NOVELSUncategorized

KWARATA 76

???? —— 74
      Yaye bargon da yake lulluɓe tayi taci gaba kuka tana ɓarke²n zagi tana ma Dikko gori wai yaji kunya ya rasa wacce zai aura sai karuwa ɗiyar ɗan caca jahila matalautan da suka kasa siyen gidan zama saidai gidan haya ai duk talaucin da yasa mutum ya rasa gidan zama wannan talaucin ya kai abun a duba matsiyatan banza da wofi ,


       Me yake nema a wurin yarinyar nan ? Bayan ita tafi ta komai kuma su masu kuɗi gidansu Sultana fa ? Duk abinda ake nema ga mace Sultana basu da , duk abinda ya cancanta ka aureta saboda shi babu ko ɗaya da take dashi , jahila daƙiƙiya mace babu ilimi ai kwankwon ashana ce domin shi ilimi tushe ne mai nuna dogon zango , kaga tun nan abinda kake nema baka samu ba , halin kwarai jari ne , bata dashi , su kuma kuɗi jigone masu nuna isashshen iko a cikin abunda na lissafo wane take dashi ?


2gnovel

4medicals

Smidris


      Ai ni ina da duk abinda kika lissafo ko ? Ai kaine kake dashi ba ita ba , to na bata ilimina na bata halina na bata duk komai nawa ke kinsan An mata kuwa ? Ki bari tun kafin raina ya ɓaci na fara maganganun da zakiji babu daɗi dan haka ki tattara mutuncinki ki barmin ɗakina !

Bana tafiya sai kayi maganganu akanta munafikin banza maci amana , murmushi Dikko yayi cewa nine munafiki Jiddah ? Maci amana ? Wace irin amana ne naci haka da har kikemin gori ? Ban sani ba baƙin munafiki , sauka yayi daga saman gado yana cewa Allah ya baki lafiya ya wuce toilet , ita kuma taci gaba da ɓaɓɓarka mishi zagi harya gama abinda yake ya fito Jiddah bata daina sokawa Dikko zagi ba.

     Inda take tsaye yaje ya riƙota cikin rarrashi yace ni ne ? Kwantar da fuskarta tayi saman ƙirjinshi tana kuka cikin shashshekar kuka tace Yaya dan Allah bana san auren nan , tou muje saman gado saiki faɗamin kinsan ban cika jin magana daga tsaye ba , ni bazan hau gado ba , tou tunda bazaki hau ba fitarmin daga ɗaki idan ba haka ba zan hau dake dole kuma jikinki zai baki labari , da sauri ta sauka daga jikinshi tayi waje da gudu tana kuka , murmushi Dikko yayi yace matsoraciya.

       Saman gado ta faɗa taci gaba da kuka a zuciyarta kuma jinjina irin muguntar Dikko takeyi macuci idan har yana jin haushin mace sai yayi mata ƙeta mamugunci nufinshi yashata basilla murmushin mugunta Jiddah tayi a zuciyarta tace badai Yaya bane ba ? Kije kin samu Sultana idan dai tsintuwar fatalwa riba ne…..

        Inna da kanta taje ta faɗawa Kaka Sultana zatayi aure Kaka tayi murna sosai kuma tayi ma Inna da Sultana fatan alkairi , ta kuma ƙara da cewa amma me yasa saida aure ya rage kwana 6 zata faɗa mata ? Inna tace mijin ne ya zaɓi haka , Yayarta dage zaune tana saurarensu tace badai girin² ba tai mai , Inna ta gane ta maso habaici maso faɗa wanda ya tanka shi yafi tou bata da lokacinta ,

     Tunda Dikko yazo ya tsayar da ranar aurenmu dani dashi bai sake dawowa gidanmu ba kuma kona kirashi waya ya daina ɗauka ma , Inna kuwa kullum bata da aiki sai kwaɓe²n kayan mata tana bankamin saidai tsareni tana zagina wani lokaci hada mari wai bana gane wannan gata ne sai naje gidan aure , tun ina sha ina amai har cikina ya haƙura ya riƙa riƙeminshi dan idan zansha so goma na amayar Inna bata gajiya zata sake kwaɓa masifa ta bani na kwankwaɗar wa cikina.

     Labarin auren Dikko ya zaga kaf illahirin birnin garin katsina mutane sun fara canfashi ya cika aure² ya auri waccan ta mutu bai tsaya hutawa ba ya auro wannan duka yaushe yayi auren har yake tunanin sake auro wato ? Yayin da wasu kuma suke gani izzar kuɗi ce ke nuna ikonta shi yasa yana matashin shi zai aje mata biyu cikin shekara ɗaya….

     Dikko kuwa babu abinda ya dameshi da labarin dake yawo a gari shidai zaiyi , tunda ya taho kuma yaga mai tareshi matsalar bai faɗa ba zaiyi amma da zaran ya yanke hukunci tou fa ko kanshi baya saurara ,

      Duk “yan uwan Inna dasu ake hidima kuma hada yayarta kwansu da kwalkwata suna zuwa ba wanda aka rage tun bayan tsaida ranar auren da kwana biyu suka fara zuwa , kowa tambayar Inna yake tou ina maganar kayan ɗaki ? Saidai tace komai za’ayi , a kwana biyar za’ayi ? Inna tace Eh ,

     Tou basu sani ba kayan ɗaki kansu da kayan kicin duk abinda iyaye kema “ya “yansu dan fitar dasu kunya Dikko yayi saboda tunda ya fara aikin gidanshi na goruba inda zai ajiyeni daga farko dama shine yake da burin zuba komai na gida tou kayan nan yasa aka sauke su a wani gidan mijin Inna sai idan za’aje jere Inna tasa aje a ɗauka a can yadda za’ace itace tayi.

     Komai dai na hidimar auren nan cikin munafurci akeyinshi , dan ko lefe Dikko ne ya kawoshi da kanshi da daddare misalin 2:54am dashi da yaranshi bansan sunzo ba haka kuma banji tafiyarsu ba , saida safe na tashi naga wasu irin lafiyayyin akwatina masu tsinannen tsada da kyau na tashin hankali , akwatina 24 da wasu irin ƙattin jikkuna biyar babu wanda ba’a takeshi da kaya ba , wannan shine faɗawa mai zuciya biki ba mai tarin dukiya ba tou Dikko komai ya haɗa , nidai ban buɗe ba amma da Inna da mijinta saida suka zindire lefen nan kaf suka ganshi gaskiya naira wurin lefen nan taci bugu harta gode Allah wallahi komai na cikin lefen abun burgewa ne babu abu na banza komai baka isa ka raina ba saidai hassada.

       Ƙawayen Inna “yan duniya lokacin da suka zo suka ga lefe sunyi ɓarin maganganu na isashshin mata wai Dikko dai ɗan gaye ne wayayye tebirin farko wallahi magana ya gayamin a lefe turaruka kamar suce wayyo Allah masu tsada abinda dai Dikko ke nufi yana san ƙamshi , wuraren daya kamata nayi amfani da turare suke faɗa duk abinda suka ɗaga a lefen sai sun faɗa fita nayi na bar musu ɗakin dan abinda na lura basu da kunya…..

      Washe garin da aka kawo lefe akaje ganin ɗaki Jiddah tayi wulaƙanci tayi hauka marar ɗaura zani tayi bala’en daya tada hankalin duk wanda yaje ganin ɗaki Jiddah tace babu wata mace data isa ta zauna mata gida , wallahi wannan gidan tane daga ita sai mijinta , Dikko nata ne ita ɗaya babu maishi sai ita gidanta ramin kura ne daga ita sai jama’arta sai kuma “ya “yanta babu wata banzar ɗiyar ɗan caca data isa ta zauna mata da mijinta amma idan har Sultana ta shirya mutuwa ta shigo gaba ɗaya ma auren mamarta akayi wallahi , amma idan har Caca ta shigo zata goga da ita a kishi tou tabbas tana musu albishir kwanaki bakwai cas ta bawa Caca a gidanta zata dawo babu jimawa idan tana da sauran shan ruwa gaba kenan idan kuma bata dashi su tarbata a rimin badawa , sunan wata maƙabarta ne………..

     Ta bubbugi ƙofofi ta rufesu ta hana ganin ɗaki tayi maganganu masu tsauri kuma kalamanta suna da kaushi ta fa barbaɗa rashin mutunci iyakar ƙarfinta guyawu a sace “yan ganin ɗaki suka dawo ba tare da sun samu damar ganin ɗaki ba , Inna da taji bayani kuwa cewa tayi to saidai ya raba musu gida , Inna ta yaba da masifar Jiddah baza ta yadda a haɗe Sultana da Jiddah ba dan cutar mata ɗiya za’ayi idan kuwa Dikko bazai raba musu gida ba ta yadda saidai a fasa auren nan, da ƙawayenta suka bata haƙuri cewa tayi har Sultana ma nawa take ? Ta gama haɗiye wani dafin zata fara kwankwaɗar na kishiya ? Masifa nawa zatasha ? Bazata laminta ba gara tasan abinyi tun kafin tabar nigeria idan zai yuwuwu ayi idan bayayi a barshi kowa ya samu natsuwa babu wanda zaisa ma “yarta ciwon zuciya……..

      Da daddare bayan kowa ya kama gabanshi Inna tayi ma Dikko waya tana san ganinshi , yace mata baya nan yaje kaduna amma yana shigowa katsina babu jimawa idan ya dawo zaizo insha Allah , fatan isowa lafiya tayi masa ta kashe wayarta , kallona tayi tace idan kin ga dama ki tashi kije kiyi wanka kin zauna bursunai² dake kamar an ƙwatoki bakin kura , ban kalleta ba nace ai ko ɗazu nayi wanka , dan ubanki yanzu ma sai kin ƙara wani , ai Dikko dai kike so ko ? Badai kin zaɓeshi ba ? Yanzu kika fara wanka tunda dai kina san Dikko kije kinsamu , Dikko da kike ganinshi ƙyalƙyal na rariya ne zamani ne da kanshi idan zaki iya ga fili ga mai doki , tun cikin mutunci nace ki rufawa kanki asiri ki auri Sultan kikaje kikayi ta hauka tun ina nida ke saida kika ɗaga murya aka jiyoki uwayen sharri suka kira ubanshi a waya suka faɗa mishi bakya san ɗansa sun nemi sharrin duniya sun ɗora miki hankalinsu bai kwanta ba saida suka ga an fasa auren nan , hmmm Dikko dai ko ? Bazan miki baki ba.

     Da kin auri ɗan uwanki asiri a rufe babu wanda yaji ya gani amma dake  ke sakarya ce baki san wanda yake sanki ba kin biyewa ƙuruciya da san zuciya ga yadda ta kaiki Caca ma take kiranki tsabar ta maidake jaka ta ƙarshen benci iskanci da rashin kunya kuma duk garin nan ba na gaba da Dikko , “yar uwarshi ce can zaki musu iskanci su haɗe miki kai suci ubanki nidai bazan fasa tafiya ba , india ba fashi wallahi saina bi mijina zan baki makullin gida idan bai miki daɗi ba kizo ki buɗe ki shiga ko ki tafi wurin ahalin ubanki gidan Hajiya dai yai miki tsururu cikin hayani tace ki tashi daga gabana in daina ganinki , da sauri na miƙe zan fita tace baza kije kiyi wanka ba ? Jiki a sanyaye na dawo na wuce ciki danyin wanka !

      Cike da damuwa Inna ta miƙe taje ta nemi wasu magunguna ta damesu da madara tana damawa tana mita Dikko ɗan duniya idan ba’ayi shirin tashin bama²i ba ai za’aji babu daɗi , Inna a ganinta wannan shine mafita ta mayar da cikin Sultana kamar wata tsohuwar rijiya duk abinda ta kwaso a cikinta take juyewa saboda wannan garinka da take bankawa “yarta abinci ma kwata² ya daina ciwowa gareta , wata “yar duniyar ƙawar Inna kuwa ke dafo wata munafikar kaza wacce ba’acinta ma sai an kashe fitila kamar kazar tsafi , Sultana tabi ta rame ta ƙanƙance saboda masifar Inna da magunguna idan ma tace bata sha haka zata rufe ta da masifa sai tasha a karkaɗe kofi ,

     Ina fitowa daga wanka na hango Inna zaune gefen gado da ƙofinta riƙe a hannu , gabanta kuma kaskon garwashi ne , a takure nake tahowa dan ida bayyana a cikin ɗaki a tsawace tace min kiyi tafiya kamar kina da rai garwashin nan zai siƙe kuma kin sani sarai dakel aka samomin shi tunda gabanki nake ta nemansa tun safe , Inna shi kuma wannan ɗin na mene ne ? Na ubanki ne , tayi maganar tana kunce haɓar zaninta ta ciro wata “yar farar leda ta kwance tana ki wuto kizo ki duƙa nan , matsawa nayi kusa da ita nayi yadda ta nunamin ita kuma ta zazzage abinda yake cikin ledar duƙa tana cewa da kinsan ko nawa na siya saikin yaba ma ƙoƙarina , ko inda take ban kalla ba haka kuma ban bata amsa ba har ta uwarce ni dana tashi , tashi nayi ta miƙomin kofin ansa nayi nasha ta zuba ruwa na girgije na haɗiye , ɗaukar kwaskon tayi da kofin ta fita ni kuma na ɗauki kayana na saka na kwanta dan bacci nakeji bana wasa ba.

       Tana fita ɗakin mijinta ta wuce bayan ta ajiye kayan data fita dasu a kicin , ni kuma naci gaba da baccina , saida Dikko yayo mata waya yazo ta shigo dan taga ko na shirya ta ganni kwance ina bacci , cikin takaici ta tasheni bayan na tashi tace shine kinyi wanka ki iya ki shirya  kika wani kwanta bacci ? Ƙara takurewa nayi da niyar komawa bacci tace ki tashi idan kin ga dama ki gyara jikinki kafin in gama magana dashi yana ƙofar gida , cike da farin ciki na sauko daga saman gado Inna kuma ta koma palo tana jiran shigowar Dikko….

    Fuskata na wanke da bakina na fito , lokacin har Dikko ya shigo kuma Inna ta ratta mishi cewa saidai fa ya raba mana gida dan bazata yadda ba ɗiyarta tayi rayuwar takura , sundai yi maganarsu sun gama abinda dai naji Dikko yana bata haƙuri cewa shi babu macen data fi ƙarfinshi kuma gidanshi bai gagareshi yayi hukunci ba , inda yaso ya ajiye An mata bai gama aiki ba zaman na wani lokaci ne zasuyi kuma wani abu mara kyau bazai faru ba , Inna tace tou kai dole sai kayi auren ne yanzu ? Dikko yace ba dole bane ba lokaci ne yayi tunda ai ba yau naso muyi auren ba , Inna tace to gaskiya saidai ka bari idan ka gama aikin gidan sannan , mijinta ne yace ba’ayin haka idan bashi da ikon raba musu gidan ya zakiyi kenan ? Sai a fasa auren , ki daina haka ki musu fatan alkairi da addu’ar zaman lafiya , ba haka Inna taso ba dan na fahimci bata san gardama da mijinta , bayan sun gama ne suka shigo cikin bedroom in ita da mijinta , Inna tacemin kije ku gaisa farin ciki fal zuciyata na tun kari hanyar fita , zan fita daga cikin bedroom in naji mijin Inna yana cewa wai ba DK bane ba ? Inna tace waye kuma DK ? Bawan Allah cikin dai kokonto yace ba shi bane ba kamarsu dai tayi yawa wallahi shi wancan wanda nake magana bana tunanin ma zaizo nan , bata bashi ansa ba kuma sai suka rangaɗo suka biyo bayana suka fita daga ɗakin mijin Inna kuma yana ƙara kallon Dikko.

     Cike da farin ciki na isa wurin Dikko na rumgumeshi rabon da in ganshi ko inji muryarshi harna manta nayi faraicin lallausan jikinshi mai kama da bayan zomo , maimakon yaji daɗi ko yayi fara’a sai yace ke kullum sai kin hawomin jiki kamar wata mage ina dai lissafi kuma da guda² duk saina rama , gyara kwanciyata nayi saman jikinshi saida naja gemunshi sannan nace yanzu ma ka rama mana nayi maganar ina kallon cikin idonshi , murmushi duniyanci yayi cewa a , a ni na isa inzo har gidanku in rama abinda kikai min ? Zaki isko ni har gida saurin me kike ne ? Murmushi nayi ba tare da na sake magana ba , shi kuma yace meya sameki naji kin rage nauhi , da nayi niyar faɗa mishi abinda Inna takeyi amma sai wata zuciyar ta haneni kuma gaskiya dai idan ba’ayi hankali ba saina faɗa mishi abinda akemin !

     Shi kuma a ranshi tunani yakeyi kila fa itama An mata anayi mata irin abinda ake ma “yan gidansu idan za’ayi musu aure , jinjina kanshi yayi tare da cewa Allah ya sawaƙe idan kuwa anyi mata cutar yarinyar nan zaiyi da yawa , An mata kawo kunnenki in tambayeki , matsawa nayi tare da miƙa kunne ne saitin bakinshi cikin raɗa yace naji kin rage nauhi meya sameki ne ? Wata irin kasala naji ta lulluɓemin jiki na ƙara kwanciya sosai a lallausan jikinshi ban bashi ansa ba

      Shi kuma yaci gaba da cewa Mama take baki wani abu ko ? Kaina na ɗaga mishi alamar Eh , ɗago fuskata yayi idanuwanmu suna kallon cikin idon juna yace ai na sani hada kaza ko ? Shiru nayi ban bashi ansa ba , yace ai mu na gidanmu ina kallonsu wallahi hada tattabaru ake basu mutum yazo ya kasa cin abinci nasan kema hada irinsu ake baki ai ni gaskiya wannan shigamin haƙƙin rayuwa akayi gaki an takura miki an ramar min dake babu gaira babu dalili saboda ɗaukar alhaki , ni babu wata kaza da nake ci , hmmm haba An mata aiko baki faɗa nasan komai miye baƙona a mata ? Ya fara lissafe²n kayan mata kamar wata tsohuwar karuwa bayan ya gama yace sune baƙin nawa duk abinda na faɗa nasan aikinshi idan baki sani ba , Allah dai ya sawaƙe ya kuma kyauta wahala saukar min daga jiki karki shanye daɗin ke ɗaya….

      Murmushi nayi sannan na tashi na koma saman hannun kujerar da yake na zauna , mukaci gaba da firar duniya bana soyayya ba yana bani labarin abokin Yazeed da aka kama yace wallahi An mata fitinar zamanin nan yana bani al’ajabi saboda tsabar ƙazanta kina matar aure dan karnikanci kinabin mazan waje , ni na rantse da Allah da nine mijin idan nasa an kamashi Allah ya tsinemin , dariya yayi sannan yace dama ya sani yana riƙe banza yayi masa irin yadda akayi ma Saminu ya fashe idon dake ganin matan , nidai da nine ƙarya mishi wuya kawai zanyi ya mutu a rage annoba a ƙasa , dariya yayi yana kallona yace kiyi dariya mana , ƙinyin dariyar nayi kuma ban kalleshi ba , taɓoni yayi cewa An mata miye ? Ai kai dama baka iya komai ba daga duka sai kalmar kisa shikenan abinda ka iya faɗa , ke karfa ki raina min hankali , daga haka fira ya koma rigima wai wannan “yar maganar harya ɓatawa Dikko zuciya ni kuma bada wani manufa nayi maganar ba , tsoki yayi tare da miƙewa cikin ɓacin rai ya tunkari hanyar fita ,

       Binshi nayi da ido harya fita daga palon , saida ya fita na tashi nabi bayanshi har ƙofar gida amma banyi mishi magana ba , ina fitowa duk su Ashiru suka gaisheni cikin girmamawa kaɗan na ansa gaisuwar nabi Dikko da aka buɗewa mota kafin a rufe na riƙe murfin motar nace kayi haƙuri idan kaji babu daɗi insha Allah bazan sake ba , ba tare daya kalleni ba yace na yafe miki , yawwa ngode na bashi ansa sannan na juyo da sauri na dawo cikin gida , murmushi Dikko yayi yace kura ta fara lafiya yau wace rana bata biye an tashi hankali ba , murmushi ya sakeyi tare da kwaikwayon maganar Sultana wai da haka zatace naje nace mahaukaci aljannu kamar iccen tsamiya ! Hmm jarumata kenan….. Ina komawa kwanciyata nayi naci gaba da baccina dan yau su Hajiya Inna ba’a ɗakin za’a kwana ba…

        Inna da mijinta kuwa bayan sun fita daga palo mijinta ya tabbatar da Dikko ne dan haka yace ma Inna wane gigi ya kaita ? Shidai babu ruwanshi tunda dama tun farko ta ɓoye mishi wanda Sultana zata aura Dikko dai ba kanwar lasa bane ba , amma yana musu addu’ar zaman lafiya kuma bazaiyi binciken inda Sultana da Dikko suka haɗu ba tunda dama ba’a so ya sani…….

     Duk iskancin da Jiddah ta zaƙula ma “yan ganin ɗaki bai isheta ba Mardiyya ta tirota tace idan ta saki ta tsaya sanya za’ayi babu ita ta tadawa Dikko hankali a daren nan ta hana mishi bacci , shi kuma a gajiye ya fito daga toilet ɗaure da rigar wanka a jikinshi dan baya buƙatar komai a halin yanzu sai bacci , da masifa Jiddah ta shigo ɗakin kallo ɗaya Dikko yayi mata ya ɗauke idonshi daga kanta ya matsa inda ya ajiye kayanshi na jersey ya ɗauka ya saka ,

     Jikin socket ya matsa da niyar kashe fitila ta riƙe mishi hannu , kallon hannu yayi sannan ya kalli Jiddah na tsawon minti ɗaya yasa hannun haggunshi ya kashe fitilar ya koma saman gado ya kwanta , yana kwanciya ta kunna fitilar , jinjina kanshi yayi sannan ya sauko yazo ya kashe fitilar a karo na biyu , saida ta sake tabbatar daya kwanta ta sake kunna fitilar yanzu bai sauko ba yace kasheta , bazan kashe ba , ki kasheta nace , bazan kashe ba nace maka , rufe idanuwanshi yayi sannan yace ke…….. Ki kashemin fitila nace , a ɗan tsorace Jidda tace bazan kashe ba , cikin wata irin murya Dikko yace na rantse da girman Allah idan har kika bari na sauko daga gadon nan wallahi saina takaita miki rayuwa zuwa ɗaya zan miki na tasheki aiki har abadan duniya , da sauri Jiddah ta kashe fitila tayi waje da gudu tana kuka….

       Tsoki Dikko yayi tare da ɗaukar wayarshi ya fara kiran An mata , saida ya kirani so biyu ana 3n naji cikin faɗa yace wai ke An mata sai inta kiranki sai kin gama iskancinki zaki ɗauki waya , a sanyaye nace kayi haƙuri bacci nakeyi , nine baccin , kayi haƙuri bazanyi haƙurin ba duk kina nufin bakiji ina kiranki ba sai yanzu munafurci kawai , cikin ɓacin rai nace kai Dikko kaima munafurci , murmushi yayi sannan ya ɗaga idonshi dakel saboda baccin da yakeji yace nine munafurcin ko ? Haba kaima wallahi neman fitina gareka , tou yi haƙuri An matana raina ne ya ɓaci kuma bacci nakeji na fiso inyi bacci dake a raina kiyi haƙuri don Allah idan dake ne zanyi bacci idan bake bace wallahi bana iya bacci raina zaiyi ta ɓaci a banza kiyi haƙuri mu raba ɓacin ran kin yafemin ko ya ƙarasa maganar yana jan wani irin numfashi mai ɗauke tunani yace muyi bacci mai daɗi ki ga Dikko a baccinki jarumata ,

     Shiru nayi banyi magana , a kasalance ya kira An mata cewa meye ? Dakel na haɗiye miyan bakina banyi magana ba har yanzu , An mata…. ? Na’am , Dikko ne ? Umm tou yi haƙuri kinji zanyi bacci na gaji saida safe ya kashe wayarshi , yana kashe wayarshi yaci gaba da baccinshi cikin natsuwa da kwanciyar hankali saɓanin Sultana da bacci ya gagari idonta ,

    Dikko baida adalci gaskiya shi kanshi kawai ya sani , matarshi ta ɓata mishi rai akan me zai kira wata da bataji ta gani ba kuma bata san anyi ba ? Ita Jiddah me yasa bayacin ubanta yadda yake ma Sultana ? Danni nayi imani da Sultana ce ta kashe fitilar nan wallahi sai Dikko ya zaneta , amma ita Jiddah sai tayi kwance² ta ɗana iskancin ta amma Dikko baya zane mata jiki irin yadda yake ma Sultana me ne ne dalili ? Shin san Jiddah yafi ko kuwa …..?

      Ranar da akaje jere ma Jiddah ta ɓara iskanci wanda yafi wanda tayi ranar ganin ɗaki , ta tara ƙawayenta ƙosashshin “yan iska kuɗin mota ta turama ko wace har naira dubu ɗari wai suzo su tayata tarar kishiya sun cika gidan ba masaka tsinke sai iskancin suke zazzagawa wallahi zaman jere bai yuwu wurin mata ba maza ne kaɗai suka tsaya dan kayan na ɗaurawa ne kunga kenan ba aikin mata bane na maza ne , ko iri ɗan tukuicin nan da ake badawa na jere duk Jiddah ta murjeshi ta hana , dama na ganin ɗaki ma bata basu ba , kai Jiddah riƙaƙƙar “yar iska ce mai tikiti lallai Dikko ya ɗauki alhakin Sultana da zai haɗata zama da Jiddah…….

     Bayan tafiyar matan suka faɗa kicin ita da ƙawayenta wai wannan kulolin da duk wani abu da aka saka mata yafi ƙarfin sayen ɗan caca dan haka tasa suka kwashe duk abinda take so aka kai kicin inta , ita kuma Mardiyya an tsaida ita a kicin tana dafawa Dikko da baƙinshi abincin da zasu ci sai waya yakeyi a kawo , “yar kwalbarta ta jawo daga cikin breziya ta kakkaɓe maganin ta kaf a cikin abinci , hamdala tayi ga Allah bayan ta tabbatar ta gama zubawa…..

      Banda faɗuwa babu abinda gaban Inna keyi ganin taron mata sun dawo suma kansu sunji tsoron Jiddah ina ita Sultana ? Ƙaramar yarinya wacce shekarunta bai kai na Jiddah ba gaskiya zalinci yasa Dikko zai haɗa mata “ya zama da Jiddah , da tsausayi ta kalli inda Sultana take tana shiri Dikko ya turo Ashiru ya ɗaukota ya kawota wurinshi bayan yace masa wai kar yayi tuƙin ganganci kuma karya biyewa kowa yayin daya hau titi ya ɗauka duk wanda ke saman titi mahaukaci ne shi kaɗai ne mai hankali , hijabi Inna ta bani na saka bayan na gama shirina , saida ta rakoni har bakin get ta koma ni kuma na fita na shige mota muka tafi….

     Kallon kaina nakeyi a zahirance wai in banda abin Inna taya zata sadani da hijabi ? Wannan ma idan wani ya ganni ai sai a rainani umm to ya zanyi ? Haƙuri kawai zakiyi Maryama….

       Tun daga ƙofar gida har cikin gidan motoci ne , sai dawakai da aka tara a wajen gidan da ciki ƙosashshi “yan gayun dawakai masu tsada wata irin haniniya sukeyi sun karaɗe kaf illahirin wurin da kuka , ciki Ashiru ya shiga ya samu wuri yayi parking sannan ya turawa mai gida saƙo isowarmu ,

      Shima rubuto masa yayi wai mu shigo yana ciki bayajin daɗi cikinshi ke ciwo , da Ashiru ya faɗamin cewa nayi bazan shiga ba idan baya fitowa ya bari , a , a ranki ya daɗe kiyi haƙuri mu ki shiga , wallahi bana shiga idan bazai zo ba ya bari yasa an ɗaukoni tun daga gidanmu nan ɗinma bazai iya zuwa ba ? Idan yana zuwa yazo idan baya zuwa can shi ta matse mawa….

     Tura masa yayi cewa bazan shigo ba , yace gashi nan yana zuwa , fita Ashiru yayi daga motar yana cemin ki jirashi yana zuwa , ya daɗe sosai sannan ya fito mutanen da basu gaisa ba suke gaisawa bayan ya gama ya taho wurin motar ,

       Gaba ya buɗe kujerar mai zaman banza ya ziro ƙugunshi ya zauna a gajiye ƙafafuwanshi a waje bai rufe motar ba , kwantar da kanshi yayi jikin kujerar yace wallahi bansan abinda ya sameni ba cikina kemin wani irin ciwo kamar zan mutu , ai idan ka mutu ka huta , Eh na huta ke kuma taki ta ƙare juyowa yayi ya kalleni sannan yaci gaba da cewa ai nasan idan na mutu ɗan ƙaramin hauka zakiyi sai kin riƙa kwacewa ana riƙoki , tou ka mutum ka gani idan zanyi haukan , hmmm yarinya kenan kina wasa da lamarina An mata , nima kana wasa da nawa lamarin kedai kika sani , kaima ka sani dakel yayi “yar gajeriyar dariya tare da duƙar da kanshi ya riƙe cikinshi yace wai Allahna…..

     Jikinshi yana wata irin kyarma ya kwantar da kujerar daya ke zaune kai yana cewa matsa daga nan ke , gefe na matsa yana cewa kin dai yafe ni ko ? Tou zan mutu in mutu ? Wata irin ƙara nayi cewa ban yafe ba Dikko dake duƙe ya riƙe ciki da sauri ya ɗago yace mene ne kuma ? Ajiyar zuciya na sauke na kalleshi murmushi yayi cikin ƙarfin hali idonshi ɗauke da hawaye kaɗan yace ya akayi ne wai ? Fashewa nayi da kuka nace mafarki nayi zaka mutu yanzu , murmushi ya sakeyi cikin jarumta yace ina nan zaune kikayi baccin ?  ya ƙarasa maganar yana min wani irin kallo , tou amma na ganka ka kwanta kace zaka mutu , Dikko yace anan ɗin na kwanta ? Eh , ba kin ganni gani nan zaune ba ? Idan ba kaine ba waye ? To ni An mata ya za’ayi in sani ? Wallahi na ganka , hannunshi ya miƙomin na riƙe yace ke… wai mene ne ? Ko yunwa kike ji ne ? A , a , banajin yunwa kalli idona in ganki , kallonshi nayi shima ni yake kallo bayan wani lokaci yace ya isa haka fita muje ya fita……..

       Ƙin fita nayi ina tunani to wai idan ba Dikko bane ba waye ? A dai² lokacin daya buɗe murfin motar ya fiddoni yana cewa yunwa nakeji amma banajin zan iya cin abincin can gaskiya…….

(function loadPageAds() { return afriPageAds({ ‘pid’: 8612, ‘uid’: 9740, ‘t’: ‘300 by 250’, ‘url’: ‘https://2gnblog.blogspot.com/’ }); }());

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button