HAUSA NOVELKADDARA Complete Hausa Novel

KADDARA Complete Hausa Novel

 

***JOS

Sosai jikin Tajdeen yayi sauƙi kasancewar ya na samun kulawa ta musamman daga iyayen shi,tsakanin shi da Avani da Raj kuwa sai gaisuwa ita ma ba kullum ba .Duk da yanzu Avani ta rage jin haushin Tajdeen sakamakon cikin da likita ya tabbatar mata da shi,da sannu ta fara jawo Tajdeen jikinta abun ka da yaro sai ya manta cutarwa da tayi mashi ya ke zuwa gun ta sai dai da zarar Raj ya shigo ya ke fito saboda kallon tsanar da ya ke jifar shi da kuma faɗan da ya ke ma Avani dan mi take bari ya na shigowa.

Cikin Avani na shiga wata tara da ƴan kwani ta haifo kyakyawar ƴarta mace mai kama da turawa,tun a ranar da aka haife ta aka yi mata laƙabi *Mari* sai da aka ɗauki wata biyu sannan aka yi biki.
Tunda Mari ta zo duniya Tajdeen ya ɗauki son duniya ya ɗora mata,kullum ya na ɗauke da ita in kuma ya tafi makaranta bai da hira sai ta Mari dan wasu abokanan shi har zuwa su ke kawai dan su gan ta.

Zaune suke tsakiya falo ya sa Mari gaba sai wasa ya ke mata ita kuma tana wangale baki ta na mashi dariya,kuka ta fara alamun ta gaji yunwa take ji hakan yasa Tajdeen ɗaukar ta ya nufi part ɗin Avani da ita ya na ɗan ririgata.
“Mi kayi mata take kuka iyeee?”Raj ya tambaya kamar zai kashe Tajdeen,shiru yayi bai ce komi ba sai jikin shi da ya ɗau rawa dan har ga Allah tsoron Raj ya ke.Wani gigitacen mari Raj ya sauke ma Tajdeen wanda yayi sanadiyar ɗaukewar numfashin shi na wucen gadi,wata irin ƙara Tajdeen ya ƙwalla tare da sakin Mari bai shirya ba.A gudane ya nufo waje jini nayi mashi zuba ta hanci,karo suka ci da Mom wadda ƙarar Tajdeen ta caki ƙahon zuciyarta ta nufi part ɗin Avani.Jikinta ya faɗa ya na kuka,saurin ɗago shi tayi tana bubuga goshin shi dan tsayar da jinin amman abu ya cuttura.Ruwan sanyi Père ya ɗauko tare da wanke mashi fuskar shi nan jinin ya tsaya,Père na shirin shiga part ɗin Avani dan zaƙulo Raj sai Dad ya riƙe shi ya girgiza mashi kai “Père ba komi ba ne ake ɗaukarwa mataki,Deen tamkar Ɗa ya ke gun Raj ya na da incin hukunta shi ƙila laifi yayi mashi”ya na faɗin haka ne tare da jawo hannun Père zuwa kujerar zaman shi.Cike da jin haushi Mom ta harari Dad murmushi kawai yayi mata,lamo Tajdeen yayi yana shasheka kafin daga bisani barci ya ɗauke shi.

 

Washe gari bayan Dad ya sauke Tajdeen school sai ga shi da wasu takardu ya na yi ma Père bayani,huci Père ya sauke yace “ban ƙi ta taka ba Jean amman ka na ganin shi Deen ya na son aikin soja?kuma mi zai hana ka bari har sai ya girma?”kai Dad ya girgiza yace “a’a Père gwara ya tafi tun yanzu dan zai fi samun horo mai kyau kuma hankalin shi da namu zai fi kwanciya”
“To Allah ya taimaka ita Vani ɗin ta yarda?” “Ban kai ga gaya mata ba sai yanzu “.

Sosai Mom tayi murna da maganar da Dad ya zo mata na tafi Deen école ɗin soja,hakan ya sa Tajdeen na zuwa ta shaida mashi nan ya hau kuka yace shi aikin likita ya ke so cikin rarrashi Mom tace “Ɗana Deen aikin soja da na likita duk ɗaya”cikin kuka yace “a’a Mom nayi ma…nayi alƙawari”sai kuma ya ƙyale ya na jin kan shi na sara mashi sakamakon wani abu da ya so ya tuno kuma ya kasa.Zuciyar Mom kuwa lugude ta shiga yi dan ita har ga Allah ba ta son ya na yi mata zancen Anya kuma babu shakka ta tabbata abinda ya ke son faɗa kenan,ɗaki ta kai shi ta ɓalli maganin shi ta ba shi dandanan barci ya ɗauke shi.
Da ya farka da maganar zuwan shi aikin soja ya tashi,cike da murna Mom ta rinƙa kwaɗaita mashi aikin.
Farin cikin da ya ga ta na yi shi ya zame mashi ƙwarin gwiwa,hakan ya sa ya ɗaura ɗamarar kasancewa kamar yadda su ke so.

Abu kamar wasa sai ga Tajdeen luntsum cikin makarantar yara ta sojoji wacce ke babbar jaha ta Abuja,sosai kasancewar shi a nan tayi mashi daɗi duk da baƙar azabar da ke gana masu amman samun abokan ƙwarai ya sa shi jin daɗin rayuwar,gefe guda kuma ya na jin kewar gida da soyayyar ƴar ƙaunar shi.
Kwance Tajdeen yayi bayan ya fito daga wanka,lumshe ido yayi gidan su nayi mashi gizo bai ɗau wani lokaci ba barci ya ɗauke shi mai cike da mafarka iri-iri,duk cikin su guda ne ya tsaya mashi ba wani mafarki ba ne yayi fa ce na yanzu girma ya zo mashi alƙalami ya hau kan shi.Kasancewar shi yaro shiyasa bai gane komi ba dan a lokacin shekarar sha biyu da wasu watanni za’a iya cewa yanzu cikin 13years ne ya,wani wankan ya sake yi ba wai na yadda addini ya sharanɗa ba a’a sai dan kawai wanke ƙazamtar jikin shi.Cikin wani irin yanayi na shiga sabon zangon rayuwa ya shirya tsaf ya nufi terrain ɗin ake buga wasa,tun kafin ya ƙaraso Irfan da Faruk suka yi mashi signe.
Hannu ya basu suka gaisa sannan ya zauna suka cigaba da kallo,Irfan ne ya kalle shi yace “Deen sai na ga kamar yau ba ka cikin walwala why?”murmushi kawai yayi yace “ba komi”ba dan Irfan ya yarda ba ya ƙyale shi dan sam ba haka ya san Tajdeen ba.
Har aka gama ƙwallon Tajdeen bai ce ufan ba Irfan da Faruk kawai ke hira,tun su na tambayar shi lafiya har su ka ƙyale dan sun lura Deen irin mutanen nan ne masu zurfin ciki.

 

Ko da dare yayi bayan sun gama cin farar Macaroni da mai da maggi wata hira suka ɗora inda Tajdeen ya haye ɗan ƙaramin gadon shi ya faɗa tunanin yarinyar da ya gani cikin mafarki jefi-jefi kuma ya na sauraron hira abokan na shi.

Yayi nisa a cikin tunani yaji Faruk na cewa “Ni kam Tajdeen na tambaye ka”ba tare da ya juyo ba yace “um ina jin ka”
“Miyasa ba ka sallah ne kullum sai na ga kayi wanka ka shafa mai?”ita ce tambayar da Faruk ya jefo ma shi,shiru yayi ya fara tunanin ina ya taɓa jin kalmar sallah da dai yaji zai jawo ma kan shi ciwon kai sai cewa yayi “minene sallah?”waro ido su kayi a tare suka ce “minene ya sallah kuma?”a yadda yaji sun yi maganar cike da mamaki ya sa shi juyowa yace “eh mana ni ban san mi kuke zan ce ba”kallon-kallon suka fara yi kafin Irfan yace “ka na nufin kai ba Musulmi ne ba?”saƙe Tajdeen yayi zuwa can ya girgiza kai yace “Ni ban san komi Please telle me mi kuke son faɗa ne ?sai naji kamar na taɓa sanin wannan kalmar”cikin ɗan ilimin da su ke da suka shiga yi ma Tajdeen bayani akan addinin Musulunci har sai da dare ya tsala sannan suka dakata tare da yi mashi alƙawarin gobe sun ƙarasa mashi…

 

****Maradi

Rayuwar farin ciki Nazifa ke fuskanta gun mijinta inda kuma ɓangaren guda ta ke fama da irin cin kashin da Maman ke yi mata,ƙiri-ƙiri Maman ke nuna banbanci tsakanin ta da Sappa musamman yanzu da ita ma Sappai ke ɗauke da ciki sai tayi ta ƙulla mata sharri iri-iri ita kuma Maman ba bincike ta hau Nazifa da faɗa tun malam Nur na tare mata har ya kai ya zuba ma sarautar Allah ido.

Yanzu abinda ya fi damun Nazifa shine wata sabuwar dokar da Maman ta kafa,in Nazifa za ta girki doli sai abinda Maman ta zaɓa haka kuma in za ta tafi gari doli sai da izinin ta ko da kuwa malam Nur ya yarje mata.

Duk wannan bai ishi Maman ba sai da ta ƙara mata da wata dokar na banda yawan baƙi a cewar ta suna zowa ne dan su zuga Nazifa,hatta da Rakiya ƙauna Nazifa in ta zo Maman ta fara habaici kenan.A na haka har cikin Nazifa ya shiga watan haihuwa wanda yayi daidai da bikin malam Jabeer da Samira.

Tun satin bikin Nazifa ta fara sallah dare tana roƙon Allah ya sa Maman ta barta taje bikin sai dai kash tana fitowa Maman tace “ina zaki Nazifa kika wani ci uban shiri ko haihuwa ce?”cikin faɗuwar gaba tace “Maman wajen bikin matar malam Jabeer kin san yau ne”baki Maman ta ja tace “eh lalle shine kike sauri zaki fice kafin na gan ki ko?”
“A’a Maman niyyata sai na shigo na shaida maki kafin na tafi”Nazifa ta faɗa muryata na rawa idonta na cikowa da ƙwalla “to ba zaki je ba,in kuma kin fita wlh akan auren ki”Maman na gama faɗa ta shige ɗaki ta bar Nazifa tsaye……

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button