MAKAUNIYAR KADDARA 51

 

*page 51*………..Kamar jira ƴan kawo amarya na wucewa Farah ta farka, sai dai a yanayin data farka ɗin yay matuƙar tada hankalin su Mammah, AK daya tuna cewar tana tare da ciki ya cema Dr Mahmud suje asibiti kawai kar a rasa abinda ke cikinta. Mammah ce tai azamar son dakatarwa Mahma ta tsaidata itama ta hanyar faɗin, “Maganar Abdul-Mutallab nakan hanya, hakan shine yafi dacewa kar azo ana dana sani kuma daga baya”.

        Cikin tashin hankali aunty Zakiyya tace, “Mahma kubarta-fa komai zai dai-daita, inaga ya ƙara mata allurar barcin sai mu wuce can gidan da ita dan Abban Ameera ya kirani cewar wanda zai kawo mana key ɗin ya iso yana can yana jiranmu”.

      “Addah abi shawarar Zakiyya ɗin na tabbatar shock ne zata dawo dai-dai idan ta ɗanyi nesa da nan ɗin kamar”.

      Ak dake binsu da kallon mamaki ya dafe kansa dake neman fara masa ciwo, dan shikam dai abubuwan na neman masa yawa gsky. Mahma da wani tunani yazo mata a zuciya tace, “To babu damuwa kai mata allurar kawai sai mu wuce”.

      Kallon AK Dr Mahmud yayi, “Amma ranka ya daɗe karfa allurar tai mata illa, ni bansan ma tana tare da ciki ba da ban mata ita ba, tanada ƙarfi, nayi mamakin ma data farka a yanzu dan allurar mai ƙarfice”.

       Karan farko AK ya saki ɗan murmushi, dan shikam dai zuciyarsa ta fara raya masa wani abu game da yanayin Mammah da Aunty Zakiyya, ya ɗan lumshe idanunsa ya buɗe da gyara tsaiwarsa. Cikin rashin sakewarsa yace, “Kaga yimata ɗin kamar yanda sukace, dan a ganina zamanta a farken yafi allurar zama matsala ga lafiyar tata”.

       Kai kawai Dr Mahmud ya gyaɗa masa, dan shikam dai baimaga wani alamun ciki a jikin Farah ɗin ba. Yana ƙoƙarin haɗa allurar yace, “Amma cikin nata yakai wata nawane?”.

      Shiru Mammah da aunty Zakiyya sukayi, sai Mahma ce tace, “Kamar dai biyar ko”.

     “Biyar fa?”.

Dr Mahmud ya ambata mamaki ƙarara a fuskarsa. Ɗan duban Farah ɗin dake riƙe jikin Mammah tana kuka da wani ɗan fisge-fisge yayi ya ɗauke kansa. Batare da yace komaiba yay mata allurar kawai ransa fal wasiwasi.

     Yana gama mata allurar ko mintuna biyar ba’a ƙullaba barci ya ƙara ɗaukarsa. Kallon AK Mahma tayi da cewa, “Taimaka ka kai mana ita mota Abdul-Mutallab, ku kuma kumuje shima ya samu ya huta”.

       Babu shiri Mammah tace, “Addah ai shine zai kaimu, taya matarsa na wannan halin yaga wani ta hutu?”.

     Murmushi Mahma tayi na takaici, muryarta aɗan hasale tace, “Duk mu da muke tare da ita bai wadatarba sai shi ya kasance a wajen?. Ai ya kamata a tausaya masa ya huta ga kuma yarinya an kawo zai barta ita kaɗai kenan komi?”.

      A take Mammah ta sake tamke fuska matuƙa. Ta kalli AK da yay tamkar bayama jinsu yanata latsa waya. Sai kuma ta maida kan Mahma, “Addah to in hakane muyi kwanciyarmu anan ɗin kawai basai yayi wahalar da kike gudar masanba..”

     “Bazai yuwuba, tunda dai ga gida can da zamu zauna mu kaɗai bamu takura kowa ba, ba’a takuramu ba, can zamuje. Abdul-Mutallab ɗauketa”.

     Yanda Mahma tayi maganar babu wasa a ciki ya sakashi zura wayarsa aljihu ya tako a hankali inda Mammah ke rungume da Farah. Ɗaukarta yay cak ya fita da ita duk da nauyin datai masa saboda yanda jikinta ya saki sosai. Duk yanda Mammah keta kumbure-kumbure Mahma batabi takantaba ta tasasu gaba suka fice suma. Dan ita aunty Zakiyya ma ta ƙagu subar nanɗin dama suje inda takeson amayar da abinda ke a bakinta.

      Aunty Zakiyya ce ta jasu. Suna ficewa daga gidan AK yaɗan lumshe idanunsa da murza goshinsa yana furzar da huci. Sai kuma yay murmushi da girgiza kansa saboda harar da Mammah keta faman antaya masa da gargaɗi da idanu.  

       Juyawa yay zuwa cikin gidan dan shima wani ma zazzaɓi-zazzaɓi ke neman rufesa, sashen Farah ya koma ya kashe komai da maida ƙofar ya rufe, koda ya fito sashensa ya nufa dan yafi buƙatar watsa ruwa a yanzu.  

      ★★★

    A ɓangaren Zinneerah kam kuka taci sosai, sai da Mahma ta leƙo tai mata sallama akan suma zasu wuce, ta kuma ɗan lallasheta da ƴar nasiha sannan ta sassauta. Fitsarin da takejine ya sakata tashi dole ta shiga toilet ɗin ɗakin tayo, tana fitowa ta sake komawa saman gadon ta kwanta dan zazzaɓi takeji yana neman rufeta ga ciwon kai. Ba tare data damu da cire komai ba ta kwanta a haka dajan bargo ta lulluɓa har kanta saboda sanyi da takeji yana ratsata. Ga kuma ac a ɗakin dake aiki ta kasa kashewa.

        Batafi mintuna goma da kwanciyarba barci ya kwasheta sama-sama. A ɗan firgice ta farka saboda ƙarar buɗe ƙofa da taji, ta ƙanƙame jikinta waje guda jin tabbas mutum ne ya shigo. Sai dai ta kasa ko motsi saboda yanda zuciyarta ke wani harbawa da sauri sauri na tsananin tsoron wanda zataci karo da shi a matsayin mijin nata.

      AK da tun shigowarsa ɗakin idanunsa suka fara sauka akanta ya cigaba da takowa cikin ɗakin a hankali sassanyan ƙamshin turaren wutar da ɗakin yaji, da ƙamshin sabbin furnitures dana fenti na rige-rigen shiga masa hanci, a hankali ya sauke ajiyar zuciya yana ƙarasawa gaban gadon sosai. Hannayensa ya tura duka biyu cikin aljihun wandon blue pyjamas ɗinsa har lokacin idanunsa akan Zinneerah dake ƙudun-dune cikin bargo zuciyarta na nemam faso ƙirjinta ta fito.

       “Assalamu alaiki”. Sassanyar muryarsa ta daki cikin kunnuwanta. Sosai ƙirjin Zinneerah ya buga fiye da farko, dan idan har babu kuskure ai muryar Yayansu taji kam. ‘Kai ina ganganne’ ta ayyana a zuciyarta dake raunana.

       “Nasan ba barci kike ba”. Ta ƙara tsinkayar muryar tasa a karo na biyu, a yanzu kam kasa jurewa tayi dole tai ƙasa da bargon a hankali daga saman fuskarta. A hankali ta buɗe idanunta zuciyarta na gudu dai-dai da jinin jikinta dake tsinkewa daga cikin jijiyoyinta. A wani irin firgice ta yaye bargon babu shiri tana miƙewa zaune jikinta na rawa. “Y…y….Yayanmu!”.

      Ta faɗa da wani irin kiɗimammiyar murya dake nuna tsantsar tashin hankalinta a fili. Sosai yanda tayi ɗin ta bashi dariya, amma sai ya daure ko ɗigon fara’a babu a fuskarsa, sai dai idanunsa kafe suke a kanta ko ƙyaftawa bayayi yana ƙarema ƙwalliyar tata kallo, dan zaburar da tayi ta saka lafayar warwarewa daga saman kanta zuwa jikinta. Sai baƙar rigar jikinta mai dogon hannu data lafe da bayyana  ainahin surarta da gyaran da fatarta ta samu wajen hajiya Falmata.

           Janye idanunsa dake binta da kallon yayi yana maidawa akan fuskarta, ganin yanda take ɗan ja baya da rawar jiki laɓɓanta na rawa alamar sonyin magana ya sakashi lumshe idanu ya sake buɗewa a kanta yana zare hannayensa daga aljihun wandon barcin nasa. Cikin nuna rashin damuwa da yanayin nata ya kai zaune a bakin gadon yana facing ɗinta. Hannunsa ɗaya yakai akan goshinsa yaɗan shiga murzawa. Sai kuma ya ɗago ya dubeta da birkitattun idanunsa dake rikitata, batare da yace uffanba ya miƙa mata hannunsa ɗaya alamar tazo.

     Kanta ta shiga jujjuyawa tana ƙara nanema fuskar gadon, hawaye na gudu a saman fuskarta kamar an buɗe fanfo. “Yayanmu dan ALLAH kace bakai bane ba”. Ta faɗa cikin tsananin rauni da rawar harshe.

      A karan farko ya ɗanyi luuu da idanunsa da sakin guntun murmushin da ita ko alamarsama bata ganiba, ya ɗan ƙara ware idanunsa a kanta da kai hannunsa ya shafi sajensa dake a kwance luf duk da ba gyaransa yay ba, dan koda yay wankan ma turare kawai yasa da kayan barci ya fito domin dubata. Cikin muryarsa ta rashin sakewa yace, “Bani bane mi?”.

1 2 3 4Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button