JASEENA COMPLETE HAUSA NOVEL

???? Jeeddah ja’o????
[3/25, 10:45 PM] Jeeddah ja’o????: ⚔????JASEENA????⚔ 2016
????????Jeeddah ja’o????????
6⃣1⃣⏭6⃣5⃣
Jaseena ta juyo idanuwan ta duk sun yi ja ,tace “Na baka !! Na baka ya Haidar!! Ka kula da ita domin taka ta riga ta iso inda zata tsaya da farautar kuma bani da tabbacin zata koma gareka !!” Haidar ya mik’e yace ” nagode kyakkyawa !! Jaseena tayi murmushi tace ” akwai maganar da nake son sanar da kai ne ” Haidar yace” ki fad’a mana ko ma menene. Ta kwashe duk abubuwan da ya faru a daren jiya ta sanar da shi har abunda yasa ta shiga d’akin Rizwan. Haidar ya sake bata hakuri ,sannan ta gyara zama ta ce ” baka k’arasa min labarin ka ba” ya d’an yi murmushi sannan ya ci gaba……..
????????????????????????????????????????????????????????????????????????
A lokacin ina da shekaru goma sha shida ne ,k’ anin babana wato Hasheem ya bi rud’in uwarsa na cewa Kar ya kuskura ya bar babana da rai don in har ya tsufa a kan karagar mulki nine zan gaje shi na zama sarki , don shi a cewar shi ni ba komai bane in ya kawar da mahaifina, da duk wani mai ji dani, kasantuwar kullum da safe muna fita daji ni da kakana yana nuna min nau’in ganyayyaki da amfanin su ,hakan yasa ya shirya mana gadar zare.
Mun yi Nisan kiwo nida kaka har bayan la’asar sannan muka iso gida ,muna shiga wasu mutane a kan dawakai su kuma suna fita ,ga gari duk ya turnuk’e da hayak’i ko da muka k’arasa cikin fada nan muka tarar da gawawwakin iyayena da kuma na k’annen k’ anin Hasheem Hayatud-deen , Hasheem ya kwanta a kansu sai kukan munafurci yake yi kamar da gaske ,a nan ne zuciyar kakana ya buga take rai yayi halinsa , bayan kwana uku da faruwar hakan ,kawu Hasheem ya na’da kanshi a matsayin sarkin Ramali ,duk dattijawan da basuyi Na’am da hukuncin da ya yanke ba sai ya sa aka kwashe su aka kai su masarautar Kalahari aka rufe ana basu horo mai tsanani ,daga cikin wadannan dattijawan sun had’a da mahaifan Aisha da kuma Jauda ,kamar yadda na fad’a miki Meenah itace d’iyar kawu Hasheem amma tun tana y’ar shekaru tara ne abun ya faru don duk sa’anni suke da Aisha da Jauda kinga kuma k’awaye ne hakan yasa ta baro fada ta zab’i zaman bauta a gidan Benaxir har ta girma ta kawo lokacin nan da kike gani….
Ni kuwa tun lokacin da abun ya faru na daina magana da Kowa da na gano hakan kawu Hasheem ya ke so sai na nuna mishi ma kwata kwata bana magana na daina yi ko da da wasa ,a haka shi da mabiya bayansa suka zata na riga na zama miskini. Kin ji yadda rayuwa ta ta kasance kullum cikin k’ask’anci amma ko a jikina domin na san dole ne wata rana sai gaskiya tayi halinta!!” Amma tunda haka abun yake toh mu zamu fara wargaza mishi rayuwar sa” Jaseena ta goge d’an hawayen fuskar ta sannan tace ” lallai ka shiga k’uncin rayuwa Haidar !! A nan ne Jaseena ta kwashe labarin ta ta bashi ta kuma sanar da shi ko wanene sarki Jalalud-deen. Sun dad’e suna shan hirar su ,kafin nan suka nufi gidan Benaxir don yin magana da su Jauda……….
????Jeeddah ja’o????
[3/27, 11:25 AM] Jeeddah ja’o????: ⚔????JASEENA????⚔ 2016
????????Jeeddah ja’o????????
6⃣6⃣⏭7⃣0⃣
Sarkin yak’i Amjad ne zaune a gefen sarki Hameed hannun shi rik’e da na Hameed. Na ganta! Naga y’ar ka Jaseena ,tana cikin k’oshin lafiya ,kuma ga dukkan alamu tana cikin shiri,Hameed ya mik’e yana murmushi yace ” nasan ban haifi lalatacciya ba!! Kuma nasan dama tana nan tafe , amma ya maganan mayak’an da na ce ka tara ? Amjad yace ,komai an kammala shi kuma yanzu haka suna chan a kogon tare da y’an fursunan k’asar Ramali! Da sarki Hasheem ya sa Jalalud-deen ya d’aure shekaru kusan goma sha da suka wuce ” Hameed yayi murmushi yace ” da kyau sarkin yak’i!!! Aikin ka yana kyau ,Allah ya mana jagora!! Sarkin yak’i yace “Ameen”sannan ya mik’e ya fita………
Yau tun da safen nan Jaseena take motsa jiki tun bayan sun dawo daga gurin su Jauda Zabil kuwa ya samu Haidar ba kasafai yake waiwayar inda Jaseena take bama don in zai fita daji tare suke tafiya. Saidai yau Haidar bai je ko ina ba yana tare da k’anwar sa Meenah a cikin makeken lambun dake wannan masarautar suna ta hirar su duk da ma dai itama maganar kurmancin yake mata amma ta saba don ko ubanta Hasheem bai iya magana dashi sosai ba. A nan ya sanar da ita cewa yana soyayya da Jaseena, murmushi kawai tayi. Haka sukayi ta hira har kusan azahar, sannan ya tafi domin gudanar da ibada yayinda itama Meenah ta juya tabar wajen ,zata koma gidan Benaxir.
????????????????????????. Jaseena????????????????????????
Yau kwana na uku kenan ana ta bidirin gasa, Sam Sam Rizwan abun ma bai dameshi ba balle ma ya shiga ,hasalima cewa yayi babanshi ya chanja wanda zai yi wasan shi bazai iya ba ,babu yadda aka iya haka aka chanja shi da wani k’ak’k’arfa daga cikin mayak’an Kalahari. Jaseena kuwa tun ranar farkon nan bata sake shiga filin ba kullum tana daga chan baya ita da su Aisha amma fa ta lura cewa sarki Jalalud-deen hankalin shi bai kwanta da ita ba. Washegari da safe ta shira cikin dogon bujen wandonta bak’i da wata riga fara sannan ta rataya takobin ta da y’ar jakar ta ta fice daga fada ,fuskarta a rufe ta bar idanuwan ta a waje kamar wanda ta saka niqab , tafiya take cikin sauri kamar zata tashi sama, duk saurin ta sarki Hasheem yana tsaye ta sama a d’akin shi daga tagar d’akin yana kallon duk abunda ke faruwa ,tana fita Rizwan ma ya bi bayanta, ganin haka ne yasa sarki Hasheem shima ya rufa wani k’aton mayafi don Kar Fadawa su ganshi su ce zasu rakashi ya fice daga fada suna tafiya yana binsu duk yana jin abunda suke fad’a har suka shiga Inda Haidar yace za suna had’uwa ,ya lab’e bayan wani dan ice yana sauraron duk abunda suke fad’a…..
????Jeeddah ja’o???? BACCI????????????
[3/30, 9:17 AM] Jeeddah ja’o????: ⚔????JASEENA????⚔ 2016
????????Jeeddah ja’o????????
7⃣1⃣⏭7⃣5⃣
Haidar, Jaseena, Aisha, Jauda, Meenah, da Rizwan!!!! Duk na ji abubuwan da suke shiryawa !!! Don haka dole ne mu kawar da su tun kafin su cimma burinsu????. Sarki Jalalud-deen ya mik’e tsaye ya rasa me zai ce saboda ko kad’an baya son dansa ya shiga wannan alamari amma tunda ya nuna taurin kan shi a fili toh lallai ba makawa sai an hukunta shi.
Haidar yana sane da cewa sarki Hasheem yana wannan gurin shi yasa ko ‘kala bai ce ba a gurin ,sannan kuma yasa Jauda tayi karya akan shirye shiryen da sukayi ,sun yi akan sai an gama gasa zasu far musu amma ashe shirin Sam ba haka yake ba !!! Cikin dare k’afa duk ya d’auke suka shirya duk irin yadda Jaseena take shiganta ,suka shigo fada ,Jaseena akwai ilimin duk wani abu da ya shafi yayan itatuwa da ganyayyaki saboda haka ta shiga d’akin da sarki Hasheem yake ta zauna bakin makeken gadonsa tana wani muguwar dariya ????ta fito da had’in maganin da tayi sannan ta debi kad’an ta watsa a fuskar shi a take ya farka gami da yin wani atishawa ya sulale ya koma kan filow ,nan ta d’aure shi ga igiya tam sannan tayi fito a hankali ,Haidar ya shigo shi da Rizwan suka ciccibeshi suka yi waje. Haka ne ya faru da sarki Jalalud-deen ma ,suna fita basu zame ko ina ba se cikin wani tangamemen daki mai kama da keji suka tura su ciki ba komai bane ke gadin wajen illa damisa guda uku manya manya ????