HAUSA NOVELKADDARA Complete Hausa Novel

KADDARA Complete Hausa Novel

“Nayi kyau Mom”Tajdeen ya faɗa ya na taɓa hannuwa alamun jin daɗi,jan shi tayi zuwa waje inda Dad ke zaman jiran su.
Mota ya shiga yana ɗaga ma Mom hannu yayinda Dad ya figeta zuwa goudron.

Sun yi ƴar tafiya mai ɗan nisa kafin su ke tsayawa gaban ƙaton get ɗin école/school ɗin,hannun shi Dad ya kama ya kai shi har cikin class ya zaunar da shi sai da lokacin fara karatu ya kusa sannan Dad ya bashi kuɗi ya juya zai komawa ai kam Tajdeen yace bai san wannan ba.

Cikin shagwaɓar da ya ya koya tun farko zuwan shi cikin ahalin ya riƙe Dad yace “Please Dad kar ka tafi ka bar ni ban san kowa ba tsoro ni ke ji”rage tsawo Dad yayi cikin sigar rarrashi yace “ka zauna yanzu zan dawo ɗaukar ka da zarar kun gama karatu”kafaɗa Tajdeen ya maƙe ya na mai shigewa jikin Dad,wani ɗan yaro ne daidai sa’ar shi ya taso daga inda ya ke ya kama hannun Tajdeen yace “Friend zo mu tafi ka ƙyale Dady”kallon Dad Tajdeen yayi ya jinjina mashi kai alamun su tafi kafin ya shafa kansu yana mai tambayar yaron sunan shi “Junior”ya ba shi amsa,bye-bye suka ma Dad kafin su ke zauna saman table Junior nayi ma Tajdeen hira har Madam ɗin da za ta koya masu ta shigo.

Karatu tayi masu daidai yadda kwanyar su za ta ɗauka,sosai kam suka gane dama sunayen abubuwa irin su dabbobi ,kujera,allon rubutu sune ta koya masu.

Lokacin récréation nayi duk yaran suka nufi resto nan kowa ya shiga sayen abinda ya ke so.Tajdeen na cin biscuit ya dubi Junior yace “miyasa duk ƴan garin nan fatar ku iri ɗaya ce tunda na zo ban ga baƙar fata ba,kuma naji ku na Yaren Hausa?”amsa Junior ya bashi da “eh mu ba African people ba ne asalin ƴan Indonesiya ne yaƙi ne ya shigo damu ƙasashen baƙar fata” “minene Indonesiya?”Tajdeen ya sake tambayar shi”da hannu Junior yayi mashi alama da oho kafin yace “nima ban sani ba na dai ji Mama na faɗa ne”.Kallon students ɗin Tajdeen ya shiga yi kamar mai son tantance wani abu zuwa can ya nisa yace “toh miyasa ba’a sallah nan garin?”kallon ban gane ba Junior yayi mashi hakan yasa Tajdeen miƙewa ya fara gwada mashi yana Allahu Akbar sai yayi ruku’u,dariya Junior yayi yace “minene kuma wannan?”tsayawa Tajdeen yayi yace “ita ce sallah a gida na ga Anya da Kaka ta nayi kuma friday muna zuwa masallacin juma’a muyi ibada da bautar Ubangiji”da sauri Junior yace “oh yanzu na gane nan kuma duk saturday ne muna zuwa gidan bautar Ubangij,tashi mu shiga aji lokacin komawa yayi”nan suka miƙe suka shiga Madam ta cigaba koyar da su har sai ƙarfe ɗaya tayi sannan aka tashe su.

Tajdeen na ganin Dad ya ruga ya rungume shi cike da murna “ina abokin ka?”Dad ya tambaye shi “yanzu Mama ta zo tafi da shi” “ok!to ya karatu ka na dai ganewa ko?”Dad ya faɗa yana jan shi zuwa mota,”eh sosai ma”nan Tajdeen ya shiga karanto ma Dad abinda aka koya masu inda bai yi daidai ba sai Dad ya gyara mashi har suka iso gida.A zaune Père ya ke yana duba jarida sai ji yayi Tajdeen ya faɗa jikin shi yana ihu, rungume shi Père yayi yana jin son jikan na shi yace “i miss You Deen shine ka tafi makaranta ba kaje kayi min sallama ba ko?”zaman shi ya gyara kan cinyar Père yace “ai lokacin ka na kwana kuma Mom tace ka sha magani ne na barka ka huta”dogon hancin shi Père ya ja yace “haka ne maza tashi ka cire uniforme ka zo ka ci abinci sannan nima ka koya min karatun da aka yi maku”da “toh”ya amsa ya nufi ɗakin Mom da gudu sac a hannu yace “Mom na dawooo”rungume shi tayi sannan ta cire mashi uniforme tayi mashi wanka ta saka mashi kayan shan iska.Abinci ta fara bashi a baki sai da ya ƙoshi sannan ta fara mashi tambayoyi kan karatu.

 

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya kullum Dad ke kai Tajdeen school in lokacin tashi yayi kuma ya ɗauko shi yayinda Mom ita ke koyar da shi lesson.
Kasancewar Tajdeen curieux tun dama can farko hakan yasa karatu bai bashi wuya dan yana fahimta sosai,a gida kuma kullum SHENEL ɗin turanci da French ya ke kallo wannan ya ƙarfafa ma karatun shi inda a ƙarshen shekara ya zo na ɗaya cikin ajin su.

Hutun shekara wato vacances da suka shiga shi ya ba Tajdeen damar zama kullum a gidan wannan lokacin ne kuma ya ƙara fahimta lalle Raj na baƙin cikin ganin shi a gidan hakan yasa bai sakewa a duk lokacin da Raj ke wurin.

Shirye-shiryen bikin Raj bai ɗauki lokaci ba aka yi biki inda suka tare a gidan Père ,tun shigowar Avani ba su taɓa shiri da Vani ba wato Mom duk dan saboda Tajdeen a cewar Raj Père ya ɗauki soyayya ya ɗorawa Deen yanzu ko sun haifi yara ba su da wani gurbi sosai cikin zuciyar Père ,da ya ke ita ma Avani sokuwa ce sai tabi ra’ayin mijinta.

 

Tajdeen na da shekara goma sha biyu ya samu matsalar memory sakamakon dukan kawo wuƙar da Avani tayi mashi tana ta buga kan shi ga mure ita niyyata ta kashe shi kowa ya huta dan shekara cikin ta uku kenan da auren su har yanzu ba ta samu ciki ba.
Duka ahalin gidan tsaye suka yi cirko-cirko tsakiyar asibiti tunda Dr yace Tajdeen ya samu matsalar memory ba su tsaya jin ƙarin bayani ba duk suka ruɗe.
Dad ne ya shigo da mota a tsiyace ko wani ƙwaƙwaren parking bai yi ba ya fito,”mi ya samu Deen ɗin?”shine tambayar da yayi yana kallon Mom cikin kuka ta fara yi mashi bayani “mu na can gidan bauta ne sai Avani ta kira tace Deen ya faɗo daga sama ya mutu sai..sai….”kuka ne ya ƙwace mata jijigata yayi cikin tashin hankali yace “sai mi?”ganin ba za tayi magana ba ne Rahul yace “sai muka dawo gida shine muka tarar da shi cikin jini,sai muka kawo shi asibiti nan Dr ya tabbatar ma mu da ran shi matsalar memory ce ya samu”da sauri Dad ya dafe saitin zuciyar shi wace ke bugawa da ƙarfi tun lokacin da aka kira shi aka shaida mashi.

Riƙe shi Rahul yayi yana ƙarƙafa mashi gwiwa na su gode ma Allah tunda da ran shi kuma kar su fidda ran zai samu sauƙi.Ihu suka ji game da kuka Tajdeen na kiran sunan Mom ,da sauri suka nufi room ɗin da aka kwantar da shi.
Ƙoƙarin tashi ya ke amman ya kasa,an naɗe kan shi da bandeji sai ƙarin ruwan da aka maƙala mashi a hannu.Rungume shi Mom tayi tana hawaye tare shafar kan shi,cikin kuka yace “Mom mi nayi ma Mom ƙarama…”kasa ƙarasawa yayi ya dafe kai sakamakon wani irin sarawa da yayi mashi,jini ne ya shiga ɓulɓulo mashi ta hanci daidai nan kuma Dr ya shigo ya nemi alfarmar su bashi wuri ya duba shi.Waje suka fito suka tsaya bakin ƙafo,kujera Père ya samu ya zauna dan wani irin jiri ne ke ɗibar shi.Can wajan kamar rabin sa’a Dr ya fito murmushi kan fuskar shi yace “madallah an yi sa’a bai rasa memryn shi duka ba zai iya tuna wasu abubuwa uwanda suka wuce kamar na 2ans/years passé haka,sannan za’a sallame shi nan da 3days tunda jinin da ya toshe wani ɓangare na ƙwalwar shi ya samu ya fito sai dai wanda ba’a rasa ba”Dr ya faɗa yana mai miƙa ma Ranvir takarda da za’a sawo magani dan ya ga shine kawai ke da nutsuwa,”zamu iya shiga yanzu?”Dad ya tambaya kamar zai yi kuka “eh toh amman da dai kun bar shi ya huta”kai kawai Dad ya ɗaga gabanin ya kalli Rahul yace “ka ɗauki Père ka mayar da shi gida zuwa gobe sai ku dawo”kai Rahul ya jinjina tare da cewa “Tom. amman in ana buƙatar wani abu fah?bari na kai Père sai na dawo” “kar ka damu ga Ranvir nan ai”.
Miƙewa Père yayi tsaye sannan yace “Vani wuce mu tafi tare sai ki girka abinda zaku ci ki tawo da shi”ya na gama faɗar haka yayi gaba,ba dan Mom ta so ba tabi bayan shi ya rage daga Dad sai Ranvir a asibiti.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button