KADDARA Complete Hausa Novel

Malam Nur tare da wani ɗan uwan Baba su suka yi wankan gawa suka suturtata sannan suka yo gida da ita aka sallaceta sannan aka kai Baba gidan shi na gaskiya.Motoci na dawowa malam Nur ya fito ya dubi ɗumbin jama’ar da suka zana’izanci gawar Baba,sai a lokacin yaji wasu hawaye masu ɗumi kan kumcin shi.
Da sauri malam Jabeer ya riƙe shi ganin kamar zai faɗi,suna shirin shiga gida sai ga yaran Baba na Kano sun nufo malam Nur ashe tun da safe suka zo sam shi bai ma san da zuwan su bai jiya dai ya shaida masu rasuwa mahaifin su.
A tare suka shiga cikin gidan tun daga nesa Maman ta tsinkaye su, tabbas uwannan sune ƴaƴan Rahinatu dan kamar su ɗaya da Nuradeen.Yunƙurawa tayi za ta miƙe Ummu Sappa ta mayar da ita tana girgiza mata kai,kuka ne ya kubcewa Maman tana jin zuciyarta na suya.
Nuradeen kuwa shi da ƴan uwan shi suka shige ɗaki suna rarrashin juna,malam Jabeer na basu haƙuri tare yi masu wa’azin mamaci addu’a ya ke buƙata.
Sun daɗe haka kafin su ba kan su haƙuri da juriya su koma waje suna karɓar gaisuwa.
Ranar sarakar uku Inna ta samu tayi ma Maman gaisuwa da sauran jama’a kafin take komawa gida, Nazifa wuri guda ta samu ta takure dan bata san kowa ba saɓanin Sappa da ya ke gidan su.Duk lokacin da suka haɗa ido wani banzan kallo Sappa da ƴan uwanta ke jifarta da shi,ganin haka yasa Nazifa tafiyarta gida wanda hakan da tayi ya tunzura Maman tana ta zaginta a ƙarshe ma bayan mutane sun watse tayi mata gami malam Nur,cikin son kare matar ta shi yace “Maman kin san ba ta jin daɗin jikinta sakamakon juna biyun da take da”cikin masifa tace “gareta farau yin juna biyu?kawai ta rena mutane ne inda ubanta ne ya mutu ai da yanzu ka na can kana baƙar wahala da su”malam Nur dai bai ce komi ba ya ficewar shi.
40days Ago
Wani sabon gini aka ɗora cikin gidan malam Nur wanda bai wani ɗauki lokaci ba aka gama aka yi mashi penti,cikin rana guda aka kwashi ke kayan Maman aka maido su ciki.
Cike da murna dawowar Maman gidan su Sappa ta shiga ta gaishe da Maman nan suka fara taɓa hira ita da Balkis wacce rabinta duk ɓata Nazifa ne take gun su.Duk hirar da su ke Maman na jin su da sauri ta ɗago tace “miiii?gori fah?”cike da jin daɗi Sappa tace “wlh Maman gori tayi min tace wai ni juya ce ban iya komi ba sai dai na ci na kai salanga”ƙyaci Maman tayi tace “eh lalle kice yarinya ta girma ta isa yanka,yanzu har ta kalli tsabar idon ki tayi maki gori?”kai Sappa ta ɗaga tace “wlh Maman ba ki san ta rena mutane ba sai kin ga yadda take sa Ustaz aiki kamar Ɗan da ta haifa,jiya fah wankin kaya yayi mata”ƙirji Maman ta daka tace “ke mi wanki” jin sallamar malam Nur yasa Sappa ƙyalewa amsawa suka yi,ya shigo Nazifa na biye da shi a baya.Durƙusawa tayi tace “ina wuni Maman da fatan kun zo lafiya?”sheƙeƙe Maman ta kalleta tace “mun zo lafiya?balaguro nayi?Ni da gidan Ɗana kike min wani sanu da zowa?oh!nufin na zo zan takura maki ko baki so zuwa na ba”cikin girgiza kai Nazifa tace “a’a Maman ba haka ni ke nufi ba,dama gaishe ki ne na zo nayi”
“To na gode madallah a tashi a tafi”miƙewa Nazifa tayi tana kallon malam Nur wanda yayi sumen tsaye………
Please share
Jikar Rabo ce????
[27/07 à 13:59] Matar Sadauki????: *LE DESTIN…*????
(ƘADDARA)
Story
and
Writtenby
“`CHAMSIYA LAOUALI RABO“`✍????
*RUBUCIYAR*
ƁOYAYYEN SIRRI
MAHAUKACIN SO
ƘAWAR MOMYNA
SADAM
Dedicated to *Amana Writers Associations*????????
☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*☀️
____________________________________________________________
“`MA’ABOTAN SAURAREN LITATTAFAIN HAUSA ZAKU IYA SAURAREN DADAƊEN LITTATTAFAI TA WANNAN SHENEL ƊIN“`????????
*SUBSCRIBE*
_DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV_
https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ
????????????????????
Joyeux anniversaire ma grande sœur de valeur *REAL NANA AÏCHA* je te souhaite tout le bonheur du monde surtout le mariage,que cette année te soit une année de réussir et des succès????????
Page 17-18
Cikin rashin jin daɗin abinda Maman tayi ma Nazifa malam ya juya zai bin bayanta Maman ta shiga taɓa hannuwa tana sallami,tsayawa yayi ba tare da ya ƙara ko taku guda ba ne.”A’a je ka,tafi bi bayan ta sai ka tabbatar min kai mijin tace ne”cewar Maman dawowa yayi ya zauna,kallo guda yayi ma su Balkis suka miƙe suka bar wurin.Ƙafafun Maman ya dafa zuciyar shi na suya yace “kiyi haƙuri Maman sam hakan da kika yi bai dace ba,Naziii na bakin ƙoƙarin ta wajen kauce duk wata husuma na lura tun ranar sarakar uku ta Baba da kika ƙullice ta har yanzu baki sauko ba,a madadin ta ina mai baki haƙuri…”saurin katse shi Maman tayi da cewa “ni ce mai tada husumar ko?saboda matar ka kake gayamin magana har da cewa na ƙullace ta?” “A’a Maman ba haka ni ke nufi ba wlh,kawai abinda kika mata ne yanzu bai dace ba a matsayinta na surukar ki ni ina ganin da ni da ita ai duk ɗaya ne a gun ki”hannuwan shi Maman ta jaye daga kan ƙafarta tace “ka tashi ka tafi har jinin ka ya hau ka zage ni”da sauri Ustaz yace “subahanallahi zagi kuma Maman ?” “Eh mana tunda an taɓa ƴar gwal ba zagi na ba ai ko duka na sai kayi”.
Murya malam Nur ya ƙara sanyayawa yace “Allah ya huci zuciyar Ummu Nur, Allah ya baki haƙuri zan fita malam Jabeer na kirana kin san Yau za’a kai kuɗin auren shi”ya na gama ya miƙe tsaye Maman kuwa ta washe baki tana cewa “ah-ah Masha Allah ashe yarona an kusa zama manyan mutane?toh Allah sa dai ta kirki ce zai auro Allah kuma alkairi”da “Amen”ya amsa yayi ficewar shi.
Sai bayan ya sun dawo daga kan kuɗin malam Jabeer ne ya shiga gun Nazifa,waya ya tarar da ita suna yi ita da Samira.Kashe kiran tayi ta tarbi mijinta “har kun dawo?Masha Allah yau burin ƙawata ya cika malam Jabeer ya kai sadaki sai fatan kuma Allah ya nuna mana ranar biki”Nazifa ta faɗa murmushi kan fuskarta,shi ma murmushin yayi yace “shikenan sai mu huta da mita kullum sai yayi min hira ta sai kace gare su farau soyayya”dariya Nazi tayi tace “ai bai kai nacin ka ba ko ka manta lokacin da muna soyayya kullum ka na gidan mu kuma hirar ka ba ta wuce NazNur”tunda ta fara magana ya tsaya yana kallonta kamar yau ya fara ganinta,jin bai ce komi ba ta ɗan daki ƙirjin shi tace “ya dai?”numfashi ya sauke yace “ba komi kawai ina tunanin bbyna ne,ko da wa zai kama cikin Ni da Ke?”
Duban shi tayi tace “in namiji ne da kai zai yi kama in kuma mace ce da ni za tayi kama” “na fi son ki haifi namiji Saboda buri biyu,na farko da dan na saka mashi sunan Baba su na biyu da kuma dan na samu aboki”cikin rashin jin daɗin zaɓen da yayi na cewar yafi son namiji tace “ka bar ma Allah zaɓi dai shi ya fi,in kuma na haifi mace sai yaya kenan?”miƙewa yayi tsaye yace “in shaa Allah namiji ma ne,sai da safe ki zo ki rufe ƙofa”ya faɗa yana mai ficewa saboda yau Sappa ce da girki.
Kicin-kicin tayi da fuska kafin a shagwaɓe tace “yanzu sabida SapNur sai yanzu za ka shigowa bayan ka san yau ni ce da girki shine ka tafi can kayi zamannin ka?”sam malam Nur bai kulata ba sai ma dariyar sunan SapNur da yaji tace sai yaji sam bai yi daɗi ba.Cikin jin haushi Sappa ta biyo shi ɗaki sai aka yi rashin sa’a har ya shiga wanka har za ta tafi kuma komi ta tuna sai ta dawo ta zauna.Bai jima ba ya fito ɗaure ta towel, jallabiya ya saka yayi Sallah raka’a biyu sannan ya fara tilawar alƙur’ani mai girma.
Wani maƙoƙon baƙin ciki ne ya tokare ma Sappa maƙoshi,cikin jin haushi ta ɗaga murya ta yadda zai jita tace “malam alhuduhudu ai ka dakata da karatun kaji da lamuran matar ka,koko har yanzu ilimin na ka bai sanar da kai darajar mata a gun mijinta ba?”kamar zubar narkakar dalma haka malam Nur yaji maganar ta ,cak ya tsaya daga karan da ya ke ya waigo inda take zaune ta hakimce bakin bed tana kalkaɗa ƙafa.Ido ya rumtse ya cigaba da karatu ganin haka yasa Sappa yin tataki har inda ya ke ta tsaya mashi a kai tace “da kai fah nike”yadda tayi maganar tamkar uwar shi yasa ya harzuƙa ya miƙe ya kwaɗa mata mari tare da nunata da yatsa yace “ki shiga hankalin ki tun kafin ki sa na aikata abinda ba ya cikin tsarin rayuwata,wlh in kika cigaba da wannan shirmen zan maki ɗan banzan duka get out…”jiki na kyarma Sappa ta fita ba shiri,tana shiga ɗaki ta fashe da kuka tana cewa “na shiga uku ni Sappa wato duk yadda zan yi ma ka ban yi daidai ba nayi maka kissa da rangwaɗa ka wani share ni,na nuna maka fushina ka koro ni “taɓata taji an yi da sauri ta juyo suka haɗa ido,alama yayi mata da ta zo gare shi ba muso ta faɗa ƙirjin shi.Bayanta ya bubuga yace “toh ki yi shiru mana ba gani ba ko baki so na komawa ta ne?”kai ta girgiza yace “to naji ba zan tafi ba amman ya kamata ki san yadda za ki rinƙa yi ma miji magana sannan ki rage saurin fushi duk abinda lalami da rarrashi bai bayar ba to tashin hankali ba zai saka shi ba”ajiyar zuciya ta sauke tace “toh”kulawa ta musamman suka shiga baiwa junan su tamkar ba yanzu suka yi faɗa ba,hakan kuma yana ɗaya daga cikin jajircewar malam Nur na kwatanta adalci tsakanin matan shi ba tare da ya tauye haƙin ɗaya ba.