KADDARA Complete Hausa Novel

“Dan Allah Alhaji ka bar min maganar wasiya nan ai ciwo ba mutuwa ba ne,in ka mutu ka bar ni ina zan sa raina?”Maman ke faɗar haka tana kuka gefenta Balkis ce ita ma tana rera na ta.Sallama yayi basu amsa ba,cikin halin kaɗuwa ya nufi mahaifin nashi wanda ke kwance tsakiyar falo sai hawaye ta ke zubarwa.
Kan shi malam Nur ya tallabo ya ɗora saman cinyar shi yana goge hawayen da ke zuba kan fuskar mahaifin na shi,cikin rawar murya yace “Baba miye na kuka maimakon addu’a?kayi shiru ka bar zubar hawaye in shaa Allah za ka samu sauƙi yanzu nan zan kai ka asibiti”kai Baba ya girgiza yace “Nuradeen ciwo na ba na likita ba ne,abu guda ke damun raina tun shekaru ashirin da suka wuce shi ni ke ma kuka domin ban san mi zance ma ubangijina ba duk da dai ba yin kaina ba ne “cikin sigar rarrashi malam Nur yace “No Baba zafin ciwo ne ni na san babu wani abu da za ka aikata marar kyau da har Ubangij zai hukunta ka,ka bari kawai na kai ka asibiti”murmushin takaici Baba yayi yace “miyasa ba zaku fahimce ni ba?zuciyata ciwo take min saboda nauyin abinda ni ke ɓoyewa ku bar ni dan Allah na faɗa maku ko zan ji sanyi”
“Minene kake ɓoyewa Baba wanda har mu ba mu san shi?”
“Wata babba *ƘADDARA* ce da ta taɓa abkuwa gare ni, Allah ya jarabce ni da son yin mata biyu amman mahaifiyar ku ta hana duk lokacin da nayi yunƙurin ƙara aure sai ta rogaza shi abun takaici kuma ita ta kasa kula da ni kuma ta hana ni auro wadda za ta ɗebe min kewa.Da ƙarfi da yaji ta sa na lizimci yin azumi dan kauce ma hanyar ɓata da farko na samu sassauci sai kuma daga ƙarshe Rahanatu ta shigo rayuwata lokacin da na fara kasuwanci Kano-Kano ina saro kaya.Tun farko da aure ni ke sonta amman ganin hakan ba zai samu ba sai sheɗan ya buga min ganga nabi ruɗin shi ita ma da yake tana sona sai ta biye min wajen aikata kuskuren da har ƙarshen rayuwata ba zan daina nadama ba.Ɓullowar cikin Rahinatu shi ya fargar damu cewa saɓon Allah ne mu ke aikatawa mafi muni,kafin muyi tunanin zubar da cikin mahaifanta tuni sun san da zaman cikin kawai sai suka kira ni da zancen doli sai na auri Rahinatu ko kuma su maka ni kotu banda wani zaɓi na amince ta na haihuwa aka ɗaura mamu aure…”wata irin shaƙa Maman tayi ma Baba tana cewa “au mi?aure fa kace?ai gwara na kashe ka da na ida jin wannan mummunan labarin”dakyal malam Nur ya ƙwaci Baba nan ya shiga tari ya kuma ɗora da faɗin “ai duk laifin ki ne ko ma minene ke kika jawo Allah ya shaida ban aure ki ba sai dan ina son ki kuma ki haifa min ƴaƴa amma kika biye ma ra’ayin ki na yara uku kawai zaki haifa duk gudun kar ki tsufa,saɓanin Rahinatu da ta haifa min yara ɗaiɗaya har bakwai kuma duk maza”wani irin ihu Maman tayi jin abinda Baba ke faɗa,ririƙeta Balkis tayi yayinda malam Nur ya ciciɓi Baba ya nufi waje sakamakon jini da ya fara amayarwa .
CLINIC HAMDALLAH tafi kusa da gidan su hakan yasa ya nufi can,taimakon gaggawa suka shiga baiwa Baba cikin ikon Allah jinin ya bar zubowa.Oxygène aka maƙala mashi sannan suka fito da shi ɗakin hutu,cike da tausayin mahaifin na shi ya zauna gefen gado tare da kamo hannun shi ya jimƙe.Zantukan Baba ne suka shiga yi mashi kai komo cikin kwanya, tabbas dattin Zina ba zai taɓa gogewa ba ko da kuwa ka tuba akwai wannan tabon amman wani sa’in babu yadda mutum zai yi da zanen *ƘADDARA* doli sai haƙuri da roƙon Allah yafiya da kuma tsari.
Wasa-wasa sai da aka yi ma Baba ƙarin ruwa wajen sau bakwai a ranai,tun malam Nur na tsimayen farkawar shi har ya fidda rai.
Ya na dawowa daga sallah magrib ya tisa Baba gaba yana kallo,wata ƙwalla ce ta zubo mashi wadda ya kasa tantance ta mi cece,ta tausayin Baba?ko kuwa ta farin ciki ce jin ya nada wasu ƙannai bayan Balkis?.Motsi Baba ya fara yi da hannu gabanin ya buɗe ido,kusa da shi Nur ya matsa suna kallon juna.
Cikin murya ta maras lafiya Baba yace “ka yafe min Nuradeen mahaifin ku bai so ya kasance mazinaci ba,na bar maku mummunan tabon da zai rinƙa bibiyar zuri’a ku har ƙarshen duniya sai dai ka sani ba yin kaina ba ne wlh *ƘADDARA* ce Allah na gani tun ina ɗan saurayina ban yi ta ba sai bayan na mallaki hankalin kaina…”ƙyalewa Baba yayi tare da rumtse ido jin saukar hawayen malam Nur kan fuskar shi.
“Na sani Baba ni shaida ne a kan halayen ka,kullum ka kasance mai min gargaɗi daga sharrin Zina tun kafin na san mi kalmar take nufi har ya kai na santa.A kullum a ko da yaushe ina alfahari da kai a matsayin mahaifi ka bani tarbiyya ta gari duk da tarin dukiyar da kake da a kullum kana nusar da ni dogaro da Kai yafi zaman jiran,ka nuna min dukiya ba komi ba ce fa ce dauɗar duniya…”da sauri Baba ya lalubo hannun malam Nur yace “tabbas dukiya ba komi ba ce dan ba komi take saya ba,akwai kuma ranar da ba tada amfani ga mai ita ka ɗauki darasi a kaina milliards nawa ke a kwai cikin asusun bankina amman gani a kwance rai hannun Allah kuma na san ba za ta tsinana min komi ba nan da ɗan lokaci zan barta na koma ga mahallacina”kai malam Nur ya girgiza yace “no Baba ba za ka mutu ba ka bar ni kafi kowa sanin ina sonka fiye da komi, Please ka bar magana mutuwa na gaya maka zafin ciwo ne kuma in shaa Allah za ka samu lafiya”wani murmushi Baba yace “Allah bai barin wani dan wani yaji daɗi Nuradeen,ka riƙe ƴan uwan ka ka zamo masu jigo sannan kafin ku raba gado ina so ku baiwa Suleyman gida guda da wani kaso na kuɗi duk da ya na shege jinina,kace ma Maman ka ina sonta har kullum ta kula min da Balkis kar ka aurar da ita da mutumen banza,ina sonk….”tari ne yaci ƙarfin Baba yayinda na’urar da ke manne da bango ta fara ƙara tiii-tiii jan layi na fitowa,cikin azama malam Nur ya tallabo kan Baba yana mai maimata mashi kalmar shahada shi kuma ya na biyawa daidai nan likitoci suka shigo suka tsaya wuri guda suna kallon danjar da ta nuna jan layi alamu rai yayi halin shi.
Ido malam Nur ya shafe ma Baba yana mai jan dara zai luluɓe shi likitocin suka ƙaraso,gefe ya zauna yana kallon sarautar Allah shikenan Baba ya rasu “innalillahi wa’inna ileyhi raji’un”shine kawai abinda ya ke maimaitawa.
Wayar ɗaya daga cikin likitocin ya ara dan ta shi ta faɗi lokacin da ya ciciɓi Baba,malam Jabeer ya kira yana ɗagawa yace “ka zo ka same ni CLINIC HAMDALLAH Allah yayi ma Baba rasuwa”bai jira ta cewar shi ya kashe kiran.Ba’a ɗauki lokaci ba Malam Jabeer ya ƙaraso,ambulance aka saka gawa Baba aka kai shi babba asibiti ta Maradi,gidan sanyi aka shiga da shi aka laya shi kusa da gadajen matattu uwanda suka riga mu gidan gaskiya.
Malam Jabeer ke tuƙi yayinda malam Nur ke zaune kusa da shi ,ko gama parking bai yi ba mutane suka nufo motar dan duk illahirin unguwar ta ɗauka Alhaji Ali Ɗan Masani en même temps kuma Liman bai da lafiya.Jiki ba ƙwari malam Nur ya fito nan aka fara tambayar shi ya mai jiki “ciwo ya warke”shine kawai abinda ya faɗa nan wuri ya ɗauki kabbara.
Ya na shiga cikin gida ya ci karo da Maman wacce kabbara mutane ce yasa ta saurin fitowa,ba ta samu damar tambayar malam Nur ba ya wuce ta ko kallonta bai ba Malam Jabeer ne ya sanar da ita rasuwar Baba.
Tun cikin dare malam Nur ya shiga shaida ma ƴan uwa na nesa da na kusa rasuwar Baba,wasu tun lokacin suka ƙaraso ba’a ɗauki lokaci ba gidan ya cika da ƴan gaisuwa.
Miss call ɗin mutane ya shiga dubawa rabin su duk na Nazifa ne, text yayi ma Sappa ta zo gida ba jimawa kuwa ta zo nan ta tarar da tashin hankali,bai cikin nutsuwar shi hakan yasa malam Jabeer kai shi gida.
Kwance ya tarar da Nazifa tana kwana ledar magani kusa da ita,ɗaukar ta yayi ya maida bedroom sannan ya shiga wanka.Sallah isha’i ya gabatar sannan ya dawo falo ya fara karatun alƙur’ani,ya jima sosai yana karatun sannan ya koma jan casbi.Ranar nan yadda ya ga rana haka ya ga dare ko kaɗan kwana bai gigin zuwa wurin shi balle har ya sace shi,ya na nan har aka yi assalatu yayi alwala ya nufi masjid.Sai bayan ya dawo ya tada Nazifa tayi sallah,wanka yayi yace ta shirya za su fita.
A ƙofar gidan su ya sauke ta wanda aka share tass kamar ranar sallah, zuciyarta ce ta tsinke ta waigo ta kalle shi ido ya rumtse yace “fita ki shiga ciki”ba muso ta fita.