KADDARA Complete Hausa Novel

Please share
Jikar Rabo ce????
[30/07 à 11:03] Matar Sadauki????: *LE DESTIN…*????
(ƘADDARA)
Story
and
Writtenby
“`CHAMSIYA LAOUALI RABO“`✍????
*RUBUCIYAR*
ƁOYAYYEN SIRRI
MAHAUKACIN SO
ƘAWAR MOMYNA
SADAM
Dedicated to *Amana Writers Associations*????????
☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*☀️
____________________________________________________________
“`MA’ABOTAN SAURAREN LITATTAFAIN HAUSA ZAKU IYA SAURAREN DADAƊEN LITTATTAFAI TA WANNAN SHENEL ƊIN“`????????
*SUBSCRIBE*
_DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV_
https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ
Page 23-24
“Zan ci mutumcin ki wlh in ba ki karɓi yarinyar nan ba kika bata abincinta,uwar mi za kiyi da shi in ba ki shayar da ita ba?”Mama Sappa ke faɗin haka tana mai miƙa mata babyn.Kai ta girgiza cikin kuka tace “wlh Umma tsoronta ni ke,ban iya ganin ta”
“To kin dai ji da kunnen ki tun ɗazu yarinyar nan ke kuka ta bata nono ta ƙiya sai zam-zam kawai ni ke ɗura mata”cewar Maman ta na hararen Sappa wadda tayi zaune kan gadon asibiti tana rusar kuka.
Bisa cinyoyinta Umma ta aza mata Jasmine da ke ta kuka,rumtse ido Sappa tayi ganin hannu guda kawai ya fito ta rigai gudan kuma sai shatin shi kawai ake gani.Karrr ƙafafunta suka fara zanzana yayinda hawayen fuskarta suka ƙaru,wani wawan dundu Umma ta kai mata a baya tace “in dai baki shayar da ita ba Allah ya isa nono na da kika sha ban yafe ba”jin furucin mahaifiyarta ta yasa doli ta fara baiwa Jasmine abincinta.
Ƙofa aka ture tare da yin sallama,Nazifa ce hannunta ɗauke da basket ɗin abinci.Gaishe da su Maman tayi tare da tambaya Sappa ya jikinta amman ko kanzil ba ta ce mata ba,Maman tace “ina kika baro ita Laila ɗin?” “Ta na can gida wajen Balkis tana koya mata karatu” “ah to yayi ai gwara ita Balkis ɗin ta koya mata tunda shi uban ya kasa kaita makarantai” murmushi kawai Nazifa tayi tana kallon bby Jasmine da ke shan nono har yanzu kafin zuwa can ta saki alamun ta ƙoshi hakan yasa Sappa maida rigarta tana turo baki.Tashi Nazifa tayi ta ɗauko ta murmushi kan fuskarta,gefen ƙyale ta sa ta goge mata baki.
Hararenta Sappa tayi tace “munafuka wa ya sani ma ke kika yi min asiri na haifi wannan masak…”da sauri Umma ta buge mata baki tace “in na sake jin kin aibatan yarinyar nan sai nayi mugun saɓa maki, banza daƙiƙiya da ba ta san abinda ta ke”mahaifiyar Sappai ke faɗin haka,ita dai Nazifa har ga Allah ta ke jin son Jasmine.
Abinci Maman ta zuba plate biyu ta miƙa ma Sappa guda su suka ci ɗayan,ba jimawa likita ya shigo ya basu takarda sallama.
Kaya suka fidda kafin Nazifa ta fita bakin ƙofa ta kirawo ɗan taxi,shi ya taimaka masu wajen sa kayan tare da faɗa masu kuɗin da za su biya.
Har ƙofar gida aka sauke su,da gudu Twins suka tawo gun Sappa tare da kama mata ƙafafu.Hannun su ta ja zuwa ciki,direct part ɗinta ta wuce alhalin part ɗin Maman aka ce za ta tsaya.
Cikin jimami Maman tace “ya kamata fa mu samu mafita kar jaririyar nan ta mutu,a bada kuɗi kawo a sawo madarar gwangwani a riƙa bata ki na ga fah tun zuwan mu ta kama ƙofa ta rufe alamun ta bar ma mu da ƴar”cikin takaici Umma ta kalli Maman tace “yanzu sabida Allah anty jaririya uwarta da ranta da lafiyarta sai a shiga bata madara?”Maman tayi saurin cewa “eh mana in dai ba taimaka mata za muyi wajen kisan kai ba,wlh na fi ki sanin halin Sappa ke haihuwar ta kawai kika yi tunda kika ji tace ba za ta shayar ɗin ba to haka maganar ta ke ba canji.Balkis tashi ki tafi pharmacie ki sawo min madara “Maman ta faɗa ta na zuge zip ɗin bag ɗinta ta baiwa Balkis 5000f.
Ruwan zafi Umma ta ɗora yayinda Maman tayi ma Jasmine wanka,ba jimawa sai ga Balkis ta dawo riƙe da ledar madara da biberon.
“Yauwa wanke biberon ɗin sai ki kaɗa na bata,baiwar Allah yunwa ta ke ji”cewar Maman, “toh”Balkis ta amsa ta nufi kitchen ba jimawa ta dawo da kaɗaɗar madara ta miƙawa Maman.Ana saka mata tétine ɗin ta kama ta shiga sha zut-zut,baiwar Allah sai da ta sha sosai sannan ta saki dandanan barci ya ɗauke ta.
A ɓangaren Sappa kuwa babu wanda ta gaya ma ta haihu,dan a cewar ta abun kunya ne a ce ta haifi nakasasa mai hannu guda.
Ita ke dafa ma kanta ruwan zafi tayi kuma wanka da kanta,tun da aka sako su daga asibiti ba ta ƙara sa su Maman a ido ba balle wata can Jasmine.Duk abinda ta ke buƙata malam Nur ta ke gayawa ya kawo mata,dan sam shi ma bai marhaba da haihu Jasmine duk da malam Jabeer na bakin ƙoƙarin shi wajen tunatar da shi amman fafur ya ƙi fahimta,a ƙarshe ma dai malam Jabeer ne yayi ma Jasmine huɗuba.
Sati na kewayowa aka yanka ma Jasmine ragon sunanta ba tare da yin biki ba, Sappa da malam Nur ko a kwalar rigar su dan ba su san wainar da ake toyawa ma ba.
Da dare ya shiga part ɗin Nazifa sai ganinta yayi rungume da Jasmine tana bata madara gefenta kuma Laila ce zaune ta na cin abinci tana karatun da Balkis ta kowa mata.
Baki ya taɓe a zuci yace “uwar masakai tunda ke kin ji kina iyawa ai sai kiyi”ƙarasowa yayi ya zauna ta ɗago ta kalle shi ba tare da tace komi ba.
Laila kuwa ido ta shiga juyawa tana ɗan buɗe ƙofofin hancinta tace “Abih…?Ammy Abih ya shigo nan?naji ƙamshin shi”ido malam Nur ya waro cikin suɓutar baki yace “toh mayya”Nazifa tace “Allah kiyaye ni ban haifi mayya ba”Laila kuwa tashi tayi tana lalube tana cewa Abih,”kar ki taɓa ni”ya faɗa da sauri ganin ta zo dab da shi cikin rashin sa’a ta ɗora hannunta bisa farar shaddar shi,cike da murna ta ke furta “Abihhh”wata ɗunguza yayi mata yana mai tashi tsaye ya tattare gun da ya ɓace ya nufi toilet ya na banbami.
Kuka Laila ta fashe da shi ta na kiran sunan mahaifiyarta,wani mashi ne ya tsaki zuciya Nazifa lokacin da ta ɗago Laila ta ga goshinta yayi ƙululu sakamakon bugewa da tayi da ƙafar kujera.
Tun daga wannan ranar Nazifa ke kafa-kafa da Laila da zarar taji muryar malam Nur ta na son zuwa sai ta riƙe ƴarta,shi kam ba ƙaramin daɗi ya ke mashi ba dan a ganin kiran sunan shi ma da Laila ke yi takura ce.Gefe guda kuma sosai ya ke tattalin Twins da saya masu duk abinda su ke so,a duk lokacin da babu school kuwa da su ya ke tafiya makaranta.
Karamci da Nazifa tayi na ɗaukar Jasmine yasa ta ciri tuta a zuciyar Maman da umma,wanda kuma hakan ya fara damun Sappa sai ta fara kula ƴar makauniya ta na janta a jiki wani sa’in har part ɗinta ta ke kwana.A tunanin Maman Sappa tayi hankali ne yasa take son maida alkairi da alkairi ga Nazifa ba su san cewa aiki ne ta ke sa Laila ba ,ba tare da tayi la’akari da ƙaramtar ta ba.
Lokacin da Laila ta shiga 10years zallar kyawunta da kamalar ta suka fito wanda ba komi ya ƙawata ta ba sai tarin ilimin da ta ke samu gun mahaifiyar ta da kuma amarya Balkis.Cike da jin daɗi da annushuwa Maman ke kallonta tace “yanzu dagaske Lailana kin hardace alƙur’ani hizib satin?”kai Laila ta ɗaga tana murmushin da ke fito da zallar kyawunta “gaya min duk abinda kike so ni kuma nayi alƙawarin zan yi maki shi”cewar Maman,shiru Laila tayi zuwa can tace “ina so nima idona ya buɗe na rinƙa gani kamar kowa kin ga shikenan Twins ba za su sake tsokanata ba”kamar daga sama amsar ta zowa Maman,wasu hawaye ne suka zubowa Maman cikin dauriya tace “in shaa Allah zan yiwa Abihn ki magana ya shirya mana visa mu tafi ƙasar waje ayi maki gyaran ido”rungume ta Laila tayi cikin farin ciki.