HAUSA NOVEL

JASEENA COMPLETE HAUSA NOVEL

Haidar yace sojojin yak’i su shiga su nemo koma waye yayi wannan Harbin a kawo masa shi. Ana cikin wannan alamari ne wani soja ya zo da gudu wujiga wujiga duk jikinshi yanka ,sai haki yake yana kiran sarki Haidar. Fadawa suka tare gurin shigowar amma ya umarce su da su barshi ya karaso domin daga ganin shi kasan akwai wata matsalar da ke tafe da shi. Kafin mutumin ya fara magana ,Haidar ya juya ya dubi su Rizwan yace ” a shirya gawar baba mu sallace shi Mu kaishi makwancin shi na gaskiya,” sannan ya juyo ya dubi mutumin yace ” bawan Allah me ya faru da kai haka? Wa ya aikata maka wannan taaddancin kuma daga ina kake?

Cikin rawar jiki mutumin yace ” Allah ya baka nasara daga Ramali nake ….” Ko da Haidar yaji an ambaci Ramali yasan tabbas babu lafiya gashi sarki Hameed ya rasu ,ga Jaseena Kwance babu maraba da matacciya dole su Jauda su kasance tare da ita , toh me ma yake faruwa ne haka?” Tambayar da yayi wa kanshi kenan gaba daya ya kasa tunanin abu daya, ya tura wasu Fadawa tare da mutumin su bashi taimakon gaggawa kuma a kula da shi”…….

Ana shirin sallatar Hameed ne Jaseena ta farka ,bata bi ta kan su Jauda ba ta furma a guje ko mayafi babu duk gashi a barbaje gashi duk ta zabga gumi gashin ya mammanne mata a fuska bata zame ko ina ba sai gaban gawar mahaifin ta cikin yanayi na tausayi ,bakinta karkarwa kamar mai jin sanyi , ta d’aga hannun ta mai karkarwa kamar zata yaye masa fuska sai kuma ta fasa ta dunkule hannun cikin kuka tace ” baba !! Ka tashi don Allah kar ka tafi !!! Abunda ta yi ta maimaita wa kenan hakan ya sake tada wa Haidar hankali don a tunanin su ta zauce ne ,yadda take yi din abin tsoro da kuma tausayi. ” Meenah ku koma da ita ciki don Allah ” shima yana kokarin danne kukan da ya so kufce mishi.

Bayan sun dawo daga janaiza Haidar bai zame ko ina ba sai cikin fada don ya nemi dakin da Jaseena ke Kwance ,ko da ya iso gurin shi da Rizwan basuga Kowa a d’akin ba ,babu Jauda ,Jaseena Aisha da kuma Meenah. Haidar ya fito a fusace ya dubi bafaden da ke bakin k’ofar yace ” ina suka tafi kuma ?” Bafaden yace ranka shi dad’e sun fita su hud’u amma fa naji kamar suna maganar Ramali ban sani ba ko Chan suka nufa……. Bai ma saurari k’arshen zancen ba ya juya suka nufi hanyar fita……………….????

????Jeeddah ja’o????

[4/8, 8:19 AM] Jeeddah ja’o????: ⚔????JASEENA????⚔ 2016

????????Jeeddah ja’o????????

9⃣1⃣⏭9⃣5⃣

Gudu suke kamar zasu tashi sama ,Jaseena ce kan gaba sai faman k’walla take yi zuciyar ta na ta tafarfasa har suka isa masarautar Ramali ,shigan su ke da wuya suka ji ana ta rufe kofofin gurin wasu sojoji suka zagaye su kamar masu kama barayi ,babu wanda ya motsa a cikin su tabbas Jaseena ta lura cewa duk sojojin da ke zagaye da su kibiyar da ke kwari da bakan su iri d’aya ne da wanda aka harbi mahaifin ta ,ta tabbatar cewa wannan aikin Jalalud-deen ne ba Kowa ba ,abunda ya sake kulle musu kai shine yaya akayi suka fito daga wannan kurkukun? Jauda ma abunda take ta sak’a wa kenan………

Ko da Haidar ya fito waje ,yasa an tara mishi jama’ar garin manya da k’anana da kuma gagga gaggan sojojin yak’i wadanda ake ji da su suma sun hallara nan ne Yerima Rizwan ya rok’eksu yafiya kuma ya sanar da su cewa zai yi koyi ne da irin halin kawun shi marigayi sarki Hameed ya kuma yi rantsuwa da hakan ,Kowa ya ji dad’in wannan alamari saboda haka dattawan garin basuyi wata wata ba suka na’da shi sarkin Kalahari ,bai hau kan karagar mulki ba yace har sai yaje an yak’i azzaluman da suka kashe sarki Hameed kuma in har bai dawo da rai ba ,toh ya bawa Meenah wannan gadon mulkin domin ita tafi chanchanta ,amma idan har komai ya tafi daidai toh za’a hada masarautar Ramali da Kalahari su zama masarauta d’aya a k’ark’ashin mulkin sarakuna biyu wato sarki Haidar na Ramali da kuma sarki Rizwan na Kalahari ⚔

Jaseena bata wani tsaya 6ata lokaci ba ta zare takobin ta ta diro kasa suka fara fada su Jauda ma suka biye mata gurin ya kaure bakajin ‘karar komai sai na had’uwar karafuna kafin kace wani abu sun gama da sojojin suka tsaya a gurin sai haki kamar zakanya Jaseena ke yi ta mayar da takobin cikin rigar shi ,d’aga kanta da zata yi kawai ta hango munafukan guda biyu ,sarki Jalalud-deen rik’e da kan d’aya daga cikin damusar da ke gadin kurkukun ya d’aga sama yana kyalkyata dariya daga chan saman benen da yake yace ” me ya farune GIMBIYA JASEENA!? Ina fata ba karaya kika yi ba don in hakane wasan Sam bazai yi dadi ba ! In kin isa yadda na saka tsaro dinnan ki karaso kiga me zai faru! Amma ko da yake ina so inyi magana da ke ,kuma ke kadai don haka ke kadai nake so ki zo ki sameni babu makami kuma !!! Ya sake burgewa da wata muguwar dariyar. Jaseena da idanuwan ta sun kad’a sun yi jajir ta kau da kanta daga duban da take masa tace KAI !!!! MATSORACI!!! KAI NE KAKE TUNANIN TAKOBI KO BAKA SHINE ASALIN MAKAMI ,AMMA ASALIN MAKAMI A ZUCIYA YAKE!!!!” Ta zubar da makaman zata tafi su Jauda suka sha gabanta Aisha tace ” Jaseena ba zamu barki ki shiga ke kadai gurin wad’annan azzaluman ba gaskiya” Jaseena tayi murmushi tace Haba Aisha ,ai koda kashe ni zasuyi inshaa Allah zan shiga kuma zan d’auki fansa!!:evil: ta wafce hannun ta tayi ciki duk fadawan suka bita da kallo ????

Shiganta kenan su Haidar suka iso gurin ,garin ma shiru kamar babu Kowa , a nan ya iske su Jauda cikin matsananciyar damuwa , suka sanar dashi duk abunda ke faruwa hankalinshi ya tashi Rizwan yace ” yanzu meye abun yi ??¿

Jaseena kuwa da ta shiga kai tsaye fada ta nufa shiganta kenan taji an rufe k’ofa ta juya da sauri don taga wanene daga cikin su, Muryar shi ne ya fara ratsa kunnuwan ta tabbas sarkin yak’i Amjad ne:oops: ta waro ido waje tace ” kai ! Dama Kaine?!! Me kake yi a nan kuma?!!” Ya matso kusa da ita ya makureta a bango kamar me neman kasheta ,sai taji yana mik’a mata abu a hannun ta ,tayi amfani da tunanin ta taji ashe karamar wuk’a ce tayi wata k’aramar dariya yace ” godiya nake” shi kuma ya hankad’a ta gefe ta zube a ‘kasa su Jalalud-deen kuma basu san wainar da suka toya ba sai wani dariyar keta sukeyi. Jalalud-deen ya karaso inda take rik’e da irin kibiyar da aka harbi Hameed yace ” ban sani ba Jaseena ! Ko tayaya zan fara gamawa da ke ! Ko in sambad’e ki da wannan takobin ne kokuma wannan kibiyar wadda itace silar barin ubanki da uwarki duniya?? Ko kuma………… Kafin ya karasa ta buga masa wannan y’ar wuk’ar a daidai mak’ogoro kamar me bud’e madarar peak ???? tuni ya durkusa kan gwiwar shi ,Jini na malala kamar ruwa, ta zare wuk’ar tace ,ba sai ka za6a ba???? take ya fadi ‘kasa ya gama shure shuren sa har ya margaya (Hmmmm duniya kenan budurwar wawa akan son abin duniya har ka kai kanka ga halaka!!) Ta juya ta dubi sarkin yak’i tace” ina Hasheem? ” ya nuna mata k’ofar fita yace ” ya fice tun tuni! Mu bishi!!!!! Jaseena tayi wata muguwar dariya tace Kar ka damu ,yayi gudun gara ne ya tadda zago don nasan yanzu haka jikina yana bani ZAKI NAH!(Haidar) ya riga ya iso ????

Suka dunguma sukayi waje suma, ko da suka fita basu tarar da Hasheem a raye ba amma kuma kamar mutuwar kasko sukayi da Jauda???? da gudu Jaseena ta yo kan Jauda da ke Kwance a gurin matacciya ta rungume ta ,kuka takeyi duk ta susuce su Meenah ma na durk’ushe a gaban su suna kukan. Haka ranar Jaseena ta kwana tana kukan zuci wanda yafi kuka ciwo????……………

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button