BAKAR WASIKANOVELS

BAKAR WASIKA 2

Page -2️⃣

“Akwai abubuwa da yawa da rayuwa bata iya tafiya sai da su, a ciki akwai numfashi ci da sha, da kuma soyayya. Bana jin zan iya rayuwa idan babu kai a kusa ni, zan iya rasa ci da sha kuma na rayu da soyayyarka”

Ta nade wasikar da ta gama rubutawa da hausar azami, tana murmushi sannan ta mike tsaye ta maida biron da littafin cikin jakarta ta islamiya ta rataya a jikin kusar dake gurin sannan ta saka hijabinta ta fito.

“Inna an gama?”

“Auta tun dazun na gama, kin yi sallah dai ko?”

Ta saka wasikar a cikin jikinta tana murmushi.

“Inna ke ma kin san bana wasa da sallah fa”

“Haka ne, Auta Allah ya miki albarka”

Inna ta fada Baba da ke zaune saman tarbarma yana sauraren redio ya amsa da Ameen yana murmushi. Sanusi ma dake aikin auna tuwon dawo a bakinsa ya so ma zolayarta kamar yadda ya saba.

“Ku na fasa mata kai da wannan kafafuwan nata kamar itace”

Aiko kamar jira take sai ta fara kukan shagwaba, musamman ganin duka gatanta suna nan Inna da Baba.

“Baba kana jinsa ko?”

Baba yayi dariya tare da kai hannunsa ya kashe redio dake gefensa, ya tofar da goron bakinsa. Yai mata alama da ta zo da hannu, kamar jira take sai ta karaso inda yake tana ta turo baki ita ala dole an taba ta.

“Auta Mamana, ki daina biyewa Sanusi, shi da yake ragon maza, ke da kike Jaruma, ki daina nuna musu rauninki, kin ga shi kin ga Rilwanu ki daina bari suna saka ki kuka, da an miki aure sai kun yi ta marmarinki”

Ta rufe ido da sauri cike da tsantsan kunyar irin ta ya mace bahaushiya. Hakan da tai sai ya kara saka Baba murmushi.

“Allah ya miki albarka ya nuna mana lokacin Autata”

Kasa amsawa tai da ameen domin Aminatu irin yan matan nan ne masu kunya da kawarda ido ga wasu abubuwan. Sai kawai ta mike tsaye har lokacin bata janye hannunta daga fuskarta.

“Wai kunya take, kunya kike kika yarda kina fita zance”

Sanusi ya fada yana dariya, a cikin hasken farin watan Aminatu ta watsa masa harara. Ta nufi inda kwallar tuwonta take ta nada ganwo ta dauka ta dora a kai sannan ta mika dayan hannunta ta dauki miyar dake cikin bokitin roba.

“Ni na tafi gurin sana’a ta”

Ta fada tana kara murda masa baki, Inna dai bata ce komai ba bayan murmushin da tai. Har ta kai bakin kofar fita daga gidan sai Baba ya kirata.

“Mamana”

Ta juyo.

“Na’am Babana”

“Allah ya miki albarka”

Sai ta amsa tana kallon gefen Sanusi.

“Ameen, yan bakinciki sai dai su mutu”

Ba Inna da Baba da Sanusi kadai ba, har Rilwanu da Iro da suka shigo yanzu sai da suka saka dariya, domin sun san tatsuniyar gizo bata wuce ta koki, inda Aminatu ta yi habaici ko shagube to ba zai wuce Sanisu ko Rilwanu ba take yi ma.

“Mai tuwo a bani na hansin”

Ko kallon Rilwanu ba tai ba ta saka kai ta fice tana cinno baki gaba kamar zai zazzago ya zubo kasa. Kusa da Baba suka zauna ko wane ya aje bindigar maharba da manyan wukaken dake hannunsu. Kana ganinsu ka ga zaratan jarumai, tun daga kirarsu har yanayin shigarsu da muryarsu. Domin suna daya daga cikin manyan yan saka na yanki, abu ne mai wahala ka ga gidan da ke da maza uku ko hudu baka samu yan sakai a gidan ba balle kuma gidansu Aminatu da suke da maza bakwai. Ba wuka ba ko bindiga bata huda mahaifinsu balle kuma su da suke shiga dajijikan kauyen neman barayi da kansu.

Tana yin nesa da gida kadan sai murmushi ya wanke mata fuska, a cikin abubuwan da tafi kaunar a rayuwarta akwai yan’uwanta, musamman Rilwanu Sanusi da Musa, domin sun fi sauran sake mata, da kuma kyautata. Gashi basa yarda ko da wasa wani ya nuna mata yatsa a waje balle har a taba ta.
A natse take tafiya, tana ta mikawa mutanen data sani kuma suka santa gaisuwa cikin girmamawa, musamman abokan mahaifinta, sai da ta kusa dandali sannan ta rage saurin tafiyarta da alama akwai wanda take jira ko take son hangowa, can kuma ta ja ta tsaya ta juyo tana kallon hanyar data fito sai ta hango masoyinta tafe da saurinsa cikin shigar kananan kaya, murmushi ne ya cika fuskarta, sai ta sauke idonta kasa domin bata jin kunyarta zata barta tai ta kallonsa har ya karaso inda take.
Sai da yai wani gyaran murya ya waiga ya ga babu mai ganinsu sannan ya ce.

“Auta”

“Na’am barka da dare”

“Yau ina fitilarta?”

Sai da yai maganar ta tuna da zancen wata fitila, sam ta manta bata zo da ita ba, sai a yanzu ta suna ta bar fitilar a dakin Inna bayan ta gama rubuta wasikar.

“Wallahi na manta ta”

Ta fada tana dukawa ta aje bokitin miyar dake hannunta, sannan ta saka hannu a cikin zanenta ta dauko wasikar ta mika masa, ya karba da dayan hannunsa dayan hannun kuma ya mika mata tasa wasikar.

“Na je gida na karbo miki?”

Ta zaro ido.

“Kai Baba yana nan fa, ni ban saba aikin maza a gidanmu ba”

Yayi yar dariya yana kokarin magana suka ji muryar Sanusi.

“Auta…”

Ba karamin tsoro Aminatu ta ji ba, domin bata saba tsayuwa da maza har a ganta ba, duk kuwa da kasancewar ta kai munzalin da zata iya yin hakan, amman kunya da tsoron yayyunta ya hana ta yin haka, duk inda ta san idan ta tsaya da wani za a gani ayi mata magana ko fada bata yarda ta tsaya a gurin. Maniru ne ya soma wayancewa ya mikawa Sanusi hannu suka gaisa, Sanusi ya amsa yana musu dariya.

“Ka ce na zama yaya daga yanzu”

Maniru yayi dariya Aminatu kuma ta duka da sauri ta dauki bokitin miyarta daman tuwon yana saman kanta.

“Ga fitilar in ji Inna”

Ya mika mata yar karamar touch light din dake hannunsa, sai ta karba da sauri ta juya ta cigaba da tafiya cike da tsananin kunya gabanta sai faduwa yake. Sai da tai nisa sannan Sanusi ya kalli Maniru ya ce.

“Maniru idan kana son Aminatu ai gidansu ya kamata ka ta fi ba wai ka rika tare ta a hanya ba, amman irin wannan ai ba lallai ne kowa yai maka fahimta mai kyau ba”

“Wallahi Sanusi ina son zuwa, ita take hana ni, sai tace tana jin kunya kuma yayyunta za su iya mata fada”

Sanusi yayi dariya.

“Shirmen ta ne, ba a aure mu za mu yi, idan ka shirya kawai ka min magana zan sanar da Baba sai a komai cikin mutunci”

“Maa Shaa Allah, na gode sosai daman ni abun da nake nema kenan domin na gaji da zageye zageyen nan Wallahi”

“Inshallahu zan yi magana da Baba, duk yadda ake ciki zaka ji”

Sai da Maniru ya sake mika masa hannu suka gaisa sannan ya wuce yana ta jindadi abun nema ya samu.
Aminatu na daya daga cikin irin yan matan nan da suke da farin jinin siyarda sana’a musamman a dandali duk kuwa da kasancewar ba wani kula samari take ba, amman abu ne mai wahala ta je da tuwo ta dawo da shi sai ta saida kaf wani lokacin ma har ta karbi na wasu ta siyar musu, saboda tsabtarta da kuma dadin miyar Inna. Har ta gama sai da tuwon ta nade komai nata a guri daya Wasikar da Maniru ya bata tana cikin jikinta, a dayan bangaren kuma tana ta tunanin yadda zata shiga gida, domin ta san abu ne mai wahala ace Yayanta Sanusi be fada cewar ya ganta da Maniru ba, ba fada kadai ba wata kila har doka sai ta sha a gurin Yayanta Amadu. Da gangan ta ki yarda ta je gida da wuri duk kuwa da kasancewar ta siyar da tuwonta a cikin lokaci, sai ta zauna a gurin tana ta kallon mutane fuska ba yabo ba fallasa, ba zaka iya karantar damuwarta ba, sai dai hakan kuma be isa ka fadi cewar tana cikin farinciki ba.
Har kusan 11 na dare bata tafi gida ba tana zaune a gurin sai ta fakaici idon mutane sai ta matse yan kwalla da suke cika mata ido, sai kuma ta dan turo baki, sai kallon mutanen dandalin take sai ka rasa wa take turowa bakin. Ganin babu sarki sai Allah yasa ta mike tsaye ta dauki robar ta dora a kai tai ma abokan sana’arta sallama, ta fara tafiya kamar bata son zuwa, ta san inda bata je ba sai an aiko nemanta kamar yadda ake idan ta dade bata dawo ba, dan haka bata da wata mafita data wuce ta koma gida.

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button