HAUSA NOVELKADDARA Complete Hausa Novel

KADDARA Complete Hausa Novel

 

Wani gigitacen mari ne ya kifa mata wanda sai ta ga gilmawar wasu taurari kafin ta dawo daidai ta kuma jin wani,cikin ɗaga murya ya ke mata masifa akan bugun Tajdeen da tayi.Ya daga hannu zai sake kwaɗa mata wani marin Père yace “ya isa haka Rajjj!”saurin juyowa suka yi dan ba su san da shigowar su Père ba sai jin murya shi da suka yi.
Takowa yayi har tsakiyar falon ya nuna Raj da yatsa yace “duk laifin ka ne da ace baka nuna ma Tajdeen tsana ba da matar ka ba tayi kuskuren taɓa lafiyar shi ba,amman ba komi duniya ce”Père ya faɗa yana mai wucewa part ɗin shi Rahul ya take mashi baya.
Kallon ido cikin ido Mom ta yi ma Avani ta goge ƴar ƙwallar da ta ciko idonta sannan ta wuce kitchen,tsaye tayi ta rasa mi ke mata daɗi ashe bugun Deen Avani tayi shine tayi mata ƙarya tace faɗowa yayi a zuci tace “kenan shine binda Deen ke son faɗa min?”……

 

****Maraɗi

Sai bayan sallah Zuhur malam Nur ya shigo gida, kyakyawar tarba ya samu gun amarya shi Nazifa.Bayan sun gama cin abinci ne suka fara ɗan taɓa hira da Samira wacce ta zo ta taya ƙawarta aiki,kallon malam Nur Nazifa tayi tace “ɗazu anty Sappa ta shigo nan”dariya yaƙe yayi ya na jin zuciyar shi na bugawa “toh Masha Allah mi ta kawo maki?” “hira mana dan ta jima nan kafin ta koma part ɗin ta” “to yayi kyau”shine abinda malam Nur ya faɗa “ya kamata ka tashi ka dubo ta tunda ka shigo baka leƙa ba”cewar Nazifa ta na mai komawa kusa da Samira ,ba tare da yace komi ba ya miƙe ya nufi part ɗin Sappa can ƙasar zuciyar shi kuma ya na jin daɗin visite ɗin da ta kai ma sahibar shi.

A zaune ya tarar da ita ta na kallo tana ganin shi ta miƙe tana mai mashi barka da zuwa,amsawa yayi yana mai tambayar ta journée ɗinta ta amsa mashi da alhamdullah.
Ruwa masu sanyi ta ba shi kafin tace “ko na zuba maka abinci ?yanzu anty Nazifa ta aiko min shi”cike da jin daɗin haka ya sakar mata murmushi yace “no na ƙoshi sai dai zuwa an jima”baki ta turo tace “da fah an yi sallah la’asar ƴan damu za su zo gidan zai cika da jama’a ina zan ganka balle na baka abinci” “toh sai ki aje har baƙin su tafi,yanzu dai miƙo min télé commande”miƙa mashi tayi ta zauna kusan ƙafafun shi tana kallon yadda ya ke recherche ɗin chaîne.

 

Zuwa bayan la’asar aka fara gudanar da Damu kamar yadda al’adar Maraɗi take a duk sadda aka kai amarya ga washegari ƴan uwa da abokan arziki sukan taru gidan amarya dangin ta su bayar da kyaututuka ga dangin ango.
Bayan an gama gudanar da bikin Damun,dangin Sappa suka rakota har ɗakin Nazifa suka damƙata amana tare da yi masu nasiha.
Malam Nur ma da ya zo haka ya tara su ya gindiya masu sharaɗan zama gidan shi tare da doguwar nasiha mai ratsa jiki.

Sai da malam Nur yayi sati guda cur a ɗakin Nazifa sannan ya koma ɓangaren Sappa ita ma yayi sati guda,daga nan suka yi rabon kwana biyu-biyu.
Tun daga lokacin bikin su babu abinda ya haɗa su na rashin jituwa, Sappa na bin Nazifa sau da ƙafa wannan ya sa ta ciri tuta gun malam Nur har ya faɗa cikin kogon sonta ba tare da ya sani ba.

 

Tun safiyar yau Nazifa ta tashi da wata irin kasala da zazzaɓi,tun tana daurewa har ta kasa hakan yasa ta nufi part ɗin Sappa.Ƙwanƙwasa ƙofa tayi amman ba’a amsa ba hakan yasa ta cigaba da bugawa da ɗan ƙarfi,jin an buɗe ƙofar yasa tayi saurin ɗago kanta Sappa ce sanye da riga kwana iya cinya.Hamma tayi ta kalli Nazifa ta yamutsa fuska tace “yaaa lafiya irin wannan dukan ƙofa?”
“Banda lafiya ne”Nazifa ta bata amsa kamar za tayi kuka “to sai aka yi yaya?ni na ɗora maki ciwon ne da zaki wani kwaso jiki ki zo gayamin?”da mugun mamaki Nazifa ke kallonta kafin tace “ki kira min shi ya kai ni asibiti”kallon baki da hankali Sappa ta watsa mata tace “barci ya ke kuma saboda wata banza ba zan tada mijina ba”gam ta rufe ƙofa ta bar Nazifa sake da baki.

Ganin tsayuwar ba tayi mata yasa ta koma ɗaki,kuɗi ta zuba a sac ta kulle ɗaki ta nufi bakin titi.Ba jimawa ta samu abun hawa Likita Agaji ta tafi bayan ta ga likita yayi mata tambayoyi,nan yayi ƴan rubuce-rubuce ya bata takarda ta sawo allurain da za’a yi mata ta dawo .
Allura ruwa ya saka mata dandanan barci ya ɗauke ta ,ko da ta farka sérum ɗin ta ci rabi.Text tayi ma Samira ba jimawa sai ga ta tazo, result ɗin likitan ya shigo ya bata tare da yi mata congratulations.
Cike da murna Samira ke karanta farar takardar da sakamakon ya nuna Nazifa na ɗauke da ciki na tsawon wata biyu…….

 

Please share

Jikar Rabo ce????
[26/07 à 11:26] Matar Sadauki????: *LE DESTIN…*????
(ƘADDARA)

Story
and
Writtenby
“`CHAMSIYA LAOUALI RABO“`✍????

*RUBUCIYAR*
ƁOYAYYEN SIRRI
MAHAUKACIN SO
ƘAWAR MOMYNA
SADAM

Dedicated to *Amana Writers Associations*????????

☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*☀️

____________________________________________________________

“`MA’ABOTAN SAURAREN LITATTAFAIN HAUSA ZAKU IYA SAURAREN DADAƊEN LITTATTAFAI TA WANNAN SHENEL ƊIN“`????????

*SUBSCRIBE*
_DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV_

https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ

Page 15-16

Cike da mamakin ganin ta kulle part ɗinta malam Nur ya ciro waya ya danna mata kira,bugu biyu aka ɗaga tare da yin sallama amsawa yayi yace “ina kuma kika tafi na ga ƙofar gidan ki a rufe?”
“Ina asibiti”ta bashi amsa “asibiti?shine ba ki kira ni na zo na kai ki ba ?shine kika fita ba da izini na ba saboda kin isa da kan ki ko mi?”a yadda ya ke maganai za ka gane cikin zafin rai ne ya ke yinta hakan yasa Nazifa ta sanyaya murya tace “babyn ka ne ya matsa min tun safe ni ke jin kasala ga kuma zazzaɓi shine na zo asibiti sai kuma aka tabbatar min da zaman shi”wata sanyayar ajiyar zuciya ya sauke a ɗan bayaninta ya gane so take tace mashi ta na ɗauke da ciki “to kuma Naziii shine ba zaki kira ni mu je tare ba?”murmushi tayi jin ya sauko daga dokin zuciya tace “dan kar na shiga haƙin ƴar uwata ne shiyasa,ya ne kun tashi lafiya ina amarya?”bai amsa gaisuwar ba sai tambayar ta asibitin da ta je yayi,tana gaya mashi ba’a fi 10mns ba sai gashi ya zo baki buɗe yana fara’a kamar gonar auduga.

Gaisawa da Samira yayi nan ta shiga zolayar shi kai kace ba malamin ta ba ne, fuskar Nazifa ya shafa ya na jin wani farin ciki na luluɓe shi.
“Mu ga cikin?”ya faɗa can ƙasan maƙo shi ta yadda ita kaɗai za taji,kallon shi tayi ta turo baki tare da yi mashi alama Samira fah na nan.Inda Samira ke zaune ya waiga sai ya ga hankalinta sam ba ya gare su waya take dannawa hakan yasa ya ɗan ɗaga rigar Nazifa ya shafi mararta yace “ya aka yi ban gan shi ba?”sake da baki Nazifa ta kalle shi tace “wai mi ba dai cikin ba?”gira ya ɗaga mata yace “eh mana”dariya ta shiga yi kafin ta tsagaita tace “juste 2month ne fah,kuma har kake tunanin ya fito?”
“To sai yaushe kenan?”kafin ta bashi amsa kira ya shigo wayar shi ɗagawa yayi bakin shi da sallama sai dai bai kai ƙarshenta ba ya yanke sakamakon jin kukan Maman.
Fita yayi waje yana mai tambayar lafiya “Alhaji ne ba lafiya sai suratai ya ke dan Allah ko mi kake ka tawo,ciwon na shi sai tsananta ya ke”Maman ta faɗa cikin kuka “innalillahi wa’inna ileyhi raji’un”shine kawai abinda malam ya faɗa ya kashe wayar .Komawa ciki yayi ya shaida ma Nazifa Baba ne a bai jin daɗin jikin shi ,nan yayi mata sallama tare da ba ta kuɗi in buƙatar hakan ta taso.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button