KADDARA Complete Hausa Novel

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya yau ƙunci gobe daɗi,Maman an fara kasuwanci sayar da kaya na Lome da kanta take zuwa dan sam ba ta da yarda.
Duk in ta tafi sai tayo ma jikokinta sayayya Laila da ƴan biyun Sappa wanda malam Nur ya ɗauki son duniya ya ɗora masu .
“Maman wannan ai sun yi ma Amar da Anas yawa sai dai ko Laila tunda ita ta nada ƙiba”cewar Balkis wacce ke zaune tana duba kayan da Maman ta sawo,warce kayan Sappa tayi tace “ina Makauniya ina wannan kayan?ai na masu ido ne”da sauri Nazifa ta ɗago tana kallonta,murguɗa baki Sappa tayi tace “eh ko ƙarya ce ba Makauniyar ba ce kike wani kallona kamar wacce tayi maki ƙage”wasu hawaye ne suka zubo ma Nazifa a zuci take cewa “kenan dagaske Makauniya ce?zargina ya tabbata”kallon Maman Nazifa tayi wadda ita ma ƙwalla ta cika ma ido “kiyi haƙuri Nazifa ni nace kar a sanar da ke”cewar Maman tana kwashe kayan da aka baje a capet.
“Maman kenan ke kin san da haka?”Nazifa ta sake tambaya “eh kowa ma ya sani daga ke sai Sappa ne a baku sani ba,ita saboda irin wannan ranar yasa na hana a shaida mata ke kuma saboda kar ki tada hankalin ki”.
Ɗaukar Laila tayi ta fita direct part ɗinta ta wuce,hawayen idonta ta goge sannan ta ƙura ma Laila ido wacce yanzu take wata na biyar da haihu.Da ɗan yatsar ta tayi kamar za ta tsone idon Laila dan tabbatarwa amman ba ta ƙyafta ba, rungume ɗiyarta tayi a ƙirji ta saki wani marayan kuka na tausayin kansu su biyun.
A fili ta furta “wannan dalilin ne Abban ki a bai son ki,shin kyautar Ubangijin ce yayi fatali da ita har ya ke ƙyanƙyamin ta?miye laifin ki a ciki dan kin fito Makauniya alhalin ba ke kika yi kan ki ba?shi malami bai yarda da *ƘADDARA* ba to ina ga jahili wanda bai san Allah ba?”ba ta san da shigowar shi ba sai ji tayi ya daka mata tsawa yace “ya isa haka!ni namiji ni ke so shine kika tashi ki haifo min mace,macen ma Makauniya.Da wane kike so in ji rashin cikar burina koko ɗawainiya da ita?ita kanta mace rauni ce to yaya kike gani in ta kasance da naƙasa?”wasu hawayen baƙin ciki Nazifa ta goge tace “ai Naƙasa ba kasawa ba ce nufi ne na Allah,kai da kuma ba ka da ita babu tabbacin haka za ka zauna har ƙarshen rayuwar ka domin ba’a gama hallitar ɗan Adam ba har sai ya koma ga mahall….”wani gigitacen mari ya ɗauketa da shi tare da nuna mata yatsa yace “zo ki naƙasa ni ƴar baƙin ciki, Makauniya dai ce ki riƙe abar ki”ya na gama faɗa ya juya zai fita a fusace har ya kai bakin ƙofa yaji tace “ai ba ita tayi kanta ba”bai saurareta ba dai yayi gaba.
Cigaba tayi da kuka tana yi ta na fyace majina,Laila kuwa sai wasa take da ƴan hannun mahaifiyarta da suke ƙara.Aje ta Nazifa tayi ta shiga wanka,ta na fitowa ta saɓa ƴarta a baya ta goyeta.Hijab da sac ta ɗauka ta rufe ɗaki tana shirin fita taji Maman na ƙwala mata kira ta window,kewayawa tayi cikin ɗakin tayi tsaye ta sunkuyar da kai ganin Maman nayi mata kallon mai saman ruwa.
“In dai kin san yaji ne zaki yi to ki kwance min jika dan ba da ita kika zo ba,ki barta a gidan su kafin ki tafi na ku gidan.Gare ta farau makanta da har zaki ɗaga hankali in ke ma baki sonta sai ki bani na raineta,tunda ku Allah ya baku kun ce baku son kyautar wasu na can suna neman ko kuturwa ce Allah ya ba su”Maman ta faɗa da alamun faɗa-faɗa ,kukan da ta ke riƙewa ne ya kubce mata tace “Ni Maman ina son ƴata a yadda ta ke shi ne…shi ne dai a bai so “taɓe baki Maman tayi tace “to sai mi?ni ban ga abun damuwa ba tunda mu muna son abar mu,kin ga miƙo min ita tafi ki ɗora girki ki ci ki ƙoshi in kika biye ma namiji takaici ne zai kashe ki”kwance goyon Nazifa tayi ta miƙawa Maman ,baiwar Allah Laila sai barcin ta take.
Ɗaki Nazifa ta koma tana jin zuciyarta ta rage nauyi, zantukan Maman ne kawai tayi zaune ta na tuna ta na ɗan jin sauƙi.Tun daga wannan lokaci Nazifa da ƴarta ke fuskantar tsangwama gun malam Nur da Sappa yayinda Maman ta ke ƙarƙafa ma Nazifa gwiwa,tun lamarin na damunta har abun ya zame mata sabo.
Cikin shirin fita ta fito tana jaye da hannun Laila wacce yanzu ta ɗan girma tana cikin shekara ta biyar.Da shigar su part ɗin Maman Amar da Anas suka shiga yi ma Laila dariya su na tsokanar ta”ƴar makauniya…”cikin jin haushi Laila ta ƙwace hannunta daga na Nazifa ta nufi inda ta ke jin maganar su tana lalube,dariya suka sake yi tare da cigaba da tsokanar ta suna guje-guje ita kuma tana bin duk inda taji motsin su.
“Miyasa baki jin magana ne Laila ba na ce ki bar kula su ba?”cewar Nazifa ta na kamo hannunta,hawaye na kawowa idonta tace “Ammy baki ji su ke tsokana ta ba?”kai Nazifa ta girgiza tace “to ai ƙannan ki ne sai kiyi haƙuri,tawo mu tafi Maman na bedroom”tsuki Sappa tayi wacce tun ɗazu ta ke zaune ƙasa da uban cikin ta ƙatoto haihuwa ko yau ko gobe tace “Allah kiyaye mu irin mu babu masakai can ku ƙarata ke da makauniyar ki,Twins ku zo nan kar ku taɓa wacen abar ta liƙa maku nakasa”murmushin da yayi kuka ciwo Nazifa tayi kamin ta wuce ɗakin Maman,ba’a jima ba sai ga su sun fito Maman nayi mata a dawo lafiya.A zaune ta tsinkayi malam Nur ya ɗora Twins a cinya ya na raba masu biscuit,har za su wuce Laila taji murya shi da sauri ta waiga tana ƙyafƙyaf da ido kamar mai gani tace “Abih…”ɗagowa malam Nur yayi kallo guda yayi masu ya maida hankalin shi gun Twins da suke mashi surutu ya na amsa masu.
Zuciya na yi mata zafi ta nufi bakin hanya ta samu abun hawa ya kaita gidan Samira wacce ake bikin haihuwar da ta yi ta biyu,abun biki kawai ta bada ta samu wuri ta rakuɓe.Shikenan yanzu ita da farin ciki sai dai ta gani gun wasu?haka dama maza su ke ba su da tabbas?miye laifin ta dan ta haifi makauniya? wannan ne tambayoyin da Nazifa tayi ta yi har bikin ya watse ta dawo gida.
Cikin dare Sappa ta kasa kwana saboda naƙudar da ta tawo mata gadan-gadan,cikin tashin hankali malam Nur ya fito ya shiga ƙwanƙwasa ma Maman ƙofa kasancewar ba ta da nauyin kwana yasa taji bugun.
Ta na buɗewa ya shaida mata Sappa ce ke naƙuda da sauri ta koma ɗaki ta kimtsa suka nufi asibiti,Twins kuma aka bar su wajen Balkis.
Gari na wayewa Nazifa ta je gaishe da Maman Balkis ke gaya mata Sappa na asibiti wajen haihuwa “Allah sauke ta lafiya”ta faɗa tare da koma ciki ta fara girkin da za’a ta kai.
Ta na gama girki su ka shirya ita da Balkis da yara suka nufi asibiti,tun daga nesa su ke jin kukan Sappa sun tsaya tunanin room ɗin da take sai ga malam Nur ya fito fuskar shi a kumbure idon shi sun yi ja alamun kuka ya yi.Ba su tsaya tambayar shi mi ke faruwa ba suka shiga ɗakin da ya fito,kwance suka tarar da Sappa sai fizge-fizge ta ke yayinda likitoci ke ƙoƙarin yi mata allura barci.
“Maman lafiya ko jaririn ne ya zo ba rai?”cewar Balkis,kai Maman ta girgiza tayi masu nuni da ɗan ƙaramin gadon da aka shimfiɗe bbyn tace “a’a da ranta kawai dai mal formation ne aka haife ta da shi”da sauri Balkis ta zaro ido tana ƙarasawa bakin gadon,wata kyakyawar baby girl tayi tozali da ita mai hannu guda ɗayan kuma gundululu ne.
Tausayinta ne ya ratsa zuciyar imani ta Balkis hannu na rawa ta ɗauke ta,ɗaya daga cikin nurs ɗin tace wane suna za’a sa ga takardar babyn ” *Jasmine* “Balkis ta faɗa a takaice tana miƙawa Nazifa bbyn…………