HAUSA NOVEL

JASEENA COMPLETE HAUSA NOVEL

Da dariya suka fito su Jauda suka d’aga Jaseena sama yayinda Haidar da Rizwan ke ta musu dariya, suka koma cikin gari ,kasantuwar inda suka je da nisa ,sai kusan asubah suka iso cikin Ramali ,wannan kurkukun kuma shine asalin kurkukun masarautar Ramali kafin sarki Hasheem ya hau mulki. Isarsu cikin gari basu zame ko ina ba sai fada ,Haidar yasa a tara masa duk jama’ar wannan masarautar su hallara a cikin fada ,kafin awa d’aya duk Kowa ya samu isowa ,Haidar yayi murmushi ya gyara murya sannan ya fara da cewa:

Al’ummar Ramali !!! Akwai wani d’an karamin labari da zan baku labari ne na mikiya kuma ina kyautata zaton daga jin wannan labarin zaku fahimci Inda na dosa!!” Cike da mamakin jin magana da sukaji yarima Haidar yayi suka amsa da ” muna sauraron ka yarima!”

????Jeeddah ja’o????

[4/3, 10:43 PM] Jeeddah ja’o????: ⚔????JASEENA????⚔ 2016

????????Jeeddah ja’o????????

7⃣6⃣⏭8⃣0⃣

Ita mikiya wata tsuntsuwa ce wadda zata iya rayuwa har tsawan shekaru saba’in, amma domin kaiwa wannan Shekarun ,dole sai ta d’auki tsatsauran matakai,domin lokacin da takai shekaru arba’in dogin faracinan ta zasu zama basu da karfin neman ko kuma chafke abunda zasu samu a matsayin abinci,wannan dogon bakin ta mai kaifin zai kwanta (lank’washe ) fukafukan zasu zama tsofaffi, masu kauri kuma ga nauyi , wannan fukafukan masu kauri da nauyi ,zasu zama kamar a k’irjin shi suke hakan zai basu wuya wajen tashi sararin samaniya daga nan ne mikiya zata zama bata da wani zabi wanda ya wuce guda biyu kachal ✌???? ko ta MUTU ko kuma ta rayu cikin salo mai wuya na neman SAUYI! Hakan yana bukatar mikiyar ta tashi ne sama ta hau kan tsauni ,ta zauna cikin gidanta (nest) sannan sai Yayita buga wannan tsohon bakin nashi jikin dutse har sai ya fincike shi , sannan wannan mikiyar zata bari har sai sabon ya fito sannan sai ta fincike tsofaffin faracinan ta da shi ,lokacin kuma da wadannan faracinan suka fito ,sai ta fara fiffige tsofaffin fukafukan nata da shi wannan shine chanji da yafi ciwo zafi!! Toh daga nan ne wannan mikiyar take sake daukan sabuwar rayuwa ta sake yin wasu shekaru talatin din a gaba! ME YASA AKE buk’atar CHANJI??? Saboda a rayu kuma ayi zamantakewa!! Muma dole mu bi hanyar SAUYI!!! Amma ba kamar mikiya ba ,Muma dole mu sauya munanan d’abiun mu zuwa kyawawa da kuma abubuwan da muka aikata marasa kyau zuwa masu kyau ,mu zama masu koyi da abunda addini ya zo mana da shi!!

Saboda haka domin daukar hanya zuwa wannan SAUYI sai ku watsar da wadancan d’abiun domin samun sababbi ,duniyar da fadi take amma mu bita a Sannu! Ku bude ajiyayyan k’wak’walwar ku don ku Adana wannan ko zaku tashi da sabuwar rayuwa irin ta mikiya!!!……..

Kowa yayi shiru jiki a sanyaye ,fadar tayi dub kamar babu wata halitta a cikinta , wasu na hawaye amma hawaye ne na farin ciki cewa yau gaskiya ta dawo masarautar Ramali! Wani dattijo ya mik’e yace ” wannan haka yake yarima Haidar! Muna tare da kai ! Dattijawan gari suka na’da Haidar a matsayin sarkin Ramali , ganin yadda komai yazowa Haidar cikin sauk’i yasa Rizwan ya mak’ale mishi yace shi zai raka shi masarautar Kalahari don ya nemi gafarar mutane wata’kila in yasa baki za’a yafe masa shashanci da yayi ta aikata musu ba dare ba rana,nan suka sake sabon shiri dukan su tare da wasu mayak’a guda ashirin suka d’au hanyar Kalahari…………

????Jeeddah ja’o????

[4/7, 6:04 AM] Jeeddah ja’o????: ⚔????JASEENA????⚔ 2016

????????Jeeddah ja’o????????

8⃣1⃣⏭8⃣5⃣

Kasantuwar ba hanyar da su Jalalud-deen suke bi don shiga k’asar Ramali zasu bi ba ko dawakai basu d’auka ba cikin sauki suka bi ta inda Jaseena ta fito suka shiga wannan ramin ruwan har ta kaisu ga asalin cikin kogon ,bayan sun gama dirko wa daga wannan dutsen ne suka tsaya karkade jiki su Jauda se kalle kalle ake yi basu ankara ba suka ga sojojin yak’i sun zagaye su kowanne hannu rik’e da mashi ,gashi kuma abun da ya basu mamaki duk babu saurayi cikin su don duk sun manyanta da gani kasan sun yi zamani, Jauda ce ta fara jefar da jakar da ta rik’e tana motsar k’walla ” baba!!! Abunda ta iya furta wa kenan ta nufi gurin d’aya daga cikin wad’anda suka zagaye su ta rungume tana kuka Aisha ma ta nufi gurin wani da ke tsaye yana kallonta sai hawaye ,Jaseena da ke kallon su tuni itama ta fara k’wallar saboda ta tuna nata mahaifin da bata ma san wanne hali yake ciki ba , Muryar sarki Haidar ne ya dawo da ita daga duniyar tunani, tana juyawa taga gurin babu Kowa daga shi sai ita ta fara juye juye fuskar ta cike da alamar tambaya?? Kafin ta furta komai Haidar yace ” ya ke ma’abociyar kyau da farin hali, kada ki damu Mun basu dama ne su gana da iyayen su domin kuwa sun yi kewar juna ” Murmushi Jaseena tayi sannan ta fara share hawayen da ke gangaro wa daga idanuwan ta ,Haidar ya matso kusa da ita yace ” ya isa haka Kar ki sake yi min asarar hawaye ! Kuma baba yana cikin k’oshin lafiya” Jaseena ta d’ago manyan idanuwan ta tace ” don Allah muje in ga baba na ,don hankali na bazai kwanta ba in ban sa shi a ido ba tana fad’in hakan hannunta guda kuma ta chafke wuyar rigar shi ,inda ta shak’e ya kalla sannan yayi Yar murmushi cikin murya irin na zolaya yace ” irin wannan chafka haka ,duk kin yamutsa min riga! Lallai kina so na sa a kulle min ke a kurkuku yanzungaske.???? ” Hakan yayi matuk’ar bata dariya yadda ya ta6e fuska kamar da gaske. Ya ce Haba!! Ko ke fa ? Amma matar sarki guda gashi kuma jarumar mata amma tana hawaye kamar raguwa?” Dariya ta bushe da shi tace ” Aa ba wani nan ! Cewa zakayi jarumar mata da maza ???? ai mazan ma saidai in basu nemi in sambad’e su ba ????????”. Dariya sosai ta bawa Sarki Haidar har ya shagala ya nemi gurin zama yana kallonta, ita ko sai fama take da y’ay’an innibi???? ,yana kallon yadda karamin bakinta ke motsawa cikin nutsuwa ta lumshe idanuwa sai faman tauna take, yayi murmushi ya mik’e ya d’auki wani dan karamin dutse ya wulla mata ya samu damtsen ta ,tuni hankalin ta ya dawo daga duniyar da ta lula tace ” ya dai?* ya had’e rai yace ” kin barni babu hira sai faman tauna kike yi !! Ni na fa gaji ma kuzo mu tafi inda zamu je kafin dare yayi mana” chan sai suka lura ko ina yayi shiru cikin kogon

Cikin sand’a yake tafiya tana biye da shi ,haka suka gama dube duben su basuga Kowa ba a cikin kogon ,Jaseena tace ” toh ina suka tafi ne?” Haidar ya yi shiru na yan mintina sai yace” duk yadda akayi sun nufi Kalahari ne zo mu tafi!! ” ko da suka fito bakin kogon suka tsaya suna tunanin yadda za’a yi su tafi Kalahari babu doki kuma gashi da nisa suna so su tadda su Jauda. Har ta hak’ura ta jingina da jikin kogon kawai suka jiyo sautin doki ,tana juyowa ta hango zainu shi kad’ai ya dumfaro su ta juya ta dubi Haidar tace baba ne ya turo shi , na tabbata sun isa Kalahari!! ”

???? Jeeddah ja’o????

[4/7, 9:36 PM] Jeeddah ja’o????: ⚔????JASEENA????⚔ 2016

????????Jeedah ja’o????????

8⃣6⃣⏭9⃣0⃣

Isarsu Kalahari basu zame ko ina ba sai cikin fada kamar wanda ake jiran isowar su mutane aka fara bude hanya don su samu su wuce ,Jaseena kam da ta hango baban ta taga yadda suke tafiya a hankali a saman dokin ,yasa ta dirko daga kan dokin ta ruga. Rungume mahaifin nata tayi tana kuka ,ya d’ago ta yana faman share mata hawaye ,zata yi magana kenan suka ji Hameed ya ja wani irin numfashi kamar an shak’e shi ,idon shi na hawaye ,tace ” baba!! Me ya sameka baba??” Kallo na biyu da zata masa ne ta ga abunda ya matuk’ar tada mata hankali ,mashi ne a wuyan shi ga kuma Jini yana malala kamar ruwa ,a take ta kurma ihu ta zube a k’asa jiki na b’ari ,da gudu Haidar ya iso inda suke ya rike Hameed yana hawaye , abunda ya iya furtawa shine ” ga Y’ata nan Amana ,Kar ku cutar da ita marainiya ce don Allah!! ” ya dan saki wani ‘kara gami da Kalmar shahada take ya mace a gurin ,wani irin ihu Jaseena tayi ta sulale daga zaunen da take ta fad’i sumammiya Haidar ya dubi su Jauda da ke faman zubar da k’walla yace ” ku kai Jaseena ciki ku tabbatar ta samu kulawa don Allah ! Suka yi kamar yadda ya umarce su.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button