HAUSA NOVELKADDARA Complete Hausa Novel

KADDARA Complete Hausa Novel

Su na nan zaune malam Nur ya fito daga ƙurya ɗakin “ungo wannan ko buƙatar wani abu ta taso “malam Nur ya faɗa yana miƙa ma Nazifa kuɗi karɓa tayi ta na kallon shi sai ya kuma cewa “eh gobe zaki koma gida shan kunu kamar yadda kuka buƙata,ban san lokacin da za ku tafi ba ƙila ina kwana sai ku shiga taxi”ya na gama faɗin haka ya fice.

Wani abu ne ya caki zuciyarta sam ta kasa yarda wannan malam Nur ɗin ta ne,tunda ta haihu komi na shi ya canza.Jiki baƙwari ta miƙe ta nufi bedroom shimfiɗar da Laila tayi ta koma can ƙarshen gado tayi tagumi ta na tunanin rayuwa,ganin tunanin ba zai ɓarkata mata komi ba yasa ta miƙe ta ɗauro alwala ta fara jan tabzi.

 

Washegari misalin ƙarfe goma na safiya Inna Lami ta taro mai taxi,kayan da za ta buƙata ne kawai za ta tafiya da su.Sallama su kayi ma Maman sannan suka wuce gidan Inna,yaya Ɗalhat ne ya shigar masu da kayan ya kuma sallami mai taxi.
Cike da begen jikanyarta ta Inna ta rungume ta dan rabonta da ita tun a asibiti,sosai yarinya ta ƙara yi mata kyau.
Yaya Ɗalhat ne ya matso yace “Inna kin kama ɗiya kin riƙe ba ki da niyya ba iyayenta”dariya tayi tace “mi ake da kishiya,ɗiyar taku ma da ba wani kyau ne da ita ba sai dogon hanci kamar bic”dariya shi ma Ɗalhat yayi ya karɓe ta ya manna a ƙirji ya na jin son babyn,bisanin ya miƙa ma Rakiya wacce ke zumɓuro baki tayi gajen haƙurin a bata.

Nazifa kuwa babu abinda ya dameta sai ɗumamen tuwon masara ta ke ciki ta na kallon diramar su.Sai yamma lisss Inna Lami ta tafi gidanta bayan ta karɓi sha tara ta arzikin da Bazifa tayi mata.

 

Sosai Bazifa da ƴarta su ke samun kulawa wajen Inna da ya Ɗalhat da kuma Rakiya,dan kowa na iya ƙoƙarin shi wajen kyautata mata wannan ya sa damuwar Nazifa ta kawar duk da shi ma malam Nur ɗin na zowa ganinta ku san kullum sai dai bai ɗaukar Laila,da ya ga Nazifa na damuwa da hakan ne ya ke shafa kanta duk in ya zo wani sa’in kuma yayi kissing nata a go shi ya ɗauki hoton ta.

 

A kwana a tashi asarar mai rai,Nazifa tayi arba’in har ta koma ɗakinta inda rainon Laila kwankwacakwam ya koma hannun Maman da Balkis,kullum tana part ɗin Maman sai dare kawai ake maido ta ko kuma in tayi kuka.
Wannan abu shi yayi ma Sappa kaluluwa a zuciya ji take kamar ta jawo watan haihuwar ta kusa ta haihu ko nan ta rage haushi da tunanin kuma Maman za ta so ɗanta fiye da na Nazifa.

 

Zaune take a falo Balkis na matsa mata ƙafafunta da suka kumbura,gefe kuma Maman ce ke ta faman koyawa Laila zama ta sakata tsakiyar ƙafafunta.
Lokaci zuwa lokaci Sappa ke kallon su “Allah sa ta faɗi ta washe baki da goshi”shine abinda kawai take rayawa a zuciya.
Kamar daga sama kuwa sai jin kukan Laila tayi ta faɗi ɗin kamar yadda ta so,da sauri ma ta cirota ta shiga ririgata amman taƙi yin shiru hakan yasa Maman tashi tsaye ta goyeta a baya ta shiga kewayen ɗaki.
Takaici,baƙin ciki da hassada su ne suka turnuƙe Sappa barin tausar Balkis tayi ta nufi Maman tana yi ma Laila wasa daga goyen tsit ta ƙyale tana sauraren ɗan kacau-kacau da Balkis ke kaɗawa,tsabar baƙin ciki yasa Sappa sarƙewa da yawun bakinta ta shiga tari????.

Harararta Maman tayi tace “lafiyar kuwa?minene kike ci wanda ya ƙware ki?”ƙyafƙyaf da ido Sappa tayi ta turo baki cikin jin haushi,baki Maman ta taɓe tace “ki shiga hankalin ki Sappa ba ruwana da sarkarci dan na ga har yanzu kin ƙi ki sauwa daga mugun halin ki,jikanyar tawa ma banda iko na kula kawai dan ki na kishi da uwarta?”cikin jin haushi Sappa tace “toh wai ni mi nayi?ni ai ban faɗi haka ba” “to minene ya sarƙe ki?in ba kin ji zafin hakan ba?ko ko kece ɗin a ban sani ba mai yin tarin baƙin ciki in kin ji haushin abu?”shiru Sappa tayi dan sarai ta san da Maman tayi mata farin sanin da ko uwar da ta haife ta albarka.

Ana cikin haka sai jin sallama su kayi,malam Nur da ƴan uwan shi maza bakwai sai mace datizuwa wanda ke nuni ƴaƴan ta ne.Kicin-kicin Maman tayi da fuska kamar ta ga mala’ikan mutuwa,gaisheta suka yi ta amsa da “lafiya”gabatar da su malam Nur kafin daga bisani ya ƙara da cewa “wannan ce mahaifiyar su kuma ba komi ne ya kawo su ba sai rabon gado”daram ƙirjin Maman ya buga sai ido da ta fiddo tana kallon samarin bakwai wanda su ke a jere ras gabanin ta kalli Nuradeen da Balkis ƴaƴanta biyu rak…..

 

*Ba ku comments amman ku na ƙorafi,bai komi duk wanda ya gyara ya sani ranar da canza niyya na mayar da book ɗina na kuɗi ba wanda zan saurara,ko sallah da ake yinta ai dan lada ne*

 

Please share

 

Jikar Rabo ce????
[29/07 à 16:03] Matar Sadauki????: *LE DESTIN…*????
(ƘADDARA)

Story
and
Writtenby
“`CHAMSIYA LAOUALI RABO“`✍????

*RUBUCIYAR*
ƁOYAYYEN SIRRI
MAHAUKACIN SO
ƘAWAR MOMYNA
SADAM

Dedicated to *Amana Writers Associations*????????

☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*☀️

____________________________________________________________

“`MA’ABOTAN SAURAREN LITATTAFAIN HAUSA ZAKU IYA SAURAREN DADAƊEN LITTATTAFAI TA WANNAN SHENEL ƊIN“`????????

*SUBSCRIBE*
_DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV_

https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ

Page 21-22

 

Cikin dauriya Maman tace “to sai a kayi yaya in za’a yi rabon gado?”kallonta duk su kayi banda Rahinatu da sunne kai dan ita har ga Allah tsoron Maman ta ke.Ganin duk sun ƙyale Maman ta cigaba da cewa “in rabon gado za’a yi ai malumai ke yin shi ba wai tsakankanin magada ba,in banda masifa da zanzana irin ta tallaka duka-duka yaushe ne alhajin ya rasu da har za’a yi maganar rabon gado sai kace masu jiran mutuwar”cikin jin haushin wulaƙancin da ake yi masu Suleyman ya miƙe tsaye yace “ku tashi mu tafi tunda da alama wannan matar ba ta san arziki ba,kawai daga zuwan za ta wani rufe mu da masifa”baki buɗe Maman ke kallon kamin tace “ka ga masifa nan kusa da kai,uwar ka ita ce masifafa shege ɗan Zina kai miye na ka cikin rabon gadon?in banda sa kai uku”duk miƙewa su kayi suka fice Rahinatu na matsar ƙwalla.
Kusa da Maman malam Nur ya matsa yace “haba Maman miye haka? ƴaƴan mijin ki fah ƴaƴan ki ne minene na tozarta su?”
“To Baba dake ni.Nace ka dake ni na taɓa ƙannan uwar ka”cewar Maman tana juya mashi baya,cike da mamaki malam ke kallonta dan abun Maman ya fara barin bashi mamaki sai dai tsoro.
“Allah ba ki haƙuri”ya faɗa ya na mai zaunawa ya fara kallon tv.

Maman kuwa ɗaki ta shige ta fara zagaye tana neman mafita dan tabbas Rahinatu sai tafi ta samun kuɗi ita da ke da yara 6 kuma maza,yatsa ta cije tace “miyasa ma na biyewa ruɗin zuciya nayi ta shan magani dan kar na haihu mtsw…”haka dai tayi ta saƙa da warwara har sai da kanta ya fara ciwo sannan ta kishingiɗa tayi barci.

Washegari sai ga su Suleyman sun sake dawowa da maganar dai ta rabon gado,malam Nur shi kan shi sun bashi haushi hakan yasa ya nemo malamai masu ilimi kamar yadda Shari’a ta zartar haka aka raba masu gado bayan an cika wasiya Baba an fidda ma Suleyman kaso daga ciki.
Wannan rabon gadon sosai ya ɓata ran Maman ganin Rahinatu da ƴaƴanta sun ɗauki wajen kaso 85 cikin ɗari na dukiyar Alhaji ,tun tana masifa tana cewa an cuce su har ta kai ta kasa dangana ta fashe da kuka.
Sai da tayi mai isarta sannan ta ƙyale,malam Nur da Balkis Maman suka ba duka kuɗin dan tun ba yau ba ta shaida masu kasuwanci za ta fara.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button