ka gani ,zamani ya chanja domin babu wata dabara da basu sani ba ,bar ganin shi da nakasa ,kaga fa yadda ya mamaye zukatan al’umma ! Abun yi kawai shi ne ka kawar da shi kwata kwata domin in baya nan tare da kai babu yadda za’ayi Meenah ta ‘ki kar6ar mulkin Ramali ,ka duba fa ka gani ,mace ce mai kwarjini ga jarumta bai kamaceta bama a ce Wai ta bar daular dake cikin wannan masarautar! Ni ina da shawara ,me zai hana a had’a su aure da d’an wajena Rizwan? Kaga zasu yi mulkin Ramali cikin kwanciyar hankali ,kasan ko d’ana Rizwan bashi da masaniya akan abubuwan da nayita tufkawa a masarautar Kalahari , don na lura yan da son gaskiya shi yasa na ci gaba da 6ata shi da sakalci don in har ya gano ni ba mai gaskiya bane ,Rizwan zai iya juya min baya kasan duk da ba Saleemah bace ta haife shi amma goyon ta ne shi yasa nayi duk yadda zan yi su daina ganawa da juna kullum!!” Duk suka bushe da dariya Hasheem yace ” baka da dama abokina!! Shikenan! Na amince da shawarar ka!! …..
Jaseena ta toshe baki da hannayen ta ,ganin fitowa zasuyi yasa ta ruga a guje ,bata ankara ba taji an fizgo hannun ta cikin wani d’aki an rufe k’ofar ,zata yi magana yasa hannu ya toshe bakin ta yace , “ki nutsu” tana juyawa tayi ido hud’u da Rizwan:oops: tace ” kai!!! Sake min hannu na !!! ” ta fisge hannunta daga rik’on da yayi mata ,ta bud’e baki zata ‘kara wata maganar ya ce ” naji duk abubuwan da suke shiryawa !! Kamar yadda kema kika ji su ‘ da na zaci ni ne asalin wanda ya cancanci sarautar k’asar Kalahari ashe ba sarauta ta bace ta wani ne ! Duk rashin mutunci da cin amanar da nake wa mutane ashe de duk a banza ne , duk kuri da gadara da mulki ashe ba ta mahaifina bane !!! Kaicho na wlhy nayi nadamar samun irin wannan uban ,wanda kawai son zuciya ya saka a gaba ,kuma yanzu na tabbatar ba sona yake ba don yana turanine cikin halaka !! Wani hawaye ne ya biyo kumatun Jaseena tace ” hakane yaya Rizwan amma ai babu komai akwai Allah!! Tana kai wannan ta fice tana goge hawaye ,tabar Rizwan yana tunanin dalilin k’iran shi da tayi da yaya Rizwan ; cikin ranshi kuwa sai tambayar kan shi yake ,dama akwai ranar da zata zo har zai zubar da kwalla da kuma jin tsananin tsanar mahaifin shi?
Da sassafe Jaseena ta shirya cikin irin shigar da ta saba ,ta fice don gari ko gama wayewa bai yi ba ,bata zame ko ina ba sai inda sukayi alk’awari zasu na had’uwa ita da Haidar ,amma abun da ya d’aure mata kai shine tun da taje tana masa magana ko kallon inda take bai yi ba ballantana ya amsa mata ,da gani kasan ranshi a 6ace ne. A fusace ya tashi zai bar gurin ta sha gabanshi da gudu tace ” Wai ni laifin me nai maka ne!?tun d’azu ina maka magana ka min shiru kamar da gunki nake magana alhali na tabbata kana ji na “! Bai saurareta ba ya bi ta gefenta zai wuce ta sake tare shi ,cikin tsawa yace ME KIKE YI JIYA A DAKIN RIZWAN!!! ” shiru tayi tana kallon shi ido da ido ta ce ” me kake nufi Haidar ? Me kuma zanyi a d’akin Rizwan ,chan ta juyo tace ,yaya Haidar !! Yaushe muka fara haka da kai? Me yasa bazaka fad’a min ba? Me yasa kake boye min ? ” Haidar yayi sauri ya tari bakin ta yace ” Jaseena ban fahimce ki ba ” tayi murmushi wanda yasa hawayen da ke idanuwan ta suka zubo ba shiri tace ” ka kasa fadamin kana sona ko” ka kasa kuma bawa zuciyar ka hak’uri har ta fara zuga ka,ka fara zargin abin da kake k’auna kuma sannan ka kasa daurewa! ” Haidar ya juyo yana kallon cikin idonta” yayinda ta juya zata bar gurin. Haidar yace ” na soki Jaseena kuma har abada zan soki ” ya durk’usa k’asa yace ” kiyi hak’uri ya ke Kyakkyawa ! Ki taimaka min da zuciyar ki domin tawa ta riga ta kufce min ! Ban kuma san yaushe zata dawo gareni ba don ta fita farautar abunda tafi mata komai soyuwa ne!”